BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Hajia ce tsaye a d’akin Alhaji ta tisashi gaba tana fad’in “Akan mene zaka musu gini ba tare dana sani ba? Sai yanzu kawai ana maganar gyaran d’akin sai ka wani ce wai ga gidansu nan, sun fad’a maka suna sha’awar zama anan d’in ne?”
Shiru Alhaji ya mata kamar bai jin me take cewa sai jan carbin hannunsa da yake, d’orawa tayi da “Babu wanda baya da lafiyayyen gida a cikinsu, an musu wannan tanadin ba tun yau ba saboda irin wannan ranar, kuma kai ma kasan da haka, amma ka had’e musu gida d’aya su hud’u, kuma wannan kurkukun gidan me zai musu? Sai kace wasu jarirai ne su da ba zasu iya kula da kansu ba saida taimakonmu, to ni gaskiya wannan gidan bai min ba, inhar kana son su zauna kusa da kai ne to sai dai in zaka raba musu gidan ko da hakan na nufin ka siye duk rabin unguwar nan ne.”
A hankali cike da dattako ya d’ago kai ya kalleta, hak’ik’a shi d’an halak ne, kuma har yanzu yana tuna hallacin mahaifinta gareshi, wanda kusan shine silar arzik’in shi, ya mishi hallaci sosai a rayuwa, dan haka har yanzu yake iya shanye duk wani wulak’anci da k’ask’anci daga wajenta. Murmushi ya sakar mata tare da mayar da kanshi ya sunkuyar, hakan kuma k’ara b’ata mata rai yayi, cikin hassala tace “Wato ga mahaukaciya ko? Shikenan ba komai, yanzu fad’a min ita kuma waccen k’ofar da naga ana yi ta kusa da b’angaren samari ta mecece?”
Ba tare daya kalleta ba yace “K’ofar da zasu dinga shigowa kai tsaye ba sai sun shigo ta waje ba.”
“Amma w…” Kallon daya mata yasa taji ta kasa k’arasawa, ita kanta tasan a cikin zamantakewarsu akwai ragowa da d’aga k’afa, ta kuma san yana k’yaleta ne kawai saboda mahaifinta, amma ba dan haka ba ko a zahiri tasan yafi k’arfin zama lusari a gidanshi, turo mishi d’an k’aramin bakinta tayi mai kama dana Ammar tare da jujjuyashi ta fice da sauri, murmusawa yayi tare da girgiza kai yace “Allah ya shiryaki Zeeya’atu, ina fatan ganin ranar nan.”
Duk da a k’afa aka shigar da amare d’akunansu, amma hakan bai hana abokanan angayen yin kururuwa ba a k’ofar gidan kan ababen hawansu, saida suka tayar da k’ura sukayi juyi da motoci, Maryama ma sun iso lafiya ta shiga d’akin ta. B’angare hud’u ne a cikin gidan wanda daga waje ake mishi kallon k’arami, kowane b’angare matsakaicin doron zabuwa ce aka mishi, a kowane b’angare kuma yana d’auke da falo da d’aki uku a ciki sai k’ananun madafa (cuisine), a kowane d’aki kuma akwai ban d’aki a ciki bayan wasu ban d’akin dake akwai guda biyu a waje, idan ka cire Maryama da ita ma babu laifi an mata kayan d’aki, duka amaren saida aka cika dak’unan da kaya, Gambo da Labaran ne sukayi wannan k’ok’ari bayan doguwar musu da akayi, Labaran yace shi ya d’auka zaiyi musu kayan d’aki, colonel yace shi zaiyi, lieutenant ma haka, a k’arshe dai Gambo da Labaran suka barma, babu ce kawai babu a d’akin su, hatta kayan kallo basu bari ba saida suka zuba musu, kuma kayan duk sanfiri d’aya ne kala da abinda ba’a rasa bane ya banbanta.
*Party*
Kayan da Ammar ya d’inka mata ne ta saka, leshe ne da ak’alla kud’in zasu ishi wani talakan rayuwa na tsawon watanni, kalar ruwan madara ne da bleue wanda ya k’ona sosai, haka shi shi ma tanffatsetsen yadin dake jikinshi kalarsa take, mota dai ba wata tsiya ba kam kamar suyi magana, dan wajen ajiye motoci a babban hall d’in ma kasa d’auka yayi, duk girman gurin saida aka matsu akayita had’a gumi, har ya zama ba’a jin tashin kid’an dake wurin sai jininin mutane da kuma hayaniyarsu. Da gani kasan babban biki ne na manyan mutane kuma masu tarin dangi, kowa daka gani shafar gumi yake saboda matsatsi yayi yawa, abincin kam dama ko da colonel ya samu labarin jama’ar dake wurin ya sake odar abincin a restaurent har guda biyu, da hakane aka samu abinci ya wadata a wurin, duk wanda bai samu ba to baya kusa sanda aka raba. Hasken waya kam ta ko ina ganinshi kake ana d’aukar hoto, ana cikin wannan rak’ashewa aka ce Hamna ta zo a d’auki hoto kuma a dole su sa Ammar tsakiya.
Hamna na tsayawa ta wurga masa harara tana gunguni k’asa k’asa, Ammar dake amsa waya cikin akasi idonshi suka sauka kanta tana harararsa, kashe wayar yayi ya murtuke fuska yace “Ke uban wa kike harara? Allah kankana ki kiyayeni.”
Murgud’a masa baki tayi tace “Ank’i a kiyayeka, da wani abu da zakayi ne?”
Kallonta yayi da mamaki yace “Kutumar uba, ke ni kike fad’awa haka? Me…” Bai k’arasa ba ya juya ya kalli Amna dake ta doka murmushi, murmushin ya mata shima yace “Amaryar, ci gaba da murmushi irin haka kinji, bari na gama da kankana.”
Bai jira amsarta ba ya sake juyowa kan Hamna ya zaro mata ido ya sassauta murya yace “A waccen ranar me kika gani? Ga dukkan alama kankana ban baki tsoro ba, dan dana tsorata ki da ko ganina kikayi sai gabanki ya fad’i, amma akwai lokaci.”
K’wafa yayi ya juya gabanshi ita kuma tace “Tabbas.”
Da sauri ya juyo ya kalleta, d’orawa tayi ba tare data kalleshi ba tace “Tabbas akwai lokacin da zan huce haushina a kan ka, kuma tsoro da kake magana, kai a wa zanji tsoronka? Fasik’in? To ai ko abinda ya faru ma ni baisa na kalleka a matsayin namiji ba, watak’ila baka gama k’wari bane ko kuma dai kana da k’arancin lafiya, amma dai ka sani ni banji komai.”
Ruf ya rintse idonshi, yawu ya had’e masu d’acin gaske wanda suka sanya mak’walaton dake wuyanshi yin sama da k’asa, bud’a idonshi yayi wanda suka fara d’aukar launin ja, ya kasa d’auke idonshi a kanta saboda so yake ya tattartsa mata mari, amma ya rasa yanda akayi ya kasa d’aga hannun, ya tabbatar da wata ce ko Amna tuni data dafe kunci, to amma me yasa ita ya kasa. A hankali ya sake lumshe ido ya bud’e a kanta, tattaro kuzarinshi yayi yace “Da bana da lafiya da bakiyi kururuwa ba, da ban cika namiji ba da tafiyarki bata canza ba, yanzu kuma zan tabbatar da abinda kika fad’a ne idan har kika ga al’adarki a wannan watan.”
Wata mummunan fad’uwa gaban Hamna yayi, kallonshi tayi tsoro ya bayyana a tare da ita, fahimtar haka da yayi yasa ya murmusa ya kalli gabanshi yace “Ba alfahari nake ba, amma inada tabbacin ke bakiyi k’osawar da har madara zata kasa zama d’an mutum a cikinki da zubawar farko ba, musamman ni da nasan na zubata a daidai a lokacin da komai ke bud’e yana maraba da kowane bak’o ya shigo.”
Hamna kam fashewa tayi da kuka ta taka zata bar wurin tana fad’in “Allah ya isa, Allah saiya saka min, mugu azzalumi.”
Dariya yayi wacce ta fito da kyawunshi murya k’asa k’asa yace “Ba farau ke da zafi ba dama, ramau, kuma nima Allah ya isa da kika rabani da samartaka ta, muguwar kankana kawai.”
Amna dai da babu abinda take ji kallonshi kawai tayi, suna had’a ido ya sakar mata murmushi yace “Ina k’aunar ki amaryata.”
Kunya ce ta rufeta ta sunkuyar da kai, shi kuma kallonta yayi ya tambayi kanshi “Da gaske *kana k’aunarta*?”
D’an murgud’a baki yayi yace “Ko bana sonta ai ina k’aunar ta, kuma yanzu matata ce sannan zata zama uwar ‘ya’yana insha Allah.”
Tsam yayi sai alamar tashin hankali daya ziyarceshi lokaci d’aya, abinda ya fad’a mata ne ya dawo kanshi, *yanzu kuma zan tabbatar da abinda kika fad’a ne idan har kika ga al’adarki a wannan watan*! Tashin hankali, to idan fa haka ta faru? Wata zuciyar ce tace mishi “Haka ma ba zai faru ba, ai ka fad’a mata ne kawai dan ita ma taji zafi kamar yanda ta cizgaka.”