BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Kallon Hamna yayi yace “Kinga kakana nan ta mayar dani kamar katinta na kud’i, sai dai tace kawo, kawo, kawo kullum a haka.”
Ba tare data kalleshi ba tace “To idan bance kawo ba wa zan ce wa, ka hanani fita inda zan samu kud’in dole ka zama katina ai.”
Gwalo ya mata yana fad’in “Hanjin doguwa ce kike ci ta cikin ruwa.”
Ita ma gwalon ta masa tace “In ma dai ta cikin k’asa ce na ci, mu ai haram d’in ita ke girman da k’assan jikinmu.”
Kallon Sayyada yayi yace “Kina ji ko uwa, yarinyar nan fa yanzu yar daba ta zama.”
Tab’e baki Sayyada tayi tace “Karka damu zata daina idan taga ka mata kishiya.”
Haka dai sukayi hirarsu cikin raha kafin ta mik’e zata koma, jaka sha biyar ya bata yace ta shiga taxi canji saita ci goro, godiya ta masa ta fita ya rakata har k’ofar gidan tare da Hamna, har zai bi bayanta Hamna ta rik’o rigarshi tana fad’in “Ina kuma zaka tafi? Malam muje ciki.”
Kallon Sayyada yayi yace “Uwa zan kiraki a waya muyi sirri, yanzu d’iyar nan tafi k’arfina.”
*Bayan sati biyu*
Tun jiya dai taga kai da kawonshi ya k’aru sai kaya kaya yake, yau kuma bata san me ya faru ba tun a waya dai taji yana ta fad’anshi, zaune yake kan teburin cin abinci yana daddana wayarshi yana ta sababi kuma, ita dai jera mishi abincin ta shiga yi da duk abinda yake buk’ata k’ala ba tace mishi ba, zuba mishi tayi ta aje mishi gabanshi ta zauna kusa dashi dan ta saba tana kallon tv daga nan.
Kallonta yayi ya ga kenan ma babu ruwanta da damuwarsa ko? Cikin masifa yace “Nagode Hamna, dan ki nuna ni mahaukaci ne shine kika aje min abinci wato ina ci ina fad’a ko? Ki ma tambaye ni lafiya abun ya gagara sai ki zuba min ido kina kallo? To nagode.”
A hankali ta juyo ta kalleshi, yanzu da tace yi hak’uri yace kuma ta ci uwarta ita da hak’urin, sake juya kanta tayi bata ce mishi uffan ba, a hassale ya sake kallonta yace “Ah yayi daidai, yanzu kuma baki da lokaci na ko? Yayi kyau Hamna ki ci gaba da wulak’anta ni son ranki.”
Mik’ewa tayi ta kalleshi tace “Na d’auke abincin ne har ka gama saboda kar ya huce?”
Wani kallo ya mata irin yana so yayi magana amma baisan me zai ce ba, d’auke kanshi kawai yayi daga gareta yana datse leb’enshi dake rawa rawa tsabar fitina bai kuma samu abokin yi ba, juyawa tayi zata shiga d’akinta yace “Ke.”
Juyowa tayi ta dawo ta tsaya, kallonta yayi yace “Bani ruwa nasha mak’oshi na ya bushe.”
Cikin kwanciyar hankali ta tsiyaya masa ruwa ta mik’a masa, karb’a yayi yasha ya aje kofin ya kalleta yace “Mak’ogwaro ya fara ciwo wallahi.”
Cikin nutsuwa tace “Idan baka kiyayi saurin hawan nan ba zaka jawa kanka matsala.”
Yana ci gaba da kallonta yace “Wai yanzu nan fad’a gareni sosai? To ni ina na samo wannan bak’ar zuciya?”
Murmushi kawai tayi tace “Ina ma zakayi koyi da Alhaji, da ka zama mafi dacen rayuwa wallahi.”
A k’ufule yace “Ke fito fili ki ce Ammar kai masifaffe ne kai mafad’aci kai jarababbe ne, anje anyi d’in to inba tab’aka akayi ba ai haka kawai ba kayi fad’a ba.”
Juyawa tayi ta bar masa wurin dan ta lura da tsiya ne take so ya jata ta biye masa k’arshe ya turmusheta kuma ya d’inketa da kanshi, sauk’inta d’aya ma yanzu ciki dake gareta bai cika mata wannan hawan k’awarar ba.
Ko da ya ga zata shige d’aki ya d’auki cokalin abinci yana bubbuga teburin yana fad’in “Yeeee, ku dubi matar dake kallon mijinta masifaffe, an daiji kunya wallahi, kuma sai nayi mata uku a lokaci d’aya naga wanda ya isa ya hana ni.”
Ko juyowa ba tayi ba har ta shige tana jin shi yana ta sambatunshi, saida ya gama yayi wanka ya shirya zai fita ya same ta a d’akin, bai kai ga mata magana ba kuma wayarshi tayi k’ara, yana dubawa ya ga Sayyada ce, tun ranar data zo ya kirata sukayi magana kan ranar haihuwar Hamna da zata zagayo yace yana so ya shirya mata party a gida, shi kuma yana so ya mata bazata shiyasa ko da ya ga kiran saiya d’auka yace “Oui zan sake kira idan na fita.”
*Mata muke fa, kowane yare na maza ganeshi muke cikin sauk’i*
Daga jin yace zan kira bai ce zan kiraka ba kenan ba namiji bane, sai kuwa Hamna ta sauko daga kan gadon tayi kafar da wayar ta d’ora a kunne tana fad’in “Hello! Hello.”
Fizge wayar yayi yana fad’in “Ke me yake damunki ne?”
Cikin d’aga murya tace “Abinda yake damunka, Ammar amana ta kake ci? Wace yar iska ce ke kiranka har cikin gida?”
A hassale shima yace “Wai ke kullum sai ki ce yar iska, to duk matan duniya yan iska ne? Ke ma fa macece saiki dinga kiransu da yan iska?”
Cikin b’acin rai tace “Saboda yar iska ce kawai zata kula min miji.”
Kallonta yayi yace “Fito kai tsaye ki ce nine d’an iskan mana, idan ban kulasu zasu kulani ne? Kinga kenan nine kike so ki zaga dama.”
Wayarshi tasa hannu zata fizgo tana fad’in “Na ga wayar to.”
Hannu ya d’aga kamar zai mareta yana fad’in “Idan ban mareki ba Hamna kice Allah ya tsine min, ke bari gani ina k’yale ki fa.”
“To ka da ka k’yale ni d’in ka kashe ni.”
Zaune tayi kan gadon ta fashe da kuka tana dafe cikinta tana fad’in “Daga yau zan fara addu’a Allah ya cire min sonka, tunda dai dan kaga ina sonka ne kake wahalar dani, me ye gare ni da ba zaka iya rayuwa dani ni kad’ai ba? Kullum tunani na shine yanda zan faranta maka amma kai ba haka ba.”
Da sauro ya zauna kusanta ya rumgumota a jikinshi yana fad’in “Kai kai kai Hamna, karki fara wannan addua’r dan Allah, kinsan kuwa yanda nake ji idan kina wannan sababin akan kishina? Wallahi karki tona raina kiji farin cikin da nake, kamar yanda nake kishinki nake jin zan iya komai haka nake so ke ma kiji a kaina, kiyi hak’uri kinji.”
Kaallonshi tayi tace “To wacece ta kiraka yanzu?”
Wayar ya fito da ita ya mik’a mata yace “Duba ki gani.”
Dubawa tayi kam ta ga sunan Sayyada, kallonshi tayi tace “Sayyada ce ta kiraka ba zaka iya magana da ita a gabana saika fita, wani abu ne tsakaninku?”
Da sauri ya dafe k’irji yace “Ni? Wallahi babu komai, ki yarda dani.”
Kallonshi tayi da kyau tace “Allah yasa haka, amma ka sani Ammar duk ranar dana ji wani abu ya fito tsakaninku mai kama da soyayya ko aure saina maka sabon yanka.”
Zaro ido yayi yasa tafukan hannayenshi ya rufe baki yana fad’in “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un, Hamna gaba d’aya fa anan mazan suke.”
Ba alamar wasa tace “Saboda nasan anan suke d’in ai shiyasa suke alamta maka daka kalli matar da ba taka ba ai.”
Tab’e baki yayi yace “Gwara ki kashe ni ai da ki tab’a min kayan aiki na.”
Murmushi tayi tace “Ai saboda su d’in ne zakayi sha’awar k’ara aure.”
Kallonta yayi yace “Ke ma ba zaki iya zama dani ba ai idan da bana tsoratarwar nan.”
Cike da tabbaci tace “Zan iya mana, kuma ita Sayyada ai zata iya tunda yar uwarka ce.”
Mik’ewa yayi yace “Ke babu aure tsakani na da ita fa.”
Ita ma tsayen ta mik’e tana fad’in “Inji wa yace? Ai ko su Abba akwai aure tsakaninsu da ita bare kuma kai.”
Ba tare daya kalleta ba yace “Ni ai Sayyada ma bata cikin tsarin irin matan da nake so, ni nafi son masu manyan cinya da mazaunai yanda idan na shiga zaiyi luf abuna.”
Kallon sama da k’asa ta mishi tana fad’in “Kace haka mana, kafi son irina yanda zaka ji dad’in b’arka mu kana d’inkemu.”
Dariya yayi yace “Ai da kinga na miki d’inki to kin b’ata min rai ne.”
“To me yasa ba zaka hukunta ni ta wata hanyar ba sai wannan? Kana so ka lalata ni ne?”