BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wata dariya Jano yasa yana fad’in “Babban arne kenan.”

Ammar dake cike da shakku matsowa yayi wurinsu ya kalli kawu rai a b’ace yace “Me yake faruwa ne tsakaninka da shi? Kasan waye wannan kuwa? Ba mutumin kirki bane.”

Wani kallo Jano ya mishi yace “Ammar, ka sanni na sanka, karka shiga sabgata mana tunda bansa da kai ba, kayi abinda ya kawoka nayi abinda ya kawo ni.”

Daf dashi ya matsa yana fad’in “Ba zanyi sabgar tawa ba Jano kayi abinda za kayi, kai ka sanni wallahi ba zan lamunci iskancin nan daga gareka ba.”

K’asa da sama ya kalleshi yace “Bana jin rigima, kai kuma kullum a cikinta kake kamar wanda aka haifa ana dabbatuwa, dan haka banda lok…”

Bai yarda ya k’arasa fad’a ba ya kai mishi bugu a baki, baya baya yayi ya kaiwa motarshi karo ya dafeta yana kuma dafe da bakinshi, idonshi jawur sukayi har da k’wallar wahala, da sauri kawu ya shiga tsakani yana bawa Ammar baki ya rabu dashi, cikin jin bala’i da masifa yake nuna kanshi yana fad’in “Ni d’in? Ni ne aka haifa kamar ana dambe? To bani ne ba sai dai in kaine ubanka ya haifa yana dambe.”

Tasowa Jano yayi yana tofar da yawun bakinshi da yake jin sunyi gishiri alamar jini yace “Ni ka wa haka Ammar? Ni? Tak’amarka akwai iko da masu saka kakia gidanku? To wallahi sai kayi nadamar dukan nan daka min, in kuma bansa kayi dana sanin haihuwarka ba to kace ba d’an halak bane ni.”

Cikin d’aga sauti ya fara fad’in “Yeeee, kai ba d’an halak bane, da gani ma ai ana ganewa, banza mata-maza kawai, ashe k’aramin d’an jagaliya ne kai, to kaji da kyau Jano, ba boka babu malam babu d’an bori, kuma a haka zan ci uwarka, ruwan randa kawai zansha na ma iskancin da baka tsammani, idan har kuka gagara kai da matsafan naka to ka nemi lambata a wurin wanda ya sani, ka zab’i rana da lokacin da zamu had’u da kai a bayan gari saika sa min hannu, watak’ila ka iya huce haushinka ta hanyar rama dukanka.”

Juyawa yayi ya kama murfin motarshi ya bud’a zai shiga, tsaya yayi ya kalleshi da kyau ya d’aga mishi yatsarshi ta tsakiya wacce tafi tsawo tana kallon sama, sannan yayi alama da yatsunshi cewa sai sun had’u shiga yayi ya tayar ya wuce. Suna had’a ido kawu ya sunkuyar da kanshi yana murmushin mugunta, a ranshi yana fad’in “Ashe kowa da wanda ya raina.”

Tsaki yayi ya juya a fusace shima ya bar wurin, Ammar ma daga nan asibiti ya sake komawa, wannan kayan ya cire dan baya so kowa na gida yasan shi dasu ya mayar da nashi kafin ya sake komawa gida.

Jano na barin nan ya so ya zarce ofishin yan sanda, ba wai dan ya dake shi sai dan ganinshi da kakin soja da yasan ba soja bane kuma yake sawa, yasan inhar doka ce ya taka ta hanyar sa kayan dole hukunci zai hau kanshi, amma saiya bari har safiya tayi sai yayi k’ararshi. Ammar kuma na ko da yaje gida kai tsaye wajen amaryarshi ya nufa, tana zaune kan kujera tana kallo ya same ta, tsaye yayi ya bud’e mata hannayenshi alamar ta rumgume shi, bata fahimce shi ba sai cewa da tayi “Sannu da zuwa yah Ammar.”

Mik’ewa tayi ta nufe shi tana k’ara fad’ad’a murmushinta, tana zuwa ta tsaya bata matsa kusa dashi ba, saida ya mata kallon zan ci… kafin ya fizgota da k’arfi ta fad’a jikinshi, saida zaman d’an kwalinta ya canza inda tayi fiki’fiki da idonta, matseta yayi sosai yana sauke numfashi, d’agata yayi daga jikinshi ya kalleta yace “Daga yau kika ga na shigo haka zaki min, kuma ko gaban waye ban yarda ki nuna jin kunya ba, haka nake so kuma dole kiyi.”

Yana fad’a ya wuce ya barta tsaye, juyawa tayi da baki bud’e ta bishi da kallo, d’aga ido tayi sama tace “Allah gani gare ka, ka shirya min bawan nan naka.”

Zaune ta koma tayi tana ci gaba da kallo, amma duk in taji motsi daga d’akinshi sai gabanta ya fad’i, ana haka dai har ya fito sanye da farin wando iya gwiwa mai aljihu da farar singlet d’in data kama shi sosai, yana zuwa ya zauna kamar zai fad’a mata yana fad’in “Kiyi hak’uri ba zan iya yi miki kwalliya ba, yunwa nake ji kuma na gaji, amma ki sani ni makwoyin sunnar annabi ne.”

Dariya tayi ta mik’e tsaye ta nufi teburin abinci, da kallo ya bi manyan kayan dake birge shi tare da ayyana luguden da zasu sha yau a hannunshi, cije leb’en k’asa yayi yana lumshe ido, yana kallo ta d’auko kwanukan abinci ta juyo tana takowa, nan ma ido ya k’ura mata yana kallon komai na hallitarta, bai sani ba ko dan komai nasu iri d’aya ne da kankana, ko kuma dan suna da k’ira da hallita irin yanda yake son mace, dan shi dai yafi son mace mai cika hannu yar dumul dumul, ko gajera ce yana sonta a haka bare kuma su dake da tsayi, sannan ga kyawun fuska masha Allah, haka kuma Amna tafi kyau akan kankanarshi, kawai dai haske kankana tafi waccen, shi dai kawai yasan komai nasu yana birgeshi, tana zuwa ta sunkuya ta aje kayan ta durk’usa ta fara zuba mishi, kallon fuskarta yake yace “Amna yanzu ma abincin kika dafa?”

Ba tare data d’ago ba tace “Yah Ammar idan ban dafa ba to me zaka ci?”

Yatsina fuska yayi yace “Da gaskiyarki kuma, dan kinga banyi tunanin siyo abinci ba.”

D’an murmushi kawai tayi tare da kallonshi tace “Na aje maka anan ne?”

Kai kawai ya d’aga mata, gyara wurin tayi sannan ta aje mishi ta zaune yanda suke fuskantar juna, kallonshi ta sake yi tace “Bismillah.”

Saukewa yayi ya tank’washe k’afafu yana fad’in “Amma ko baki dafa ba ai ga Hajiarmu, sai muje mu ci na su.”

Shiru tayi ita dai ko kallonshi ba tayi ba, loma ya fara kaiwa tare da bismillah, saida ya tauna ya had’iye ya kalleta kamar mai karanta wani abu a fuskarta kafin yace “Kinyi kyau sosai.”

Sunkuyar da kai ta sake yi tace “Nagode.”

Da mamaki ya kalleta yace “Ke ba zaki ci ba?”

Kallonshi tayi tace “Ka fara ci ka k’oshi.”

Tab’e baki yayi ya jawota ya zaunar da ita kan d’aya cinyarshi, k’ara sunkuyar da kai tayi tana sissinewa kamar ta shige k’asa, d’ebo abincin yayi ya kai mata a baki tana fad’in “Gani ni k’aton banza kenan, na zauna ina cin abinci ke kina kallo na.”

Tun tana gocewa har ta fara karb’a ita ma, bai barta ba saida ta shagwab’e fuska tace “Wallahi yah Ammar na k’oshi, cikina kamar zai fashe.”

Kallon rainin hankali ya mata yace “Wannan d’an abincin da kika ci ne zai fasa miki ciki? To gidan ubanwa kika kwaso wannan k’ibar?”

Tab’e fuska tayi kamar za tayi kuka a zuciyarta tace “Ai ba kowace k’iba ta cin abinci ba, kuma ubana ba siriri bane bare kace banda inda na gadota.”

Saida ya shafa cikinta kad’ai ya daina bata ya ci gabada ci har ya k’oshi sannan yayi hamdala, tashi tayi ta d’auke kwanukan ta dawo ta zauna k’asa dan har yanzu shima bai tashi ba, d’aga k’afafunta tayi ta d’ora hannayenta saman gwiwan, bata ankara ba taji ya finciko k’afafunta ya mik’ar dasu, tana kallo ya d’ora kanshi ya juyo da kanshi yana kallon fuskarta, zagaya hannunshi yayi ta bayanta ya d’an zage zip d’in rigarta, d’aya hannun kuma ya zura shi ta cikin rigarta yana wasa da cibiyarta, sam bata yarda sun had’a ido ba sai kawar da kai take yi, abun kamar wasa saiya d’aga rigarta ya zura harshenshi a cibiyarta yana ta karkad’a shi idonshi rufe kamar mai bacci, ita kanta baccin taji yana son figarta ga tsikar jikinta da take mugun tashi, jikinta duk yayi sanyi k’alau d’an d’aya hannun ma bayanta ya zura shi har ya b’alle mata bras data saka wanda dama take jin ta dameta saboda rashin sabo, a hankali ya fara zarmewa ta hanyar zamar da rigarta ya cire mata hannayen, ita kanta bras cireta yayi ya cilla gefe, da sauri ta jawo rigarta zata mayar ya bud’a idonshi da suka bata tsoro saboda canzawar da sukayi, tashi yayi tsaye tare da kama hannunta ya nufi d’akinshi da ita, tunda ta ga inda suka nufa take addu’a a zuciyarta wanda bata ma san me take karantawa ba, tsabar yanda zuciyarta ke bugawa da kakkarwa da jikinta ya fara yi yasa hawaye fara zubo mata, yau kam babu tsumi babu dubara ta shiga hannu kenan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected