AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Hannunta na dama ta daga ahankali takai daidai setin hasken tareda ware yatsun hannun nata masu tsayi da kyau sun qara haske da wani irin kyan fata sosai tana son kama hasken,

Jin hasken Bai kamu ba ya Sakata motsawa ahankali tareda ware kafafunta Dake a hade sbd zaman nutsuwan da sister Ashley tayi mata Dan Bata barinta yin kowane irin zama,komai nata sister Ashley na mata masu daraja da gata take gudanar mata dashi Bata taba barin ciwon tabin kwakwalwanta maidata cikakkiyar mahaukaciya ba kaman sauran patients dinsu da hauka sukeyi tuburan ba sauki da yawansu.

Ziro kafafunta qasa tayi ta ajiyesu kasan ko gama sauka basuyiba tayi saurin daukesu da sauri tana kallan qasan da idanuwanta da suke cikeda zallan hasken kyau da sanyi,

Sanyi ne taji ya ratsata na qasan dakin dayayi mata sanyi sosai sbd Koda wasa sister Ashley Bata taba barinta saukowa kasan dakinta tayi yawo ba takarmi ba Wanda Takarman kadai datake sakawa slippers designers ne wanda da yawa wasu sakawa daya takeyi zuwa biyu ace sun Bata ko ta tsinkashi da kanta bayan ba hakan bane.

Tsaro da kulawa me tsananin gaske tareda Wani irin taka tsantsan sister Ashley keyi da AMEENATOU din tin daga ranar da Dr Adams yabar asibitin hakama barin Dr Adams asibitin shine ya dawo dawo da wannan girmamammen nauyin na AMEENATOU a kanta sbd komai ya lalace ne daga wannan lokacin zuwa yanxu dan haka sosai take kulawa da ko cup din daya shafi shan ruwanta bata wasa dashi,
Hatta iskan da Ameenatou take shaka a dakinta kiyayewa akeyi sbd kudin da ake Bata na Hakan gigita suke Neman yi da kuntar mata da kai.

Kasan dakin data dauke kafafunta Ameenatou din ta sake kalla tana Dan juyar da Kai ahankali sbd son ganin ruwan dataji sanyinsu ya ratsa har cikin kanta sedai Bata ga komaiba Dan haka ta sake zuro kafarta Daya ahankali ta sake dorawa a qasan ta sake Jin Wani sanyin ya sake ratsata me tsanani Dan haka ta sake dauke kafan da sauri tana sake kallan kasan da kyau sedai wannan Karan a hankali cikin sautin muryanta me taushi cikin sanyi tace,

“Ruwa?
Ina ruwan?
Bangansa ba”

Bude kofar dakin me tsananin karfi da kaurin gaske sbd tsaro Akai ta dago idanuwanta da sauri ta zubawa kofar tana ganin sister Ashley ta sake murmushin Daya Saka sister Ashley din sauke ajiyan zuciya sbd ba qaramin sanyin kyan Ameenatou take Gani ba hakama juyewan kwakwanta daban yake Dana sauran patients nasu Dan ita komai nata sanyi da rashin hayaniya ne dashi Wanda ita datake kulawa da ita take kallan Hakan a matsayin Kila Daman can miskila ce Kokuma gata ne yayi mat yawa yasaka batada hayaniya.

Wani murmushin me kyau Ameenatou ta sake saukewa tana dawo da kallanta kasan tana cewa

“Kafan Ameenatou ya shiga cikin ruwa” ta qarasa fada tana nuna kasan dakin da hannunta Daya har lokacin idanuwanta na qasan hakama fuskanta daukeda kyakkyawar murmushin nata me sanyi.

Qarasowa sister Ashley tayi tana kallan kasan tana Dan sake fuska da kulawa da murmushi sbd fahimtar saukowa tazo yi taji sanyi sosai shiyasa gashi Sam Sam Ameenatou din batason sanyi ko kadan shiyasa kusan koyaushe sanye take da kaya masu nauyi da rufe jiki akan uniform dinta har gwara idan tana dakinta ne takan cire mata tabarta da iya uniform din.

A farko kusan kayan da ake kawowa sbd Ameenatoun Babu Wanda bame kauri da rufe jikinba shiyasa kusan itama Ameenatou din ta Saba da kayan batason sanyi ko kadan,
Hakama socks ma kusan basa rubuta da kafafunta musamman da dare idan zata kwanta baa taba mantawa baa Saka mata ba,

Ta bangaren rayuwarta a asibitin babu Wani kusanci ko maamalantar datake shiga tsakaninta da kowa bayan sister Ashley da likitocinsu,
Kaman yanda dokar take zuwa daga Sir siddeeq Wanda shine kadai Wanda sister Ashley ta sani family din Ameenatou din Babu Wanda ya yadda dashi na a bari ya samu kusanci ko shakuwa da ita tin daga ma’aikatan asibitin har nurses da sauran patients,
Ita kadai yake buqatan rayuwarta a cikin gurin batareda kusancin kowa ko wata muamalan ba Dan hakane ya Saka sister Ashley ta yafe ranakun hutunta koyaushe tana asibitin dare da Rana sbd Ameenatoun wadda duk yanda suka samu shakuwa da kauna tana kulawa da ita bakin Rai bakin fama Amma duk yanda taso sanin komai akan Ameenatou din Bata samu sanin komaiba Abu Daya kadai ta sani a bakin Ameenatou din shine Babbah da Haroon datake fada wasu lokutan a cikin yanayin ciwonta tamafi fadansu a cikin baccinta Amma bayansu Babu sunan wani data tana kamawa,

Sanin sister Ashley sir siddeeq ba shine Asalin Wanda yake tsaya akan Duk abinda ya shafi Ameenatou ba ubangidansa ne Kokuma tace ogansa ne sedai ta rasa sanin waye to?
Waye shi?
A Ina yake?
Meyasa Bata Taba ganinsa ba sedai siddeeq?
Meyasa Dr Adams duk girmansa da matsayinsa Saida ya kusa aran hauka lokacinda aka ciresa daga asibitin dagama kasar gaba Daya Rana tsaka sbd kawai Ameenatoun yayi rejecting sauyinsa wadda ya basa matsala babba,
Meyasa Dr Adams zaiyi risking Career dinsa me tsananin girma ta shekaru akan Ameenatou?
Wacece ita?
Sbd waye Shima Dr Adams din yayi Hakan?
Menene dalilin Daya Saka sabbin likitocinsu da aka kawo suka Fi Maida hankali akan Ameenatou din Suma har Saida suka tabbatarda haukarta tafi wadda aka kawota da ita Dan yanzu komai nata ya juye kaman baby haka take shiyasa a yanzu komai nata yake a sanyi kaman yanda sanyi babu hayaniya babu abinda ta sani daga sister Ashley sai siddeeq dayake zuwa dubata kusan kullum shima har lokacin batasan waye shi a gurinta ba amma dai akwai shakuwa da kauna data shiga tsakanin sabuwan alaqarsa da ita wanda a yanzu shima duk duniya itace kadai abinda yakejin zai iya bada rayuwarsa dan bata kulawa da kariya sbd matsayinta a gurin Ubangidansa kuma mutumin dayafi so da kauna fiyeda komai nasa da kowa a rayuwarsa ta yanzu,.

***Bayan barin JEEY SEELAH qasar komai ya faru ba Ayanda kowa yaso ba sai yanda ubangiji yaso,

Yanda kake tsari daban da yanda ubangiji yake tsaro Maka,

Mam seelah rashin Haroon ya tabasa fiyeda yanda ya tsammata Dan kuwa Bai taba sanin mahimmancinsa ba sai yanzu da bayanan Dan kuwa a yanzu tamkar uban da Bai da ‘da ko Daya a duniya yake,
Bai taba sanin kaunar dayakewa Jamaal girmanta yakewa Haroon dinsa ba sai yanzu Daya rasashi,

A yanzu baida ‘dan da zai ganawa azabar yayi fadan Kuma yayi masa yanda yakeso,

Duk yanda yake nuna jarumta da dauriya tareda komawa kan harkokinsu gadan gadan Dan nuna jarumta a cikin zuciyarsa raunine da gurbi me girman gaske da Babu me iya cike masa shi harda qari idan ba JAMAAL SEELAH ba Amma yasan wannan Wani mafarki ne da bazai taba samun cikewansa ba,
Buri NE da bazai taba cika ba Kila a garesa na samun JAMAAL dinsa yanda yakeso matiqar ba zubarda makaman yaqinsa zaiyiba ya tuba ya dawo hanya Hakan ne kadai zai Saka zafin kan JAMAAL sauka ya karbesa a matsayin Uba Wanda shikuma Bai debo wainnan shekarun da kashe kashenba Dan ya tuba a gaban Dan Da shine ya haifesa batareda ya samu abinda yakesoba,
Duk rayukan da suka dauka sun tafi a banza,
A daidai yanzu zai iya cewa Bai damu da rayukan da suka mutu ba akan duka wannan burin nasu dasuke dauke dashi tin Ashalawa,
Tin daga mutuwar su kasim da jamilu har izuwa ta Abdul din Babbah zai iya cewa ya barsu a banza Amma a yanzu da Haroon dinsa ya rasu a wannan fadan bazai taba saurarawa ba sedai ayi kowa ya rasa Amma bazai iya barin OMAR JADEN SEELAH da dukiyar da gurin fadanta ya rasa ‘dansa jininsa ba kwalli Daya da duk duniyar Nan shi kadai ne yake tsananin sonsa tin daga jini da zuciya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected