BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Ko da su Hamna suka dawo aka fad’a musu Abbansu ya tafi basuyi mamaki ba, dan haka basu damu ba saima shirya fita da sukayi da yamma dan su siyo ankonsu suma, baccin rana sukayi ko da suka tashi la’asar tayi sai suka shirya cikin dogayen riguna bak’ak’e iri d’aya, komai na jikinsu kala d’aya suka saka ta yanda ba zaka iya tantacewa cikin sauri ina Hamna ba ko Amna, tun a d’aki suka fara rigima moton wa za’a hau? Nan Hamna tace ai da nata aka tafi école, Amna kuma tace jiya da nata ai aka tafi, k’arshe dai dana Amna aka tafi dan dukansu basu damu da matsayinsu ba ko na mahaifinsu, shiyasa ko dreba basu damu a d’aukar musu ba bare a siya musu mota.
Tun a falo suke jiyo hayaniya a farfajiyar gidan, can suka samu yara da iyayen ana ta hira sai dai babu Hajia babba, saida suka dawo d’akin ta da sallama amma ba’a amsa ba, wata sallamar suka sake yi Hajia dake zaune tace “Ku shigo mana.”
Shiga sukayi duk jikinsu yayi sanyi dan kar ta hana su fitar, Hamna ce tace “Hajia barka da yamma.”
Kallonsu kawai tayi bata amsa ba dan haka Hamna tace “Hajia dama…”
“Dama me?” Ta katseta, d’orawa tayi da “Fita zakuyi ko? To ku tashi ku tafi, amma ke Hamna ki sani na barki ne saboda na ganku tare da Amna, dan na lura duk shegen bak’in halin uwarki ne kika d’auko na rashin son zama wuri d’aya.”
Shiru sukayi har saida tace “Ni ku tashi ku bani wuri, saura kuma idan kun tafi karku dawo sai an aika nemanku.”
Mik’ewa sukayi sai Amna da tace “Mun gode Hajia, insha Allahu ma ba zamu jima ba zamu dawo.”
Suna fitowa Hamna ta yaye kallabinta ta zubo da manyan kitsonta na gashin doki har gadon baya tare da fad’in “Shikenan dan uwarmu bata gidan saiki d’auki karan tsana ki d’ora mana, dad’in ta dai bamu muka kashe musu auren ba.”
Suna fitowa farfajiyar suka kalli matan suka ce “Su tanti (aunty) sai mun dawo.”
Hamna ce ta tuk’a mai gadi ya bud’e musu k’ofa suka fita, a k’ofar gidan suka samu colonel da Ammar zaune kan kujeru, hira ce suke amma babu mai annuri a fuskarshi, dama kana ganin Ammar na hira ne da mutum biyu a duk fad’in gidan, ko dai colonel ko kuma Gambo, da kaga dariya ko murmushinshi to Gambo ne, tsayawa tayi tace “Kawu ana hutawa?”
“Ina zakuje kuma da yammar nan?” Ya jefo musu tambayar, cikin turo baki tace “Kawu zamu je yar kasuwa ne, amma yanzu zamu dawo.”
Kunna moton tayi yace “To dan Allah ku kula da kyau, sannan karku yarda magriba ta muku a waje.”
“To kawu.” Ta fad’a tana murd’a moton, kallon Ammar tayi tace “Boss ba ko magana.”
Sai lokacin ya d’ago idonshi ya sauke a kanta amma tuni harta ja moton da k’arfi tana mishi dariya, dariya colonel yayi yace “Saika nuna mata kai boss d’in ne ko zaku kwashe lafiya da ita.”
K’ala bai ce ba shi dai dan yana so ne ya lissafa duk iskancin data masa ta yanda idan ya damk’eta zata gane shayi ruwa ne, inda shi kuma colonel yake mamakin yanda Gambo ya bar yaranshi sakaka a gari haka ba zaka tab’a cewa wasu ‘ya’yan manya bane, sa’a d’aya ma yaran su kansu basu damu ba harkar gabansu suke.
Tashi colonel yayi ya shiga cikin gida yana jin shi sakayau, dan dama sai mutum ya zo hutu ne yake samun ‘yanci da sakewa, ya shiga ne da niyyar yin wanka ya kuma had’a kayanshi, dan yayi niyya saiya bar garin ko zeinabu ta ji dad’i, ya shiga d’aki kenan ya aje wayar zai shiga ban d’aki sai wayar ta fara ruri, dawowa yayi yana kallon mai kiran, d’an uwanshi ne wanda yake da tabbacin yana garin nan wato Abban su Amar, to meyasa yake kiranshi? Tabbas ba lafiya zuciyarshi ta gaya mishi, d’auka yayi ya d’ora a kunne, daga b’angaren lieutenant yace “…
*Me kuka ya faru ko zai faru?, sai mun had’e a shafi na gaba insha Allah.*
18/05/2020 à 13:51 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
_Bismillahir rahamanir rahim_
_4_
Lieutenant ne yace “D’an uwa kaga na kiraka ko? Dama yanzu na samu wayar *Aisata* (babbar d’iyar Fatime kanwar Hajia) take fad’a min Allah yayi wa Hajia (mahaifiyarsu) rasuwa.”
Takawa colonel yayi gaba yana fad’in “Subhanallah, Hajia kuma? Yaushe? Dama bata da lafiya ne?”
Wani d’an murmushi lieutenant yayi yace “Haba d’an uwa, mutuwa ai ba sai ba’a lafiya ba take zuwa, dan nima dana tambaya Aisata ta fad’a min yau da safe ma har unguwa Hajiar ta fita, kawai dai lokaci ne yayi.”
“Ikon Allah, kaga wata mutuwa bagatatan, yanzu to ya zamu sanar ma da Hajia?”
“Shiyasa na kiraka d’an uwa, dan kaine soja watak’ila ka fini sanin dubarun kwantar da hankali.”
Yanda ya k’arashe maganar cikin zolaya yasa colonel cewa “Ba fa nasan iskanci, ka d’auka a sojan rarrashin mata da soyayya ake koya mana ne, ai wannan aikin ko Ammar ba zan sa shi ya fad’a mata ba.”
Dariya lieutenant yayi ya mik’e daga kan teburinshi wanda ke cike da tarin takardu da tarkace yace “To ni dai na fad’a maka kasan yanda zakayi karka d’aga mana hankalin uwa, yanzu haka gani nan tafe zuwa gidan zan canza kaya, dan ina so na samu bisar Hajia dan sunce k’arfe hudu da rabi za’a rufe ta.”
Da sauri colonel ya kalli agogon dake d’akin yace “Eh to, kuma kaga fa da sauran minti talatin da wani abu, kana ganin zamu iya isa *Gidan roumji* nan da wannan lokacin?”
“Sosai ma, kai dai kawai kuyi harama, duk wanda yasan zaije ya kimtsa da wuri mu d’auki hanya, zan kira Labaran na fad’a mishi shi ma nasan zaije.”
“Shikenan.” Yana fad’a ya kashe wayar ya shiga neman wata lambar, ana d’auka ya bayar da umarnin motocin d’azu su dawo zai fita shi da iyalinshi, yana gamawa ya shiga wanka cikin k’ank’anin lokaci ya fito ya shirya cikin bla (bleue) d’in shadda amma kanshi ba hula, wayarshi ya figa ya fito ya nufi d’akin Alhaji, ba wani b’ata lokaci ya fad’a mishi abinda ke faruwa tare da cewa su fito yanzu zasu d’auki hanya, lieutenant ma na shigowa wanka ya zarce kai tsaye ya shirya da gaggawa, Alhaji da kanshi ne ya samu Hajia a d’aki yace ta saka gyalenta zasu fita, tayi tambayar ina? Amma bai bata amsa ba, da haka ta fara gunguni tana saka tsadadden gyalenta ta d’auki takalmi masu shegen kyau da jakarsu ta saka, waya a d’aya hannu sai mouchoir (handkiciep) a hannu na goge k’ura da datti, haka ta fito cikin takon izza da k’asaita suka nufi k’ofa, a farfajiyar gidan suka samu mata da yara, lieutenant ne ya kalli matan yace “Mu zafi tafi gidan roumji sai Allah ya mana dawowa, akwai yiwuwar mu kwana acan, dan haka ku kula da gidan da yaran.”
Zeinabu ce ta kalli mijinta tace “Wani abun ne ya faru yallab’ai?”
D’an juyawa yayi ya kalli Hajia da sai wani yamutsar fuska take ya kuma kalleta yace “Ba komai, zamu kiraku idan mun isa can, kuma gobe zan turo a d’auke ku.”
Muryar Hajia ce ta katse shi tace “Wai meye ya faru a gidan roumjin? Ko dai wani abu ya samu Fatime ne?”
Lieutenant ne yace “Ba komai Hajia, idan munje sai muji meke faruwa.”