AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Allah ya hore musu Jamaal din fiyeda yanda sukai tinanin samun ya dawo gurinsu dan haka Dr JAMAAL JEEY MAM SEELAH ya zama tamkar wani kofa ko bangon kariya da dukkanin ahalin seelahs Tako ina shi zaka fara tinkara idan zaka tinkari familynsa musamman iyayensa.

Haroon seelah tini ya zama kaman wani shadow a gidan baka cika jinsa ba idan ba mugun abinsu da Jamaal Bai saniba bane zasu yi to shine zaa nemosa.

Kauna da shakuwa dayake tsakanin twins din wani irin karfi gareta da Babu ranar da Dad Baya bawa Haroon tabbacin kada Koda wasa Jamaal yasan meye sirrin dayake gudana a cikin seelahs Dan hakan daidai yake da rabasu da zaiyi har abada,
Shi kansa Haroon tsoro da shakkar bari Jamaal Koda tsautsayi yasan wani abu ko fahimtar wani abu bare sanarda shi Dan gudu da shakkar fitintinu da tashin hankalin dazai iya biyowa Baya,
Shi kansa Yana shakkar Jamaal yasan cewa shi yasan komai Amma Bai sanar masa ba Dan haka Shima a cikin shakka da taka tsantsan din Jamaal yake.

******Yau a gida ya kwana sbd tafiyan dayayi wani aiki da suke Gina sabuwar kamfanin qera karfe na Seelahs a Nasarawa ba a cikin gari ba can wajen gari sosai kusada wani kauyen da Baya nesa da cikin Nasarawa din hakama kusan filin Gina kamfanin ya shiga garin sosai Dan haka kaman a garin ma zaa ce kamfanin take dan girmansa yaci kusan garin sosai.

Baccin ragewa jikinsa gajiya yayi na kusan awa uku bayan dawowan nasa kafin ya tashi sanyeda farar doguwar wandon TT me santsi ta kayan bacci.

Jikinsa Babu Riga daga doguwar wandon data zauna a qugunsa kaman zata sauka sai farar fatar jikinsa Dake glowing tana daukan ido hutun dayake cikin Yana bayyana.

Ba slippers a fafaren qafafunsa sbd saukowansa daga gado kenan Kai tsaye toilet ya nufa Kai tsaye ya Bude ya tareda zira takarmin toilet din marasa nauyi da dadin takawa ya zare doguwar wandonsa Yana nufar shower Kai tsaye Dan wankan yake buqata kafin komai.

Ya jima a cikin toilet din ba sosai ba kafin ya fito daure da towel ash daure a qugunsa kaman towel din zata Fadi sbd lazy daurin da yayi masa
qamshin shower gel na LE LABO SANTAL ne ke tashi jikinsa ahankali me sanyin dadin shaqa.

Ficewa yayi daga bedroom din nasa a yanda yake ya nufi hanyar dining room.

Fridge ya nufa Kai tsaye ya Bude ya dauko energy drink din E-Bull ya Bude yakai bakinsa yasha Yana juyowa yaji an Bude kofar palonsa Kai tsaye an shigo batareda ya waiwayoba yasan Haroon ne sbd shi kadai ne me shigowa bangarensa Kai tsaye batareda buqatan kira a waya Dan Jin Yana Nan ko Neman izinin shigowa.

Haroon Daya qaraso tsakiyar palon tareda nufo inda Jamaal din yake Kai tsaye
Yana kallan yanayinsa Haroon yayi ya Dan dauke Kai Yana Bude fridge din shima ya dauko drink din me sanyi kadan ya Bude yafara Sha Yana son sanar da Jamaal din son karban harkar sabuwar kamfanin nasu na Nasarawa.
#MAMUH#
#DR JEEY SEELAH
#BARR HAROON SEELAH
#AMEENATOU BABBAH
#THE SEELAHS
#ROMANCE
#ZAFIN KAI

ASHNA BEAUTY SKINCARE
Free class free class
Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta
Carwash
Airfreshner
Liquid soap
Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058
Karku Bari wannan damar ta wuceku

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
#Arewabooks@Mamuhgee

19
Haroon duk yanda yaso sanar da Jamaal kasawa yayi sbd shigarsa a aikin site din bazaiyiba tinda kwata kwata bayason aiki guri Daya da Jamaal inde na kulawa da harkokin Dad dinsu ne Dan tsoron bawa Jamaal daman fahimtar wani abin Koda tsautsayi ne Dan haka yauma hadiye zancensa yayi Yana dawowa Palo ya zauna a daya daga cikin lafiyayyun kujerun palon Yana cewa

“Amma yau din a gida zaka kwana tinda tafiya ka dawo ba buqatan zuwa asibitin ko?”

JEEY din baice komaiba Saida ya karasa shenye abinda yake hannunsa ya ajiye gwangwanin E-Bull din ya juyo Yana nufar hanyar bedroom dinsa Yana gyara towel dinsa kadan Daya kusa zubewa a qasa ya Bude Baki Yana cewa

“Inada patients Dake jiran dawowana na dubasu,
And inada ma da surgery da zanyi so meyasa zanyi kwanciyana a gida?
I can’t even sleep or have a rest if ba hospital din naje ba you know that”

Yana kaiwa Nan ya shige bedroom dinsa Dan shiryowa.

Bai wani jima sosai ba ya fito shirye cikin farar freesize Casablanca hoodie rigar data bayyanarda freshness dinsa sosai
sai half trousers fari Shima da slippers din Bally a kafarsa da haskenta da tsaftanta kaman ba akai yake tafiya ba.

Qamshin turaren Allure ne na Chanel ya gauraye palon gabaki Daya daga fitowarsa Wanda ya tabbatarwa da Haroon ya fito ya Dan dago nasa fararen idanuwan Shima ya kallesa Yana ajiye remote dayake hannunsa Yana sauya channel Yana duba time na agogon dayake daure a hannunsa yace

“Please kayi dinner damu mana to kafin ka tafi asibitin,Dad yayi tinanin zuwanka da Rana Kaci abinci tareda mu amma baka fito ba.”

Zama yayi kusa da Haroon din Yana kunna wayarsa da tinda ya shigo gida ya kasheta Dan samun hutun dayake buqata.

Zamansu guri Daya ne kadai wasu lokutan yake taimakawa kowa ganesu da tareda banbance waye Jamaal waye Haroon sbd fatarsu Daya Dan banbanta sai Kuma halayya da yanayi Amma suna rabewa basa guri Daya shikenan gane waye wannan waye wancan zaiyi matiqar yin wuya har Dad dinsu kuwa musamman idan zaiyi maganar Sirri da Haroon ya ringa kokarin tantancewa kenan kada yaje yayi da Jamaal ya lalata aikin shekara da shekaru.

Cikin sauti me nutsuwa da Kwanciyar hankali ya Bude Baki yace

“Idan na tsaya Kaine zaka kaini asibiti bazan driving ba ka yadda da Hakan?”

Murmushi me kyau da nutsuwa Haroon ya sake Yana gyada Kai da cewa

“Har bakin office ma kuwa zan kaika DR JAMAAL SEELAH.”

Murmushi Shima ya saki Yana kallan Haroon din Dake Dora masa da bayanin yanda Dad zaiji dadin Hakan Dan farin cikinsa a rayuwa ya zauna table cin abinci da gabaki Daya iyalinsa.

Kiran sallan magrib ya Saka Haroon miqewa ya nufi hanyar Daya bedroom din dayake palon na Jamaal Yana cewa

“Kayi magana da mum kuwa?takira dazu tana buqatan sanin yanda ka dawo wayanka is off.”

Shigewa yayi bedroom din batareda yaji amsan JAMAAL din ba,
Toilet ya nufa Kai tsaye yayo alwala ya fito suka fito tare zuwa masallacin gidan da suke sallah a ciki tareda su Dad da masu gadinsu da securities.

Tareda iyayensu sukai sallah suna gamawa sukayo ciki gaba Daya Banda Dad Lameenu daya fita tareda drivernsa zuwa wani gurin.

Dad cikin kulawa ya Kalli Jamaal Dake cika masa ido tamkar bashine ya haifesa ba ya tambayesa yanayin aikin Nasarawan Dan kuwa ba qananun dukiya zuka zubawa wannan aikin ba Wanda idan bakiyiba zasu tafka asarar da jijjigasu matiqa Dan haka Koda wasa bari kowa ya Saka hannu a aikinba sai Jamaal ne kadai project din da komai da komai yake hannunsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected