BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
“Ba zai ce ba.” Ya fad’a ko juyowa baiyi ba, saida yayi nisa kuma ya dawo da sauri ya tsaya gabansu yace “Wai me yasa ma baku fad’a ma kowa ba sai ni?”
Kallon juna sukayi sai kawai yayi dariya yace “Na gane ma, wato ni ne marar mutumci ko?” Sake juyawa yayi yana fad’in “Allah ya shirye ka Ammar.”
Yanda ya fad’a haka akayi, amma fa babu abinda aka fasa, haka dai aka samu aka kai sati d’aya, a lokacin mutane sun rage sosai wasu ma sun koma garinsu, haka ma mahaifinsu Amna ya koma tare da tanti da ita kanta Hamna, sai Ammar daya shirya tafiya yau shi ma, lieutenant ya nemi daya zauna amma saida ya kalli Ummy yace “Zan zauna Abba idan naga kowa na so.”
“Kamar ya?” Shine abinda ya tambayeshi, bai ce komai ba sai kallonta da yake, Amna ma kukan shagwab’a ta fara ita ba zata tafi ba wai, saida ya kalleta yace “In ban ci ubanki a gidan nan Amna ki ce d’an iska ne ni, ke ni zaki mayar sakarai, na barki anan ni kuma me zanyi acan ni kad’ai, tunda mukayi aure dake akwai ranar dana tab’a kwana ba’a malamalanki ba?”
Ummy da Amna tare suka rufe baki sukayi k’asa da kansu cikin jin kunya, lieutenant kam irin basarwa yayi kamar baiji ba, wata tsohuwa a cikin wanda suka zo daga k’auye na gefe ko gani ba tayi da kyau ta kalleshi tace “Halan Ammaru ne?”
Kallonta yayi ya washe baki yace “To dama waye in ba ni ba, Hajja ni ne da kaina?”
Cikin takurarriyar muryarta tace “Miye kuma malamalai? Naji kace a bayansu kake kwana?”
Ko da Lieutenant yaji haka sai yayi gaba ya fita a gidan dan shi dai yasan halin kayanshi saiya fad’a, Ummy kuma kallon waya aikeki tambaya ta mata, saida ya matso kusan Amna ya janye mayafinta yace “Kin gansu nan.”
Da sauri Amna ta juya bayanta tana gyara gyalenta, tsohuwar kuma cewa tayi “Ai kasan ba gani nake da kyau ba ko Ammaru.”
“To bari kiji.” Ya fad’a yana sunkuyawa kusanta, saida ya kamo kanta cikin kunne ya rad’a mata “D’uwawu.”
_In dai tambayar k’wak’waf gareki ai shikenan._
D’agowa yayi ita kuma tasa hannaye ta rufe kunnuwa tana fad’in “Sayadina rasulillahi, Ammaru haka ka zama dama?”
Wani kallo ya mata yace “Hajjo daina kira na da Ammaru fa, Ammar zaki ce ko *shugaba*.”
Cikin fitar da magana d’aya bayan d’aya tace “Shubagan ina kuma? Ni Ammaru na iya to.”
“Ai ko zan miki fatan mutuwa in kika k’ara kirana hakanan.”
Tsohuwa najin haka tace “Wai kai baka iya hira mai dad’i bane, to in dai shugaba ne zan fad’a amma bana son hirar mutuwa.”
Tsuke baki yayi ya k’are mata kallo sama da k’asa ya kalli Amna yace “Kiji fa wai bata son mutuwa, to ko uwar me zata zauna tayi a duniyar, irinsu basa tafiya taya zamu ji dad’in haifo sabbin yaran mu?”
Turo baki ta k’ara yi gaba ita dai har yanzu bata son tafiya, had’e fuska yayi yace “Ni kike kumburo ma bakin duniyata?”
Sakin bakin tayi tace “A’a.” kallon Ummy yayi yace “Mu zamu tafi kuma a yafe mu.”
Juyawa sukayi inda take biyarsu a baya tana magana da Amna, saida suka kai mota inda Jamil ke jiransu zai kaisu gidan bus ya bud’a yaran suka shiga, zai shiga Ummy tace “Ammar.”
Tsayawa yayi tare da juyowa yana kallonta, kallon data ma Amna yasa ta zagayawa ta bud’a gidan baya ta shiga ita ma ta zauna, saida ta ga shigarta ta kalleshi cikin taushin murya tace “Ka bar min Ameerah nan, saika fad’a min yaushe zaka dawo?”
Kallonta yayi sosai ido cikin ido yace “Ummy Ameera kuma?”
Ckkin murmushi tace “Eh, ina son yarinyar sosai kamar yanda nake son…” Kallonshi tayi sai kuma ta sauke idonta k’asa tace “Kamar yanda nake son mahaifinta.”
Baisan yanda akayi murmushi ya sub’uce masa ba, sosai yake murmushi sai kuma ya turo baki alamar shagwab’a yace “Ummy dama kina so na ne?”
Hannu tasa ta mari fuskarshi cikin fad’a tana fad’in “Ubanka Ammar, zan haifeka a cikina ne kuma nace bana sonka? Ina ka tab’a ganin wannan uwar kai? Ubanka ne kai yanzu zaka iya fad’a min adadin son da kake ma yaranka?”
Shiru yayi yana kallon sai Ummy data share yar k’wallarta tace “Yaushe zaka dawo yanzu?”
Cikin ladabi yace “Zan dawo Ummy ranar da kika ce kina son gani na a gidan nan.”
Cikin marairaicewa tace “Wai Ammar me yasa kake hakane? Nifa ranar ma magana ce kawai na fad’a maka, amma ba nayi da wata manufa bane.”
Langab’e kai yayi yace “To Ummy ai ke ce ke yawan fad’in hakanan, saiki dinga hantarata kina cewa na b’ace miki da gani.”
“To naji na daina ko.” Tana fad’a ta juya da sauri ta shige falon, da kallo ya bita sai kuma ya bushe da dariya, shiru yayi alamar yana tunani kafin ya tab’e baki yace “Ina ga fa kunyata ce take ji a matsayina na d’an fari.”
Kallon k’ofar yayi yace “Zan dawo nan da wata uku Ummy insha Allahu, na miki wannan alk’awarin.”
Shiga yayi suka d’aga zuciyarshi fal farin ciki na abinda ya faru, yau ma a Niamey suka tsaya kafin su kwana su wuce, tunda suka zo shi dai bai ganta ba ko yaji motsinta, sai dare ya shirya ya fita cikin gari tare da wani abokinshi dake nan, bai wani jima sosai ba ya dawo, tun a farfajiyar gidan ya fahimci anyi bak’o ko kuma bak’i daga yanda yaga wata mota mai kyau a farfajiyar, har zai nufi b’angarensu yaga mutane biyu sun fito daga b’angaren shak’atawa na gidan, kallonsu yale sosai har suka shigo cikin haske, da sauri ya d’ora hannunshi kan k’irjinshi saboda bugawar da yayi, rintse ido yayi yana girgiza kai, saida yaji takonsu na k’aratoshi ya bud’a ido ya kallesu, cije leb’en k’asa yayi cike da bala’in daya fara gurgurarshi, cikin jin masifa a mutu ko ayi rai yace “Hamna ya zakiyi wannan gangancin? Ya zaki jawa bawan Allah firgitar zuci? Me yasa baki tausayina ne? Akan me zaki min wannan d’anyan aikin?”
Sake kallonta yayi da kyau, yatsunshi ya fara tank’warawa suna k’ara k’as k’as k’as, to wai uban wa ma ya barta ta fito hakane, wannan ai shi take tona ma asiri, wani shegen d’angalellen wando slim wanda ya bi jikinta matuk’a, bak’i ne wulik baya da kwalliya sai zip d’in dake bakin aljihunshi da suka mishi kwalliyar, rigar ma fara ce fat amma hannayenta sun d’an wuce har gwiwoyinta, daga samanta bud’e yake sai k’asan k’ugun daya matse ya zauna kan k’ugunta d’as, wani kallabi ne kanta irin na kanti fari sol dashi shima, amma kitson atach d’inta ya sauka har gadon baya.
A hankali ya fara takowa yana yi kansu har suka game, kallon kallo akuya kallon kura aka shiga yi, kallon.da yake mata babu arzik’i cikinshi, kallon ki fara lissafawa kanki second d’in da suka rage miki a duniya ne, amma kafin nan zan fara kifar da wannan k’aton banzan. Ita kanta gabanta fad’uwa kawai yake, rabon ayi ne da tsautsayi suke bibiyarta yau, dan inba tsautsayi ba bata tab’a yarda ya zo gidan nan ba sai yau daya takurata yana so ya zo ya mata gaisuwa, ta fad’a mishi gidan amma bata d’auka yau zai zo ba sai kawai kiranta yayi yace gashi ya zo, izini ta bayar aka barshi ya shigo ciki, kuma da zuwanshi da yanzun da zai tafi baifi minti goma ba, amma tasan yau sai ta Allah su rabu lafiya, ita abinda ma ke damunta shine babban mutum ne, d’an siyasa ne shima kuma d’an kasuwa, yana da mata da yara uku, bata so ya zubar mata da mutumci kuma shima ua zubar mishi da mutumci, dan shi ba tsoran takife yake yi ba, tana cikin zaro idon nan tana kallonshi taji yace “Malam me ya had’aka da *matata*?”