BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
*Samun* labarin rashin kunyar da tayi a gidan yasa malam Rabi’u tahowa da ita har gidan, yace dole ta basu hak’uri kuma ba zai ba mijinta hak’uri danya maidata ba, duk da babu yara kuma ita kanta Zeinabu likita take kwana wajen Jamila, amma anyi katarin ta zo saboda zuwan colonel da zai kwana d’aya ya wuce *Mali*, gaban Hajia ya zaunar da ita tace “Dan Allah kuyi hak’uri da rashin kunyar dana muku.”
Jin wani murmushi da Hajia tayi yasa Maryama d’agowa cikin jin haushi, murmushi ta mata tace “Haba.”
Cike da iyayi Hajia tace “Ke ni fa abinda kikayi ko a jikina wallahi, kin tona mana asirin da bamu sani bane, dan haka ni banga abun damuwa ba, ban sani ba dai ko ga ita wacce abun ya shafa.”
Ta fad’a tana kallon Husseina, murmushi Maryama tayi ta kalli Hajia tace “Hajia ke babba ce a gidan nan, babu kyau fariya ga d’an adam bare ke musulma, bai kamata ki dinga tsarkake kanki da ahalinki ba, yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi halinsu ba, ko matan baki isa kiyi shaida akansu ba bare mazan, to wai ma akan me kike cika baki? Tare dasu kike fita? Ko kuma kina bibiyar duk abinda sukeyi ne a wajen? ko kuma a cikin gidan kina saka ido akan lamuransu? Ko d’aya fa ba kyayi Hajia, kuma a hakane kike ganin ya zama wajibi akansu su kare kawunansu? To ubangijin daya hallicemu ma ai muna sab’a masa bare kuma ke ‘yar adam.”
Mik’ewa Maryama tayi sai malam Rabi’u cikin barbarci da yace “Mari rashin kunyar ce har a gabana? Lallai kin rik’a.”
Nuna Hajia tayi tace “Malam ba rashin kunya bane, ita tana ganin kamar iyalinta sunfi k’arfin aikata laifi laifin ma kuma na zina, alhalin bata san tana tare dasu ba kuma suna kewaye da ita.”
A hankali Hajia ta sauke k’afa d’aya kan d’aya tana kallonta tace “Ban gane ba? Kinsan me kike fad’a kuwa? K’arya kike wallahi.”
Murmushi tayi tace “Babu maganar k’arya sai gaskiya, ya kamata ki farka daga baccin da kike Hajia ki tabbatar kin gano asalin kowane yaro daya fito daga tsatsonki, dan zai iya yiwuwa akwai yara dayawa wanda aka samu kafin aure kamar irinsu *Junaid*.”
Zunbur ta mik’e tana kallonta ido a tsaitsaye, da sauri Zeinabu ta dafe bakinta da hannun dama ta daskare a wurin, Husseina Soueiba malam Rabi’u duka sororo sukayi, Junaid kam bai d’auki abin babba ba ganinshi kawai sharri ne, matsowa yayi kusanta yace “Kisan me zaki fad’a Maryama, dan na rabu dake bashi zaisa ki min wannan sharrin ba, ba k’aramin abu bane wannan fa.”
Tab’e baki tayi tace “Dan ka rabu dani? To autan maza ne kai da zanyi bak’in cikin rabuwa da kai, kaga malam ka tambayi mahaifiyarka ta fad’a maka yanda komai ya faru, karka tsaya kana zare min ido.”
Malam ta kalla tace “Malam mu tafi, zasuji da matsalarsu.”
Tashi yayi yana waiwayen Husseina da shi dai yake son neman yafiyarta, suna fita colonel da lieutenant suka shigo tare da Alhaji cikin farin ciki, suna ganin yanayin mutanen wurin kowa yayi sororo ga Junaid yasa Zeinabu gaba yana magana k’asa k’asa yasa lieutenant k’arasawa da sauri wurin Hajia yace “Hajia lafiya? Meya faru duk na ganku haka?”
Colonel ma matsawa yayi kusanta yana karantar tsantsan tashin hankali daka fuskarta yace “Hajia lafiya?”
Dab’as ta zauna kan kujerar da kullum take jin dad’in zama kanta cikin isa da izza, duk yanda numfashinta ya fara barin gangar jikinta saida tayi k’arfin halin kallonshi cikin fitar da numfashi sama sama tace “Husseini..da gaske…ne.Ju…Junaid baaaa…”
Kasa k’arasawa tayi wanda hakan yasa colonel sunkuyar da kai, *wal’iyazu billah* shine abinda ya fad’a à ransa, kamar an jonata da kuran sai kawai ta tashi tsaye da k’arfinta, hannu ta d’aga sama da niyyar palla masa mari, sai kawai jikinta ya d’auki b’ari hannunta ya fara rawa da k’arfi kamar ta kama wayar lantarki, lieutenant da colonel d’in ne sukayi azamar rumgumata a jikinsu cikin tashin hankali lieutenant “Mu kaita mota.”
Da gudu Zeituna ta k’araso tana k’ok’arin rik’eta tace “Ku saketa zamu kamata.”
Soueiba ce ta taso da sauri suka kamata su kuma suka nufi mota, ana fita da ita sai asibiti wajen su Ammar, ganinsu ya d’aga musu hankali suma ba kad’an ba, Ammar da Ummy da kuma wata malamar asibiti ne suka rufa kan Hajia aka fara k’ok’arin ceto ranta.
*Awa biyu* suka d’auka kafin su fito fad’a musu halin da take ciki, Hajia kam dai…
*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_49_
Ammar ne yace “Cikin sarautar Allah komai ya daidaita, jininta ne ya hau sosai, amma yanzu mun samu mun shawo kan lamarin, ba wata bazarana a yanzu zaku iya komawa da ita gida, akwai magunan da za’a bata ta samu bacci.”
Alhaji ne yace “Ammar kana ganin zamu iya tafiya da ita gida tun yanzu? Me zai hana ba zaku barta nan ba ta samu ta huta.”
Dafa shi yayi yace “Ba komai Alhaji zaku iya tafiya da ita, kuma ko da wani abu ya faru ma ba gani ba duk da bama fatan haka.”
Sallamarta sukayi tare da Jamila ita ma amma sun rigasu tafiya, ko da aka je gida d’akinta suka kaita aka bata magani tasha, ba jimawa bacci ya d’auketa idonta na kan colonel da take matuk’ar son marin fuskarshi, suna ganin bacci ya d’auketa kowa ya sauke ajiyar zuciya, a tsanake Alhaji ya kalleshi yace “Husseini shin gaskiya ne abinda aka fad’a d’in?”
A hankali ya sulale ya durk’usa gabanshi duk da babu hawaye a idonshi amma muryarshi na rawa yace “Alhaji kuyi hak’uri ku gafarceni, kuskure na wallahi, hakan ya faru tun kafin a d’aura aurenmu, ta so na fad’a asan halin da ake ciki amma, Alhaji ina jin tsoron Hajia sosai, tsoron abinda zatayi yasa muke b’oye wannan sirrin har wannan lokacin, amma wallahi kullum da fargaban hakan muke kwana kuma muke tashi.”
Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke ya kamo shi ya tashi, kallon idonshi yayi yace “Husseini, ba’a gyara kuskure da kuskure, shiru ba shine mafita ba illa ma ya k’ara haifar da wata matsala, na so ace a lokacin ko ni ka tuntub’a da lamarin dan asan abunyi, abinda kukayi kuskure ne, kuskurenku ma akan kuskure kukayi shi, yanzu kaga me hakan ya haifar? Shi yaron da wane ido zai kalleku?”
A hankali ya d’aga kai ya kalli Junaid dake gefenshi, Zeinabu dama bata tafi asibiti ba saboda tafi Hajia ma shiga tashin hankali, kawai ita nata ya fito fili ne aka gani, k’yar kam idonshi cikin na shi, kallon babu wanda yasan na miye ma kawai suna kallon juna ne, cike da dattako Alhaji ya kallesu dukansu yace “Yanzu dai tunda haka ta faru kawai komai ya wuce, Junaid hak’uri zakayi wannan ita ce jarabawarka, kai kuma kai da ita sai kuyita istigfari wajen ubangiji, abun kuma a bud’e yake cewa yanzu shi ma magajinka bane.”