BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Da suka dawo gida ma zasu kaishi b’angarenshi ce ma Junaid yayi “D’ora min shi a baya.”
Saida yayi dariya yace “Kamar wani yaron goye, dan Allah ka barshi zai tafi da k’afarshi.”
Amar ma cikin yanayin jigata yace “Zan iya tafiya, nagode.”
Kallon fuskarsa yayi ya masa gwalo yace “Ka daku fa, wai waya dake ka haka kana tsaye kana kallo kuma?”
Saida suka fara takawa suna rik’e dashi yace “To ni ina na sani, rufeni kawai sukayi kamar Allah ne ya aikosu.”
Ammar ne yace “To me ka musu? Fad’a kake yi dama a waje?”
Murmushin k’arfin hali yayi yace “Fad’a dai Ammar? Haba dama dai kaine ai ba za ayi mamaki ba, na sani yanzu ma wani ja tsokana shine ya sauke akai na da tunanin ni ne kai, ai kasan ba yau aka saba haka ba, kankana ma nasha cutuwa a hannunta idan ta tashi zuwa d’aukar fansa.”
Shiru Ammar yayi, tunanin kalaman Amar yake yi, tabbas fa maganarsa gaskiya ce, to idan fa hakane? Amma waye ya zo dukanshi ya daki d’an uwanshi? Wane mai k’arar kwana ne wannan? Har suka kai b’angarenshi bai iya tunawa ba, to ai abun dayawa ba zai iya cewa gashi ba, shi ya sani a dangi ma ana jin haushinsa bare kuma waje, duk da dai wanda fad’a ya tab’a had’asu dashi na akai ga jiki ba yawa ne dasu ba, shi ma kuma shi ne ke saurin kai hannu maimakon cacar baki, wanda kuma ya dank’arawa magana da zagi da yan k’ananun abubuwa basu da adadi, Jano kuma da yayi sanadiyar shigarshi gidan maza shi bai ma san a ina ake ba yanzu, dan tunda aka kama shi ya rufe babinshi ya shiga wata sabgar, sai wanda ya daka suna tare da marigayiya Amna, sa kuma wannan na jiya shima, to cikinsu kuwa akwai wanda ya daki d’an uwansa.
Saida suka shiga suka zaunar dashi Farisa da Umaimah hankali tashe suke tsaya kansu suna tambayar me ya faru dashi? Babu wanda ya basu amsa sai Ammar daya kalli Farisa yace “Ku samo mishi abinci ya ci yasha magani.
“To.” Ta fad’a tana nufa madafa, Junaid ma fita yayi yaje ya sanar da iyayensu, dukansu suka rukuto suka taho da mamakin abinda ya fad’a musu da kuma jimami.
Ko da Junaid ya fita ya kalli Amar yace “Dan ubanka fad’a min wa kayi fad’a dashi?”
“Allah babu kowa, to wai me zai kaini fad’a kamar marar aikin yi ko yaro k’arami.”
Ko da su Hajia suka shigo sun samu yana fad’in “To inba wani abu kayi ba wa zai maka wannan dukan har da karya maka hannu.”
Cikin tashin hankali suka jajata masa suna tambayar ba’asi, maganar dai d’aya ce bai san komai ba kawai an rufe shi da duka ne, sai lokacin Junaid ya fara lalaba aljijunshi yana fad’in “Bari kuga abinda na gani kusa da inda na same shi kwance, abun yafi kama da d’aukar fansa.”
Firo da takardar yayi ya mik’a ma Ammar, daki daki ya shiga kallon kowace kalma yana hardaceta a kanshi, kowa ya zuba masa ido suji me zai ce sai ji sukayi ya gunduma wata ashar yana fad’in “Kuturun uban cen, ni? Yanzu nine wannan yaron ya ma tarko dan ya dake ni? Shine har da wata tsinanniyar wasik’a yana kirana da dak’ik’i, kankana kuma ita ce banzar? Banza fa, bayan yace min mai k’walwar kifi, ah lallai.”
Mik’ewa yayi yana jefar da takardar zai fita Junaid ya rik’oshi yana fad’in “Ina zaka je Ammar? Ka wa Allah da manzonsa abun ya tsaya iya haka?”
Kallonshi yayi yana murmushi yace “Haba dai kaima fad’a kawai kake, k’anan na wa su masa wannan dukan sannan ya kira kankana da banza, ni kuma dak’ik’i mai k’walwar kifi kuma ka ce na k’yale, to miye anfani na kenan inhar zan iya yin shiru kan wannan cin zarafin.”
Zai wuce ya sake rik’eshi sai Hajia da tace “Ammar dan Allah dan uwarka Sa’ada ka k’yaleshi koma wanene, kaga dai abinda ya faru yanzu bala’in ya fad’a kan d’an uwanka, ita fa fitina kwance take mu ne ke tashinta.”
Hajia ya kalla yace “Dan Allah Hajia ki cire bakinki a maganar nan, abu d’aya da nake so dake shine ki kira tonton colonel ki fad’a masa yau zanyi kisan kai ya tanadar min wuri a gidan maza, mazan ma k’arti manyan yan ta’adda.”
Husseina ce tace “Subhanallah, mun shiga uku mu kam, Ammar kisan kai?”
Ko kallonta baiyi ba ya fincike a hannun Junaid ya tunkari fita, karo suka ci da kankana da yara suka fad’a mata iyayen na b’angaren tonton Amar, bata san hawa ba bata san sauka ba kawai yace “Yar banza mai shegen farin jini, to yau dai gashi banzan lusarin saurayin naki da kika kunyata iyayenki akan shi shine ya turo miki sak’o yake kiranki da banza, wai banzar k’anwata na dafa ki na cinye.”
Ita dai da bata fahimci komai ba wucewa tayi ta gaishe da Amar tana masa ya jiki, dawowa yayi yana kallonta ya ci gaba da zazzaga masifa wai duk ita taja, ko kallonshi ma ba tayi bare ta kula shi haka kowa ma yaja baki yayi shiru, saida ya kalli kowa yace “Eh mana ga d’an iska mahaukaci na magana, dole kowa ma yayi shiru, to ni na tafi sai kunje gani na a gidan yari.”
Kamar zai tashi sama ya nufi k’ofar fita cikin rashin kunya Umaimah tace “…
*Insha Allah zanyi k’ok’ari nayi wata page d’in anjima amma fa idan kunyi comment, ku shirya kowa ya kawo goron d’aurin auren fitinannu na.*
*Alhamdulillah*
04/11/2020 à 14:38 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_69_
“Yanzu dama akan ka ne aka dakar min mijina? Dan Allah yah Ammar wace irin rayuwa ce wannan kai da jan masifa shi da shan duka? Ya kamata fa ace kasan ka girma amma irin haka bai kamata ba, yanzu gashi baisan hawa ba bare sauka kawai an sauke mishi kwandon rashin mutumci, gaskiya dai akwai alhaki wallahi Allah ma ba zai barka haka ba, haba mutum sai jaraba kawai k…”
Kamar saukar aradu kowa yaji Hamna ta daka mata tsaw da cewa “Ke.”
Juyawa tayi ta kalleta suka shiga kallon kallo kafin ta nuna mata shi tace “Umaimah tsaranki ne shi da kike fad’a masa haka? Saboda an daki d’an uwansa wanda na tabbata baki fi shi jin zafin a zuciyarshi ba, ki tambayi shi yah Amar d’in kiji kafin ki ci masa albasa, shin yana jin haushin d’an uwansa kan abinda ya faru yanzun?”
Cikin rashin mutumci tace “To ke kuma a wa? Dake nake bare ki sa min bakinki? Ki bari shi da nayi dashi ya tanka min mana amma bake ba.”
Murmushi ta mata tace “To ai naga ba shi ne daidai ke ba, ni nan ni ce daidai da ke wallahi.”
Ammar dake kallon ikon Allah saiya bushe da dariya ya nemi kujera ya zauna yace “Buga min ita a k’asa kankana, yau saina cika miki gidan nan da kankana Allah kuwa.”
Kallonshi tayi ta dalla masa harara ta mayar da hankalinta kan Umaimah da tace “Kin tare masa saboda ke ce daidai dani? Ko kuma kin tare masa saboda shine uban d’anki?”
Hajia da Husseina ne suke musu magana amma bata saurare su ba saida tace “Ki d’auka a yanda kika ga zai fi miki sauk’in d’auka akan ki, amma idan zan zab’ar miki sai nace barshi dan yana uban d’ana, ai kinsan saduwa ba k’arya bace, haka ma haihuwa ba wasa bace, ai ke wannan abubuwan biyu ne yasa kike tayar mana da jijiyar wuya saboda an tab’a mijinki, ke ga mai miji maji dad’in miji.”