BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi yayi yana kallon labb’enta masu duhu, mamakin yanda ta canza yake sai wani sunne kai take bata so su had’a ido, juyawa yayi ya zauna kan kujerar shi yaran duk suka zagaye shi kowa da abinda yake tab’awa, kallonta yayi yace “Nagode fa.”

Wutsil wutsil tayi da ido kamar mai son tuna abinda ya faru yanzun har yake mata godiya, cikin nutsuwa ta d’aga duka idonta ta sauke kanshi tace “Godiya akan me?”

Kallonta yayi yace “Akan kulawar da kike da yaran nan.”

Cikin sunkuyar da kai tace “Dan na kula da yara na har ina buk’atar a gode mun ne?”

Cike da jin dad’i yace “Yaba kyauta tukuici mana.”

D’an tab’e baki tayi kawai ko kallonshi ba tayi ba, murmushi yayi ya mayar da hankalinshi kan yaran, ganin sun fara hira zai manta da ita a tsaye yasa ta d’anyi gyaran murya, a hankali ya juya ya kalleta da alamar tambaya, kamar marar gaskiya ta kalle shi tace “A..h.mad, zamu koma ne.”

Ajiyar zuciya ya sauke ya taso daga kan kujerar, saida ya zo daf da ita ya mik’a mata shi, tana karb’arshi ta kalli yaran tace “Sai kun dawo gida.”

Juyawa tayi sai kuma yace “Kin manta.”

Juyowa tayi sai kawai ya karb’o wayarta a hannun Ameer ya mik’a mata, kallon fuskar Ameer tayi sai taga duk bai ji dad’i ba, kallonshi tayi tace “Ka bashi ya ci gaba da wasanshi, idan kun dawo gida saina amsa.”

Ba alamar wasa yace “Ita d’in ai ba abar wasa bace, ya kamata kuma ki fara nuna musu cewa rayuwa ba komai kake so kake samu ba.” Yana fad’a ya danna mata ita a hannunta.

Kallon fuskarshi tayi amma ba cikin idonshi ba tace “Hakane, amma ai abinda ya shigo hannunka da wanda ke hannunka bai kamata ka bari ya kubce maka ba, shi ta riga data shiga hannunshi, ka bar masa kawai zan karb’a ba ta yanda ranshi zai sosu ba.”

Wani shu’umin kallo ya mata had’e da murmushi yana motsa labb’enshi a hankali yace “Wannan soyayyar da kike nuna wa *Ammar* fa tana yawa.”

Kallonshi tayi sai ta fahimci iskanci ne ya soka mata, ita ma d’an murmushi tayi tace “Ina son k’aramin Ammar sosai, ba shi kad’ai ba duka yaran da suka fito daga cikin babbar Amna ma.”

Murmushi yayi sosai ya k’ura mata ido, kallonshi tayi tace “Sai anjima.”

Bai ce komai ba har ta juya zata fita yace “Me yasa? Yana ina?”

Tsayawa tayi ta juyo ta kalleshi tace “Waye?”

Ba tare daya rusuna idonshi ba yace “D’ana Shureim.”

Tab’e baki tayi tace “Yana gida mana.”

“Me yasa baki taho dashi ba? Ina so naga duka iyalina a tare dani, shi kad’ai ne babu a wurin nan.”

“Idan ka cire ni ba.” Ta fad’a kai tsaye, murmushi ya mata mai ban mamaki yace “Har da ke mana, fuskarki fuskarta ce.”

Kallonshi tayi fuskarta babu walwala, juyawa tayi zata fice taji muryarshi cikin isa da zarra da k’asaita yace “Kiyi sauri ki kawo min shi shima ina buk’atarshi anan.”

Juyowa tayi tace “Kayi hak’uri, gaskiya idan na shiga gida yanzu ba zan fito ba.”

Kallonta yayi cikin rikid’ewar lokaci d’aya yace “Ki kawo min shi nan da minti ashirin ina jiranki, inba haka ba saina daddala miki mari wallahi.”

“Mari fa? A wannan k’arnin?” Ta fad’a cike da rashin tsoro, cikin tabbatarwa yace “Ki jaraba ki gani to, ba zan tab’a yin kaffara akan abinda nake da yarda akaina a kan shi ba.”

Girgiza kai tayi tace “Ba zaka tab’a canzawa ba har abada.”

Ba tare daya kalleta ba yace “Zan canza ranar da kika so hakan.”

“Kamar ya?”

Saida ya zauna kan kujerarshi ya kalleta yace “Kamar yanda kika ji na fad’a.”

Juyawa kawai tayi suka fice ta barsu, da kallo ya bita shima har ta fita, bai kammala abinda yake ba ya fita da yaran dan yana so ya dawo kafin rana ta sake takewa sosai.

Shigar Hadiza ciki ko gaisawa basu gama yi ba gwamna ya zo gida, cikin rakiyar masu tsaron lafiyarsa har ya shiga falon kafin suka barshi, nan aka shiga gaisawa har da Hadiza saida suka gaisa cikin mutuntawa ba tare da idonsu sun had’u ba, sun gaisa da kowa amma banda lieutenant da Sa’ada.

*Ummy* kuma ta riga Hamna fita a gidan, dan a lokacin da taje dan suyi magana da lieutenan akan banzan da yake yi da ita, tana so ya fad’a mata matsayinta, tunda abun ya faru baya ko kallonta, ya daina zuwa d’akinta ranar kwananta sai dai ita taje, idan ta je kuma ko magana baya mata hasalima wani lokacin sai yace ta bashi wuri yana son zama shi kad’ai ko zaiyi wani abu, abun ya dameta sosai ta yanda yanzu ko gaishe shi tayi gaban mutane sai dai ya amsa da lafiya ko yawwa, har ta lura da mutane sun ankara da rayuwar da suke yi yanzu, dan haka safiyar ta yau taje har d’akinshi dan ayi ta ta k’are, wata shida ba kwana shida bane ai.

Sanda ta je ta same shi yana shirin fita dan yau baida fita da wuri, sallama tayi ya amsa da k’yar ba tare daya kalleta ba, saida ta tsaya d’an nesa dashi tace “Ina kwana.”

Shiru yayi yana ci gaba da saka rigarsa ta kakinshi, ko da ta ga zai b’alla botira tayi saurin matsawa zata taimaka masa, baya yaja tare da k’ara had’e fuska a cikin mak’oshi yace “Um um.”

Kallonshi tayi tare da sauke hannayenta k’asa tace “Magana na zo muyi idan kana da lokaci?”

Shiru ya mata ya ci gaba da shirinshi kamar baisan da zamanta a d’akin ba, zaune yayi kan kujera yana d’aura d’amarar takalminshi, hakan ne ya bata damar matsowa tace “Magana nake.”

K’asan mak’oshi sosai yace “Aiki ya min yawa yanzu bana da lokaci kaina ma, ki gaggauta fad’in abinda ya kawo ki.”

Saida ta gyara tsayuwarta sosai sannan tace “Tunda abun nan ya faru ka canza min, na baka hak’uri har na gaji, Hajia da su Hajiar Jibril ma duk sun tayani baka hak’uri, amma abinda na fahita shine baka hak’ura ba har yanzu, a gaskiya na fara gajiya da irin halin ko in kular da kake nuna min, shine nake so ka fad’a min a me kake kallo na ne? Sannan me ye matsayi na a wurinka yanzun?”

Cike da nuna rashin damuwa kan maganar ya d’auki hularshi ya saita zamanta yana fad’in “Duk irin zaman da kike tunanin kina yi shi kike yi.”

Jakarshi ya d’auka zai fita tayi saurin tare da gabanshi tace “Wannan wace irin magana ce? Abban Ammar ka tsaya muyi magana.”

Kallon fuskarta yayi cikin yanayin firgitarwa yace “Na gama magana ni ba zan b’ata lokaci na anan ba.”

Zai fita ta rik’e hannunshi tace “Nima ina so na kawo k’arshen abun ne, dama zamanka na ke a gidan nan, idan ka juya min baya banga anfanin zaman nawa ba.”

Shiru tayi ta ja numfashi sosai sannan ta ci gaba da cewa “Ina so ka min magana d’aya kuma tsayayya, idan ka gaji da zama dani ne to na san inda dare ya min? Tunda kafi kowa sanin inda ka d’auko ni ai.”

Ba tare daya kalleta ba yayi murmushi mai ciwo yace “Ni kuwa nasan inda na d’auko ki, da kai tsaye kika fito kika fad’a min abinda kike so, amma…”

K’ofa ya nuna mata yace “Hanya a bud’e take ban rik’e miki k’afa ba, zaki iya tafiya ko yanzu ma.”

Zai wuce ta sake rik’oshi da k’arfin da Allah ya hore mata tace “Ba zan tafi ba tare da shaidar komai ba, tunda haka ka ce to ka ban takardar da zan nuna ta zama hujjar tafiyata kenan, dan in na tafi ma bana son dawowa.”

Kallonta yayi yace “Kije zan aika miki da ita, yanzu bana da lokacin tsayawa rubutu.”

*Maza mutanen mu, mu ke shayar daku amma in kuka labta mana wata tsiyar…hummm*

Da sauri tace “Zan tafi yanzu, amma ka sani ina jiran takardata gobe goben nan.”

Wucewa yayi yana fad’in “Anfanin me ma zata miki yanzu ko an baki? Ina ce zaki koma gidan nan da ki ci gaba da kulawa da yan uwanki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected