BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Yanda ya kafeta da ido ya nuna amsa yake jira, da wani wahalallen kallo ta kalleshi da manyan idonta wanda suka canza gaba d’aya sai lumshewa suke, cikin hard’ewar hak’ora ta bud’a baki tace “Kashe ka yanzu shine kawai mafita, dan inba gawarka na gani ba hankali na ba zai kwanta ba, idan ba gani nayi ka daina numfashi ba ba zan tab’a farin ciki ba, Abbas dole ka mutu, dan ba zan iya ci gaba da zama da kai ba, to akan me ma zan zauna da kai? Ni b’ata shekaru ina killace maka kaina, sai kawai na wayi gari naga hoton iskancinka kai da wata, watan ma kuma har cikin gidan da yake mallakina, Abbas ni zaka rainawa hankali da wata banzar k’aryarka ka shigo min da karuwarka har gida, gaban iyayenka da yaranka da kuma ni, ni Abbas? To me kake so nayi idan ba kashe ka ba?”
Girgiza kai yayi yace “Yanzu kenan ba zaki saurare ni ba, shin kinsan ma wacece wannan yarinyar? Meerah daga had’uwar mu da ita har abinda ya faru tsakaninmu duk shiri ne, shine da suka shirya dan ruguza mana rayuwa, shiri ne dan tarwatsa rayuwata da kuma taki data yaranmu, idan kin tuna fa washe garin ranar da abun nan ya faru aka nemeta aka rasa, shin kinsan nawa ta nema a hannu na tana blackmailn d’ina? Ki farka daga bacci Sam, idan ba haka ba sunyi nasara a kanmu a karo na biyu.”
Mik’ewa tayi tace “Ban damu nasan wacece ita ba, abinda na sani kawai shine ita ce wacce ta kwanta da mijin da nake ganin kamar nawa ne ni kad’ai, Abbas a tunani na na d’auka ko aure kayi matarka ta sunna zakaji kunyar kwanciya da ita a gidan nan, saboda ina tunanin kana so na kuma na gama maka komai ta yanda zakaji kunyar kusantar wata mace, ashe ba haka bane, da karuwa ma zaka iya wulak’anta ni, ashe kasan abinda kake aikatawa kenan shiyasa ka d’aga hankalinka daga ganin hoton Raihan wanda ita nata mai sauk’i ne ma akan naka, haka ka dinga shirgar min ‘ya kamar ka samu jakarka duk dan kana tsoron kar tayi abinda kayi, kasa mun aurar da ita a gaggauce ko mak’wabtanmu ba duka suka san da aurenta ba kamar wata marar gata, ka had’a ta da wanda baka san halinshi ba kuma tayi nesa damu, duk dan kana so ka b’oye laifinka.”
Juyowa yayi zaiyi magana a lokacin su Abba suka shigo a hargitse, tsayawa sukayi suna kallonsu da mamaki, Abba ne ya iya cewa “Abbas lafiya? Me yake faruwa ne haka?”
Murmushi Abbas yayi ya d’an dafe ciwonka da duk taji mishi yace “Ba komai Abba, kawai dai…”
Shiru yayi hakan yasa Sameera mik’ewa ta kalli Abba tace “Abba ba gaskiya bane, baya so ya fad’a ne saboda abun kunyar daya aikata ba k’arami bane, amma ni zan fad’a maka.”
Matsowa ta sake yi inda Abba da Khalifa suke kallonta da ido, Abbas kuma matsowa yayi kusanta yana so ta bud’a bakin zatayi magana ya dakatar, dan ba zai lamunci ta fad’i abin nan ba a gaban d’an shi na cikin shi, sam ba zai jura ba ko da hakan na nufin ya mata dukan da zai sumar da ita ne, kallon idon Abba tayi ta kalli Abbas tace “…
25/06/2020 à 11:27 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K’URA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*MASOYA NA*_
_Bismillahir rahamanir rahim_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
_13_
Yana isa ya sameta a ciki tsaye bakin wata bishiya da lemu a hannunta tana sha, inda Harira ke binshi cikin iya takonka ba tare daya sani ba, yana zuwa ya tattare babbar rigarshi kamar zaiyi dambe da ita cikin fad’a yace ” Meye kuma yanzu? Meyasa kika ce na zo nan? Ko kin manta da na biyaki kud’in da kika nema?”
Kallonshi tayi tana murmushi tace “Dady…”
Yanda ya nunata da yatsa yasa tayi shiru, ido ya zaro mata yace “Karki sake bakinki ya sake kirana da ubanki, ni ba ubanki bane.”
Ita dai murmushi take kafin ta fito da wayarta ta rik’e a hannu tana jujjuyata tace “Ok, dama nace ka zo mu had’u ne saboda wani tunani da nayi, na fahimci waccen farashin nayi maka sauk’i sosai, shiyasa yanzu na zo dan na fad’a maka ina buk’atar wasu kud’in.”
Cikin b’acin rai da hassala ya shak’i wuyanta da duka hannayenshi biyu ya had’a ta da jikin bishiyar cikin d’aga murya yace “Me kike nufi? Me kike so ki mayar da ni? D’an iska ko me? To ba zan bayar ba, kije kiyi duk abinda zakiyi, abun kunya ba’a kaina aka fara ba.”
Ma’arufa da tunda ya shak’eta ta saki waya da jaka da lemun hannunta ta fara kakarin numfashi, sai dai a wannan d’an tsakanin kuma sai wani ciwon ciki daya taso mata na ajali, dafe cikinta tayi tana matsawa tana so ma tayi kuka da ihu amma Abbas ya shak’eta sosai, shi kuma duk a ganinshi wahalar shak’ar daya mata ce, ganin jini ya fito ta hancinta ne yasa shi sakinta sai kuma ta fad’i gabanshi, juya mata baya yayi yana huci da son saisaita nutsuwarsa suyi magana, juyowa yayi da k’arfi zaiyi magana sai kuma ya ga har yanzu bata tashi ba, baya ya ja yace “Ki mik’e, we need to talk.”
Shiru ko motsi ba tayi ba hakan yasa ya d’an sunkuya ya daddab’a kafad’arta yace “Dake nake magana.”
Shiru babu amsa daga Ma’arufa, turata ya d’an yi hakan yasa fuskarta ta fito tayi rairai tana kallon sama, ganin idonta a kakkafe bakinta bud’e daga yanda take neman numfashi ga kuma jini a hanci, tsoratar da yayi yasa shi wajen yayi baya da k’arfi harya fad’i zaune a wurin, tabbas gawa ce wannan, na kasheta ko me? Da sauri ya rarrafo ya fara jijjigata yana fad’in “Dan Allah Ma’arufa, karki mutua wannan halin kuma a hanu na, kar zunubin ya min yawa mana, please ki tashi Ma’arufa.”
A tak’aice ya d’auki minti talatin a wannan halin yana tausa k’irjin ta da nufin numfashinta ya dawo, amma shiru babu labari, haka kawai ya fara hawaye da sambatu barkatai yana ji kamar ya kashe kanshi, tunani ya shiga yi na mafita kafin daga bisani zuciyarshi ta yanke miki kawai ya jefar da gawarta, yana gamsuwa da haka ya mik’e ya cire balaluwarsa ya jefata cikin mota, sam ya manta da wayarta da kuma lemun da take sha, ita da jakarta kawai ya d’auka yasa a boot ya fizgi mota ya bar gidan gonar.
Harira da har fitsari ya kusa sub’uce mata a wando saida taga fitarshi ta fito, idonta akan wayar tasa hannu ta d’auka, dama kuma Ma’arufa ba tsaro take sawa a wayar ba, tana ja sama taga ta bud’e kuma abun mamaki akan wannan banzan video ne wanda ita taga zahirinshi ma, tsaki tayi ta sunkuya zata aje wayar sai kuma tayi cak kamar an tsikareta, tsaye tayi tana kallon wuri d’aya tana tunani, wani murmushi tayi jin wani tunani daya zo mata, sai kawai tasa wayar a jakarta ta juya dan barin gidan.
Ko da Ammie ta fad’awa Sameera d’aurin auren Raihan da wani tayi fad’a har bakinta ya fara kumfa, tana ganin kawai yana neman maraba da ita ne shiyasa ya had’ata da wanda bai san halayenshi ba, kuma wai yace gobe Alhaji Khamis zai tafi da ita Maradi, jibi kuma an gama mata visarta saita wuce Maroc, saida Abba tace tayi wa mutane shiru kad’ai taja baki tayi shiru tana gunguni.