BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya fad’a yana nuna Hamna dake tsaye inda take yace “Indan har Ammar baiyi magana ba Amar zaiyi, idan Junaid baiyi ba Jibril zai tsawatar, idan Jamil baiyi ba akwai Abdul Rashid, in basu min magana ba akwai *Nura* akwai akwai akwai…etc, dole yara zasu gyara su kimtsu, dan in baka had’u da wane akan hanyarka ba zaka had’u da waninshi.”

A shek’e ya kalli kowa yace “Yanzu ma nasan akwai wanda zasu ce na tarasu ina musu rashin kunya da fitsara, to ku gafarce ni duk wanda na b’ata masa rai, kuma nayi mamakin zuwanku haka da gaggawa, watak’ila kun d’auka wata dukiyar ce aka sake ganowa da Alhaji ya bari, shine kowa ya zo d’aukar nashi kason, ba’a d’auka ni na kira taron ba.”

K’arashe maganar yayi da dariya, magana ta gaskiya akwai wad’anda a lokacin suka ji yaron ya birgesu, dayawa daga ciki abu ne da yake ci musu tuwo a k’warya, amma sai gashi yayi magana ya tab’o kowa. Gogan kam Amna ya kalla ya mik’a mata hannu, Amna da taji soyayyar mijinta ta sake huda zuciyarta cikin murmushi ta mik’o masa hannu ya kamota, saida ya kalli kowa yace “To ku rufe da salatin annabi, Allah yasa mu dace.”

Amna ya kalla yace “Duniyata muje ki sauke ni, a sama nake wallahi.”

Ta gabanta suka wuce inda kowa ya bisu da kallo, numfashi kawai kake ji na fita a wurin, sun jima zaune haka kafin Hajia ta sunkuyar da kanta tace “Kuyi hak’uri, yayi maganganu da dama a wurin nan, amma duka nice mai laifi saboda ni ce ban bayar da fuskar da za’a shiga shirgin iyalina ba, ba nayi haka bane dan bana so a rab’eni ko zuri’ata ba, kawai dai ina so ne naga tawa zuri’ar ta banbanta data kowa, ina so naga babu mutanen kirki irinsu, amma ban tab’a tunanin hakan zai zama matsala da zai iya kawo rabuwar kai ba, ku gafarceni dan Allah ku yafe min.”

Alhaji Mani ne yace “Kamar yanda yaron nan ya fad’a ne Hajia ba laifinki bane ke kad’ai, mgana ta gaskiya mu ma muna da laifi, tunda ko baki so zamu iya magana amma muka yi shiru, amma yanzu dai tunda k’aramin yaro ya d’ora mu a hanya sai a yafi juna a kuma gyara gaba.”

Su Hassana da jikinsu yayi sanyi ne yace “Allah ya yafe mana baki d’aya.”

“Ameen.” Aka amsa dashi duk d’akin sai kuma aka kwashi hira, Zeituna ce ta mik’e tare da su Shafa’atu tace suje to a d’ora girki, tunda an riga da an had’u kafin kowa ya tafi, madafa suka nufa sai mazan da suka fita waje, a wannan taro na wannan rana wanda Ammar ne silarshi har suka d’ora zubin kara wanda musababbinshi had’uwa ce ake son a dinga yi duk wata, ba’a fitar da yan mata ko yaran mata ko tsofaffi ba, duk mai so ne wanda ya ga zai iya duk wata, babu wanda ya yarda aka barshi a baya duk da za’a dinga zuba kud’i, amma a lokacin abun ya shiga zuciyar kowa ba kud’in ne abun dubawa ba sai girman zumuncin da za ayi.

*A dole* ta gyara ba dan tana so ba, (rubdugu) rubdugun da akayi akanta kad’ai yasa ta d’an saya shigarta, hatta su Amie ta daina yarda yanzu su zo gidan nan sai dai su had’u a salon d’inta, amma a haka wata rana Amie na zuwa amma bayan ta sako hijab.

*Bayan wata biyu* Hajia ta tisa k’eyar Hamna da Amna Umaimah dasu Jamila suka tafi hadj, wanda tafiyar Amna ta bawa mutane mamaki sanda aka ji ta tafi da ciki, lafiya sukayi aikinsu suka gama suka dawo lafiya, har yanzu ba wani hijab take fita dashi ba, sai ma uwayen rigunan data kwaso tafiyarsu masu kyau, kusan yanzu su tafi sakawa indai ba gida ka sameta ba ka ganta da riga da siket ko da zani. Yau ma tsaf ta shirya ta tafi wani babban mall dan siyayyar abin buk’atarta, ta shiga tana cikin duba abinda take so kawai suka had’e da Habib.

Kallon da yake mata yana tunanin ya mata magana ko kuma ya k’yaleta, shi fa ko yanzu aka yardar masa zai aure ta, amma ganin irin kallon da take masa yasa shi kallonta kawai shima, wucewa taje yi ta gabanshi sai kuma hanyar ta d’an matse, karkatawa tayi zata wuce ta kalleshi tace “Malam zan wuce.”

Mamaki ta bashi ganin yanda ta nuna kamar basu tab’a sanin juna ba, kauce mata yayi a hanya zata wuce yace “Hamna abun ba ko gaisuwa?”

Kallonshi tayi ta wurga masa harara taja tsaki ta wuce, da kallo ya bita duk sai yaji babu dad’i, tana gama abinda ya kawota ta juya ta tafi, a hanyarta ta komawa ta had’u da Alhaji *Sabi’u*, babban shahararren d’an kasuwa, babban mutum ne mai iyali da tunbi, sanda suka tsaya bakin madakatar danja a lokacin ya sakar mata na mujiya, ba mutumin kirki bane ko kad’an, indai zaiga mace to fa babu lafiya hankalinsa tashi yake, binta yayi a baya har ta isa gida, gira d’aya ya d’aga sama ya cije leb’e sanda yaga gidan data shiga, lallai ko giyar wake yasha bai isa ya tunkari gidan nan da sunan zai wa yar gidan lalata ba, yana da sani sosai akan mutanen gidan, kama daga gwamnansu Gambo, lieutenant na douanes da kuma colonel na soja, kai ba ma zai yiwu ya fara ba wallahi indai yana son kansa da mutumci, amma kuma ya gani yana so saiya kenan?.

*Bari Fan’s badak’ala su fad’a maka yanda zakayi? Ni ma idan kuka min comment saina baku wata page muji me zaiyi*.

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_61_

Maganar aure ya shigo da ita dan ya samu abinda yake so, mutum ne dake iya b’atar da ko nawa ne dan ya samu biyan buk’atarsa, ita bata sanshi ba dan ko ganinshi bata tab’a yi ba, wani shu’umin mutum ne daya san kan tsiya kowace iri, kai tsaye gidan ya fara zuwa ya gabatar da kanshi ga manyanta, saboda kowa yayi karatun tanastu yasa Hajia da kuma lieutenant cewa sun gamsu da kamalarshi, daga yanda suka mata magana ya nuna umarni ne suke bata data aure shi, abinda ta fad’a musu kawai shine “Allah ya zab’a mana mafi alkairi.

A ranar da ya zo dan su fahimci junansu data ganshi saida ta tsorata, zuciyarta ta tashi sosai saboda ba wai muni ne fa shi ba, gashi da tsayi da babban tunbi, sannan bak’i wulik dashi sai idon kwartaye, da k’yar ta iya gaisawa dashi kafin tace zata koma bata jin dad’i, Ammar ne ya shigo farfajiyar b’angaren Hajia zai shiga falon yana d’auke da Ameera a kafad’arshi, saida gabanshi ya fad’i daya ga wanda take tare dashi, me ya had’ata da Sabi’u kuma har gidansu? Yana k’arasawa bai kalleta ba ya bashi hannu yana fad’in “Alhajin Allah kaine a gidan mu?”

Wuk’il wuk’il yayi da ido dan duk jikinshi ya mace ya sare da al’amarin yarinyar, yaji a jikinshi wannan ita ce yarinya ta farko data birgeshi kuma bai samu biyan buk’ata ba, dan shi sai yanzu ne ya tuna ashe wannan pand’ararren ma a gidan nan yake, to shi ina zai iya da jarabar bawan Allahn nan, yo shi ko baya da iyali ai zai k’wauracewa kwatirarsa bare kuma yana da wanda baya san sa su a matsala.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected