BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Saida ta daure sosai kafin ta samu k’warin gwiwar cewa “Wajenka na zo mana.”

Fizgo hannunta yayi ya mik’ar da ita tsaye yana fad’in “Amna baki da hankali ne? D’an iska kika mayar dani ko me? A wannan lokacin kika fito daga gida kika zo nan kuma da wannan shigar?”

Kallon kanta tayi, riga da siket d’in na leshe wanda suka amshi jikinta sune matsalar? Ko kuma d’aurin data b’ata lokaci ta kashe wajen d’aura shi? Kwalliyar fuskarta ko kuma mayafin data yafa? Kallonshi tayi tana turo baki gaba duk tayi kalar wallahi kuka zan ma ka tab’ani, a hassale yace “Billahil azim kifar dake zanyi wurin nan kika min kuka, ke ni d’an iska ne?”

Girgiza kai tayi da sauri tana fad’in “A’a.” Rik’e k’ugu yayi yace “To uban wa yace ki fito haka? Kuma waya kawo ki nan?”

Saida ta k’ara yin kalar tausayi sannan tace “Aunty Zeituna ce.”

“To waya kawo ki?” Ya sake jifarta da tambayar, saida ta d’anyi baya kad’an tana kallonshi sannan tace “Adaidaita…Ahhhhh.” Ta fad’a da k’arfi saboda d’aga hannu da yayi kamar zai kifeta da mari, a hankali ta bud’e idonta jin bai sauke mata yatsunshi ba a kumci, kallonshi tayi sai taga ya k’ura mata ido yana kallo, da kankana ce da yanzu ta zuba a guje, amma ita
saita tsaya ko kasheta zaiyi, abun ne ya bashi dariya sai kawai ya figo hannunta ta fad’a jikinshi ya rumgumeta yana dariya yace “Mahaukaciya, ke baki iya guduwa ba idan za’a dake ki.”

Cikin shagwab’a tace “To yah Ammar taya zan iya tsere maka? Mai guduwarma (Hamna) naga in kayi niyya kana ritsata duk inda take.”

Lumshe ido yayi yana sakin murmushi kafin ya d’agota yace “Yanzu to ki koma gida, amma k’asa zaki tafi in ba kya son ki jazawa masu adaidaita bala’i, kinji ko.” Ya fad’a ba alamar wasa a tare dashi.

Shagwab’e fuska tayi tace “To ai ni ban zo dan na koma ba, nan zan kwana tare da kai.”

K’ura mata ido yayi yana kallo, ya jima yana tausar kansa kafin yayi nasarar kwantar da hankalinshi yace “Amna kuka kike so kiyi ne?”

Da sauri ta rik’e hannayenshi tana fad’in “Bana so, amma kuma ina nan tare da kai yah Ammar.”

“Me yasa?” Ya fad’a yana son k’watar hannayenshi, saida ta langab’e kai tace “Aunty Zeituna tace idan na zo nan dole Abba ma zai zo yayi belinka da kanshi.”

Kallonta yayi sosai yayi murmushi yace “Uwa ta shiga al’amarin?”

Kai ta jinjina masa alamar eh, sai kawai ya zauna kan bencin ya sashi tsakiya yace “Zuba min abinci na ci kinji yarinya, tunda uwata ta shiga lamarin nasan ma dole zai zo.”

Murmushi tayi ta fito da kwanukan ta soma zuba mishi abincin, har ta d’auki cokali zata fara bashi saiya girgiza mata kai, aje cokalin tayi ta wanke hannunta ta fara bashi da hannunta, yana ci yake ce mata wai tayi hak’uri na rashin zamanshi gida a tare da ita, uffan ba tace ba sai yanka mishi loma da take tana aika masa.

Tana komawa b’angaresu ta samu lieutenant a inda ta barshi, shiga tayi ta tsaya gabanshi tana kallonshi, ta jima tsaye amma bai motsa ba alamun baisan da zuwanta ba, ajiyar zuciya ya sauke tare da d’an juyo da kanshi hakane yasa ya ganta, cikin basarwa ya d’an had’e fuska yace “Ya dai?”

Murmushi ta masa tace “Ba komai.”

Bai ce komai ba sai juyar da kansa da yayi, ita ma ba yanayin wasa a tare da ita tace “Yallab’ai akwai matsala fa.”

Kallonta yayi yace “Matsalar me kuma?”

Saida ta gyara tsayuwa ta mayar da hannayenta bayanta sannan tace “Yanzu daga b’angaren Amna nake, na sameta tana ta kuka saboda rashin sanin halin da mijinta ke ciki, dana fad’a mata tayi hak’uri dan ba zaka je ka fito dashi saita d’auki mayafinta ta fita, da k’yar ma ta fad’a min tace zata je wajen mijinta ne tunda babu mai k’aunarshi.”

Kamar an tsikare shi haka ya tashi tsaye yana mata wani mugun kallo cikin d’aga murya yace “Babu mai k’aunarshi? Wai wace irin magana ce kikeyi haka? Taya kike tunanin zamu haifi d’an a cikinmu amma mu ce ba ma k’aunarshi, akan me zaki fad’a mata haka kuma har ki bari ta fita a wannan lokacin, ke a ina kika tab’a ganin haka?”

Ba tare data nuna tsoron yanayinshi ba tace “Akan ku mana, kanku na fara gani.”

Jinjina kai yayi yace “Ok, to ni kuma yau zan nuna miki k’arya kike, ina son d’ana kuma ina k’aunarshi fiye da komai dana mallaka a duniya.”

Fuuu ya rab’ata zai wuce cike da shak’iyanci sai cewa tayi “Taya zan tabbatar ina daga nan bansan me ya faru a can ba?”

Tsayawa yayi ya juyoya kalleta da mamaki, raina shi ne tayi kome? Shi kananta ne da zata mayar dashi abokin wasanta? Saida ya jinkina mata kai yace “K’arfin shaukin da zan nuna masa zai riskeki har gidan nan.”

Juyawa yayi ya fita ta bishi da murmushi Allah ya bada sa’a, tun a hanya yake k’ulla kalar k’aunar da zai nuna masa, to wai a kan me zata fad’a masa baya k’aunar d’an shi, ko bata san shine sanyin idaniyarshi na farko bane? Bata san duk suna mishi abinda suke mishi ne ba dan suna son ya gyaru ya zama na k’warai? Ta manta da duk fafutukar da yake saboda ‘ya’yanshi yake yinta sannan Ammar shine magajinshi na farko? Me yasa bata tambaye shi me yaji ba a sanda aka fad’a mishi an rufe mishi? Amma ba komai zai nuna mata ba haka bane abinda take cewa ta ganin, da wannan tunanin ya isa ya baka tsandareriyar motar data sanar da jami’an babban mutum ya shigo, sanin sosai suka masa ba sanin shanu ba, dan haka suka sara masa cikin girmamawa ya shiga ciki, ikon Allah sai kallo, ganinshi hankali kwance matarshi na ciyar dashi cikin nishad’i, abinda ya aikata ya cancanta ya bibbige shi amma ba hali, k’wafa kawai yayi ya shiga inda zai samu belinshi. Cikin mutuntawa aka fad’a mishi ai Amar ya biya tarar kawai zasu iya tafiya, amma gobe da safe saiya dawo a musu sulhu saboda gaba, duk da haka saida ta d’ebo kud’in da baisan ko nawa bane ya zube kan teburin kafin suka fito, sai lokacin ne suka ga lieutenant, hannu ya d’aga masa yace “Abbana barka da dare, har ka iso?”

Tasowa yayi daga bencin kamar k’aramin yaro sai kawai ya rumgume shi yana wani k’amk’ame shi da kwantawa kan k’irjinshi yana fad’in “Nasan kana min son da baka ma kowa Abba, dama nasan zaka zo, ba zaka iya bacci a gidan can ba idan bana gidan nan, ko ba haka ba?”

Abun yafi k’arfin tunanin lieutenant, sai kawai ya tsinci kansa ya rumgume shi shima har da shafa kansa yana murmushin da baisan ko na miye ba yace “Gaskiya ne, ai indai har zaka kwana a nan to sai dai in gaba d’aya ahalin Gaga ne suka tare a wurin nan.”

D’ago kai yayi ya kalleshi ba tare daya d’aga daga k’irjinshi ba, turo baki yayi gaba irin tunda na samu ka biye min to bari na yi abinda na jima ina kewarshi daga gareku, sai k’ara narkewa yake jikinshi kamar zai shige cikinshi, Amna dake kallon ikon Allah tashi tayi ta wanke hannunta ta had’a kayan, kallonta lieutenant yayi yace “Shikenan ‘yata sai ki taho wurin mijinki baki sanar da kowa ba.”

Murmushi kawai tayi kafin lieutenant ya d’agoshi daga jikinshi yace “To mu tafi ko?”

Kafad’a ya d’aga alamar a’a kamar yaron goye, kallon zan ci ubanka a wurin nan lieutenant ya mishi tare da cewa “Meye kuma?”

Cike da shagwab’a yace “Sai kace muje shalele.”

Anya yaron nan banda aljanu kuwa? Tambayar da lieutenant ya ma kanshi kenan, wato dan ya ga ya zo shine saiya mishi iskanci yasa ranshi ya b’ace har ya kasa yin abinda ya fad’a, daga Ammar d’in har Amna kallonshi suke suna jiran suji me zaice, rarraba ido yake ganin jami’in dake tare dasu ne kawai yasa yayi murmushi yace “To muje shalele.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected