BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Kowa kama bakinshi yayi kamar sun cika iska, ture Jibril yayi daga kan kujerarshi ya fad’i k’asa ya zauna yana fad’in “Zan kama ki ne yarinya, Allah zaki san ni kika tab’o yar banza mai zubin gwiwar daji.”
Amar dake ta rik’e dariya ne ya kasa ya mik’e tsaye ya mik’o mishi d’an k’aramin bol d’in shayi na glas yace “Babban yaya ga shayinka, premier ( na farko) ne.”
Lokacin kowa ya samu damar sakin dariyarsa har da masu rik’e ciki, kallonsu yayi da niyyar masifa sai kuma ya fashe da dariya shima yasa hannu ya karb’a ya kurb’a, saida ya kallesu ya sumbaci yatsunshi biyu ya jefa musu sumbar yace “Ina sonku k’annai na, kune rayuwata fa.”
Jamil ne ya fito duk yayi gumi yana ganinshi yace “Yawwa Jamalun ya ake ciki? Waken ya dahu ne?”
Cikin jin haushi Jamil yace “Da k’yar na tashi Nana daga bacci ta bud’e min madafa, da k’yar na samu na d’ora ruwan, yana can zata k’arasa dafawa.”
Girgiza kai kawai yayi suka ci gaba da zuk’ar shayinsu suna hira, wani abun daya fad’a kowa sai yaji abun wani iri, wani suyi dariya kamar cikinsu zai fashe wani kuma su girmama al’amarinshi, kamar yanda ya fad’a kam saida akayi sallah asuba kad’ai ya barsu suka koma cikin gida shima ya shiga ciki, wanka yayi ya canza kaya farare tas wanda rigar t-shirt ce sai wando 3 quater kafin yasha magani saboda k’afarsa da har ya manta akwai ciwo, kiran Ummy yayi ya tambayesu yanda suka tashi tare da neman a bashi Amna, sosai suka jima suna hira cikin nishad’i kafin suyi sallama yace sai ya zo d’aukarsu.
Misalin *06:30* na safe Hamna ma ta kirasu suka gaisa ta tambayi yara, saida suka gama waya har ta kashe Amna mijinta ya zo tunaninta, tunawa tayi da fa ciwo a k’afarsa, sannan mutum ne dake wasa da cikinsa, idan ya ga abinci ne zai ci idan kuma bai gani ba babu ruwansa, ita kanta wani lokacin sai tayi rarrashi yake ci kafin ya fita da safe, sake kiran Hamna tasa Ummy tayi ta bata wayar, tana d’auka tace “Na’am Ummy.”
“Ni ce yer uwa.” Ta fad’a murya k’asa k’asa, d’orawa tayi da “Dan Allah yer uwa wani taimako zaki min.”
Daga b’angarenta ta amsa da “Wane irin taimako kuma Amna? Kin fara manta yanda muke ne?”
“A’a, amma nasan abu ne mai wuya a wajenki, ki min alk’awarin zaki min kafin na fad’a miki dan Allah.”
Cikin rashin son wasa tace “Fad’a min ina jinki, nayi alk’awarin.”
Cikin muryar rarrashi tace “Yer uwa taimaka min zakiyi dan Allah idan an kammala abin kari ki kaiwa yah Ammar, sannan idan kinje ki d’ora masa ruwan zafi ki ce masa ya gasa k’afarsa sosai sannan yasha magani, dan Allah.” Ta k’arashe da sake kashe murya.
Wani mamaki ne ya kashe Hamna tare da tunanin taya zata je su had’u bayan abinda ya faru jiya? Gashi kuma tayi alk’awari, bayan alk’awarin kuma tasan halin Amna da rik’o zata iya yin hushi da ita akan haka, a hankali ta bud’a baki tace “Shikenan naji zanyi, tunda so kike ki mayar dashi kamar wani jariri.”
Murmushi Amna tayi tace “Jariri ne mana, har yanzu baya iya kula da kanshi, Hamna yana buk’atar kulawa.”
Tsaki Hamna tayi tace “Ki kular min da yarana ni, banda lokacin haukanki ke da mijin na ki.”
Kashe wayar tayi ta aje ta sauko k’asa, madafa ta shiga su Zeituna na aiki ta kalleta tace “Aunty Zeituna idan kun kammala Amna tace a fitarwa mijinta da abincin saina kai mishi.”
Cike da sakin fuska Zeituna tace “Kin ganshi nan zan fidda mishi kuwa, dan bana mantawa da babban d’an gidan nan, tunda yau babu mai girka masa.”
Kallonta tayi tace “Amma kun gama da wuri yau aunty.”
“Eh saboda za’a kaiwa yan asibiti ne.” Saida ta d’auki wanda Zeituna ta nuna mata tace “Wa zai kai musu?”
“Ni nake son tafiya tare da Abban Fatima.” Cewar Zeituna, kallonta Hamna tayi da mamakin sunan data kirashi dashi, wato tunda ita ma yanzu ta haihu dashi ba buk’atar ta ci gaba da kiranshi da Abban Ammar? Abun ya birgeta sosai har taji ina ma tana da ‘yancin kiran d’anta da sunan ubansa data kirashi da *Shureim Ammar* da babbar murya kowa yaji, karb’ar abincin tayi ta fito ta nufi b’angaren nasu, ta manta bata saka ko da mayafi ba bare hijab, wannan siket d’in na atamfa da rigarsa wanda suka kama jikinta suka zauna daram dam, ga k’ibar data k’ara yasa k’ugun ta ya sake sama ya zauna da kyau, d’aurin kallabin mai sauk’i ne wanda zamu iya kiransa da ture kaga tsiya, dan ya turo sosai gaban goshinta, ko kwalli babu a idonta haka ta bud’a k’ofar d’akin ba tare da tunanin zata same shi a bud’e ba, amma sai ji tayi ya bud’e a hankali ta shiga tana kallon yanayin d’akin shiru kuma babu wuta sai hasken safiya kawai, saida ta je gaban teburin nan ta aje kwanukan ta nufi hanyar madafa dan d’ora ruwan d’umin kawai tayi tafiyarta, ta taka d’aya biyu na uku taji wata tattausar murya a bayanta yace “Ba sallama, ba neman izinin shigowa bare ki gaishe da mutane?”
Tsayawa tayi sai jikinta da taji ya fara rawa rawa kamar zata kifa k’asa, had’e fuska tayi alamar bata son wargi sannu sannu ta juyo, inda taji maganar ta kalla sai taga ashe ya kishingid’a ne kan kujera yayi luf, turo baki tayi cikin shagwab’a tayi k’asa da kanta tace “Ina kwana.”
Wani narkakken kallo ne yake mata inda yake jin abubuwa da dama na b’abb’akowa daga k’asa suna yin sama, ganinta a haka ba k’aramin gigita nutsuwarsa tayi ba, a hakan daya ganta ta tuna masa da duniyarsa, dan atamfar ma kala d’aya ce haka d’inkin, kuma ita ma haka suka amsheta a ranar daya fara ganinta dasu, lumshe ido yayi tare da buk’atuwar son ganin hak’oranta ko da ba ta sigar dariya bane, hakan zaisa ya yarda cewa ta daina hushi dashi, amma ganin fuskarta a had’e a haka zai rikita lissafinsa har ya kasa iya aiwatar da komai, bud’a idon yayi ya sauke kanta yace “Kunna fitilar.”
Rintse ido tayi, har ga Allah tasan inta juya saiya kalleta, fuskantarshi tayi sai kawai ta dinga yin baya baya tana nufa wajen kunna hasken, murmushi ya dinga yi yana kallon fuskarta a ranshi yana godiya ga Allah data rufa masa asiri ta juya bayan, dan shi fa ko matarsa idan zata juya masa bayan nan sau dubu sai yaji buk’atarta sau dubun, kuma yana tsoron sake faruwar al’amarin a bisa wasu dalil…Hasken d’akin daya kawo ne ya katse masa tunaninsa ta hanyar kallonta.
Da kallo ya bita ta shige madafa, wayarsa ya fito yana dannawa yana jiran fitowarta ya sata dariya ko hankalinsa ya kwanta.
Ta d’an jima kafin ta fito rik’e da robar jiya da k’aramin towel, har gabansa ta aje masa ruwan kafin tace “Wai inji ta ka ci abinci ka gasa k’afarka sannan kasha magani.”
Murmushin gefen labb’a ya mata yace “Ashe kema kina jin maganar zuciyarki akai na?”
Da sauri ta d’ago kai ta kalleshi da sauri kuma tayi k’asa da kanta saboda kallon da yake mata, ganin tayi k’asa da kanta yasa yace “Mai ladabin kunama, yanzu sai kin tashi zaki fita ki juyo ki ce min Allah ya isa ko?”
A hankali ta girgiza kai tace “A’a, me ka min da zan maka Allah ya isa?”
“Kinfi kowa sani.” Yana kallonta, mik’ewa tayi zata fita yace “Baki k’arasa ladanki ba ai, ki zuba min abincin idan kin gama ki gasa min k’afar tawa, ko ba abinda tace kiyi ba kenan.”
Yamutsa fuska tayi tace “Ni ce zan gasa maka k’afar? To ba haka tace nayi ba, wannan ma saida ta rok’e ni nayi.”
Sakar masa duka giman idonshi yayi wanda hakan ya tsorata ta, ba shiri ta matso tace “Zan zuba to.”