BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mik’ewa tayi tace “To kaji da kyau, wallahi ban yarda da zamanta a gidan nan ba, kuma kasan Hajia ma ba zata yarda ba, dan haka kafin ta muku wankin babban bargo ka gaggauta fitar da ita a gidan nan, idan ba haka ba babu ruwana duk sanda ta zo cin mutumcinka.”

“Indai hakane to ni kawai zan koma gida na, dama ban so zama anan ba kawai Alhaji ne yasa na zauna.”

Fita yayi daga d’akin ya barta tana bambami, yasan za ayi haka dama shiyasa ya shirya juya, a farfajiyar gidan ya sameta nan ya mata sallama ya fita, gidansu ta koma amma madadin ta shiga wurinta saita wuce b’angaren da bata da masaniya ko na waye, saida ta shiga da sallama a k’ofar d’akin suka ci karo da Amar zai fita, gaisawa sukayi a mutumce ya wuce, saida taga fitarshi saita wuce b’angare na gaba dan ba Umaimah take son gani ba, anan tayi sa’ar samun Jibril ko fita baiyi ba, ganinsu yasa Jamila saka hijabi akan k’ananan kayanta suka gaisa, suna zaune ya fito da alama tashinshi kenan, Huda na ganinshi ta ruga ta rumgume shi tana fad’in “Lahhh Abba, ina kwana.”

Rintse ido yayi tare da gumtse baki yace “Shit!” A zahiri kuma bud’a ido yayi ya mata dariya ya rik’e hannunta yace “Yah beby Huda, ya kike? Yaushe kika zo gidanmu? Kin zo wajen mamanki?”

Da fari fad’uwa gabanta yayi jin yarinyar ta kirashi Abba daga ganinshi, amma yanzu tana son sanin dalilin da yasa ta kira shi da haka, kafesu tayi da ido tana kallo, har suka k’araso ya zauna nesa da ita Huda na mishi magana, a kaikaice ya kalleta yace “Madame ya kike?”

Wani shed’anin kallo ne take masa wanda bai dace ba, saida tayi murmushi tace “Lafiya lau Abban Huda, ka tashi lafiya?”

Saida ya d’an rarraba ido yace “Lafiya lau, ina mutumin ko har ya fita?”

“Ya fita.” Ta fad’a tana kafeshi da ido, ganin ba zai juri wannan kallon ba yasa shi sakin Huda ya mik’e zai koma ciki, da sauri Maryama tace “Abban Huda nace ko zamu iya magana?”

Yawu ya had’e da k’arfi sannan ya juyo ya kalleta, Jamila ma da baki sake take kallonsu, cikin dai k’warewa ta bariki ta mishi alama da kai da ido cewa su fita waje mana, mik’ewa tayi tana rik’e da hannun Huda ta fita, bayansu ya bi jiki a sab’ule yana kallon yanayin yar matarshi wacce ke jin kamar ta shekara a soyayyar mijinta duk ta fara zufa, suna fita k’ofar d’akin ya tsaya ya rufe yace “Lafiya? Me kikeyi haka Maryama?”

Da yatsa ta nuna shi tace”Dakata malam, dama dan na fad’a maka Huda ta dawo nan da zama ne, ba wai dan mahaifiyarta na aure nan ba, a’a sai dan nan gidan ubanta ne, gidan da ko babu ni a raye nan ne yafi dacewa data rayu, dan haka ka fara shirya nuna mata gata ita ma tasan ‘ya ce.”

Juyawa tayi zasu wuce sai kuma ta tsaya ta kalleshi tace “Anjima zan bata ta kawo maka takardar haihuwarta, ina buk’atar ka canza mata makaranta ita ma, ya rage naka ka samar mata dreba ko kuma ka kaita da kanka ko ma ta tafi a k’afa duk matsalarka ce.”

Wucewa sukayi ta barshi tsaye kamar zai kashe kanshi, wane bala’in ne kuma wannan ke shirin danno mishi kai? A haka ya dawo d’akin Jamila na gyara teburin cin abinci, ta baya ya rumgumeta yana shinshinar wuyanta, ba alamar wasa a amon muryarta tace “Me yasa take kiranka Abban Huda?”

Dakewa yayi duk da fad’uwar da gabanshi yayi yace “Saboda ni da Junaid duk mun ce mata mun zama iyayenta, yarinyar kullum damuwarta ita ce mahaifi, amma yanzu kinga ta daina.”

Ba tare daya saketa ba ta juyo ta shafa kumatunshi tace “Je kayi wanka ka fito ka ci abinci.”

“To.” Kawai yace ya shiga d’akinshi da tunanin k’ananan iskancin da Maryama ta taho mishi dashi kuma, shiryawa yayi ya fito ya sameta suka karya.

Amar na saman hanya lieutenant ya kira shi kan yana so ya tura ma Ammar kud’i ya bashi lambar account d’inshi, dan a ganinshi daya tambayeshi kud’i to baya da su ne shiyasa, ba dan haka ba zai tambaya ba dan rabon da sisin kwabo ta shiga tsakaninsu dashi har ya manta, tun bai fara aikin likita ba ya tsaya da k’afafun, matsala ko wacce ta shafi karatunshi ce shi ke tsaya ma kanshi. Amar dai cewa yayi wallahi baisan komai a game da abinda ya shafi Ammar ba, shi kuma lieutenant yana jin ba zai iya tambayar Ammar d’in ba dan haka yace Amar ya bud’e mishi sabon count a bankinsu, yana zuwa aiki ba b’ata lokaci yayi komai ya ga sai sa hannun Ammar da yake buk’ata, hakanne yasa shi kiranshi dan ya fad’a mishi ya zo, amma mummunan labari sai police ya d’auki wayar ya fad’a mishi abinda ke faruwa, tun saman hanya Amar ke maimaita jikka sha biyar d’in me da Ammar zai yarda a d’aure shi akan ta, da wannan takaicin ya isa ofishin yayi bailinshi.

Ana fitowa dashi ya ga Amar ne sai yaji ba dad’i, tsaye yayi yace “Dama wannan yaron ne ya zo fito dani? To babu inda zanje.”

Rai b’ace Amar yace “Ammar kar kayi taurin kai mana, ba wasa na zo yi ba.”

“To yi min fad’a ubana.” Shiru Amar yayi yana kallonshi, ni yake kamar ya rufe shi da duka, amma yasan ko yayi haka shine zai sha wahala, a kausashe yace “Wuce muje.”

“Babu inda zanje, an fad’a maka ni bana da kud’in fitar da kaina ne? Abba nake si ya zo wajen nan, inba haka ba kuma ina nan wallahi.”

Juyawa yayi cike da takon isa da k’asaita ya shiga ciki aka rufe shi, harara Amar ya dalla mishi daga nan yace “Kai ka sani ka tabbata anan.”

Da kallon zaka gane kurenka ya bishi yace “Zamu had’u ne zaka san ka harare ni yaro.”

Da fari Amar shafawa yayi da al’amarin ya shiga harkokin gabanshi, saida ya tuna waye tagwaicinshi kad’ai ya sake kiran lambarshi, yanzu ma police ne suka d’auka, dan haka baiyi k’asa a gwiwa ba ya garzaya douanes ya samu lieutenant, yana fad’a mishi lieutenant ya rufe ido yana zabga masifa ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, cewa yayi ya tafi kawai ya barshi can shiya sani amma shi babu inda zaije.

Ummy ya kira a waya da niyyar yace ta lallab’i Abba, amma sai yaga tafi ma d’aukar zafi fiye da Abban, ita ma haka ya rabu da ita ya kira wayar Ammar aka bashi shi a waya, rarrashin duniya yayi dan ya fito amma Ammar sai yaga rayuwarshi ma bata da anfani, kenan babu wanda zai zo? Kashe wayar yayi ya bayar aka aje ya koma ya kishingid’a kamar a gadon sarauta yana ci gaba da tasbihi ga ubangiji yana kuma jiran yaji wa zai zo.

Bayan magriba lieutenant ya dawo gida, a d’aki ne yake fad’a ma Zeituna cewa “Kinji wannan mahaukacin yaron abinda yayi?”

Tasan sarai da wa yake dan haka bata kula shi ba ma dan bata ji dad’i ba, saida ya kalleta yace “Dake fa nake magana kina jina.”

Cikin d’an fad’a fad’a tace “To me kake so nace maka?”

“Ban gane ba? Ina fad’a miki Ammar yana ofishin yan sanda kuma d’an uwanshi yaje yayi belinshi amma ya k’i tahowa wai sai naje da kaina, shine zaki fad’i haka.”

Cikin gatse tace “Oho ashe sunansa Ammar, ai na d’auka baya da suna ne.”

Kallonta yayi yace “…

*Comment ya sani muku typing, ku ci gaba da haka zakuji bayani.*

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected