BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Nufa tayi kan kujerarta ta zauna k’afa d’aya kan d’aya tace “Ina manta wani abu fa, wasu haka suke zuwa duniya a wahalce kuma su koma babu nasara.”

Ita ma murmushin tayi wanda bai fito da hak’oranta ba ta mik’e tana kallonta tace “Ina kwana Hajia.”

K’ala ba tace mata ba dan haka ta juya zata fita sai kuma ta kalleta tace “Ba wai zama a cikin daula bane ke nuna kayi nasarar zuwanka duniya, ni a gurina nasarar da soyayyata ma tayi ma nasara ce, wasu basa da sa’ar zama da wanda suke so, ni kuma yanzu haka ina cikin farin cikin da na tabbatar sauran matan gidan nan basa cikinshi, idan kuma k’arya na fad’a ki tambayi kowace kiji zata fad’a miki indai har gaskiya zasu fad’i.”

Cikin ladabi ta sake kallonta tace “Kiyi hak’uri abisa abinda ya faru, ganin Amna na zo wacce kullum ke min k’orafin ban zo naga gidanta ba, kuma tace gidan jikin wannan yake shiyasa na lek’o mu gaisa kar nima na watsar daku kamar yanda kukayi, ko ba komai ina da ‘ya’ya a gidan nan.”

Fita kawai tayi ta barta, tana ganin gidan tasan shine dan haka kawai ta shiga, sallama ta dinga rafkawa har Jamila da Amna suka lek’o su da su kafi kusa, dukansu rumgumeta sukayi da farin ciki, Amna har kuka tayi na ganin mahaifiyarta, haka suka shiga ciki ta zuba mata kayan tab’awa inda suka bud’e shafin hira, a k’alla awanta uku kafin ta tashi suka shiga wajen Umaimah da Maryama suka gaisa, data fito zata tafi a lokacin Amna ke cewa “Mama ki jira yah Ammar yanzu zaki ganshi tunda na fad’a mishi kin zo, ba zaiji dad’i ba idan ya samu kin tafiyarki.”

Dariya ta mata tace “To ni dashi kusan kullum ba muna had’uwa ba, kowace juma’a fa sai yaje madarunfa.”

Zaro ido tayi tace “Mama kowace juma’a? Amma shine bai tab’a fad’a min ba.”

Dariya tayi zatayi magana sai gashi ya shigo da makullin mota a hannu, da farin ciki da ladabi suka gaisa kafin yace “Tanti har kin fito ne? Amma ai baki jima ba.”

Da murmushi tace “Haba dai ina laifi ai na jima anan, zan wuce can gida ne wajensu Inna zuwa bayan sallah la’asar kuma saina koma.”

“Amma kun gaisa da mutanen ciki kuwa?” Saida tayi dariya ta kalleshi tace “Mun gaisa, harda kakarka ma.”

Dariya yayi shima yace “Ashe kunsha hira.” Dariya tayi kafin ta kalli Amna tace “Ki koma ciki ni zan tafi, sai kuma na sake dawowa ganinki ko auta.”

Cikin shagwab’a ta kwantar da kanta a kafad’arta tace “Mama yaushe zaki dawo?”

Kallon Ammar tayi da tunanin abinda zata fad’a mata sai kawai yace “Sai kin haihu mana zata dawo.”

Kunya ce tasa Amna k’ara sunkuyar da kanta tana murmushi, Tanti kuma a ranta tace “D’ana kenan, anyi halin ba .”

Ammar ne yace “Muje tanti saina ajeku.” Kallonshi tayi tace “A’a haba daka barshi ma, watak’ila akwai abinda kake wannan shirmammar ta taso ka.”

“Ku zo muje kawai, ai babu abinda yafi mana ku.” Ya fad’a yana nufa hanyar fita, rik’eta Amna tayi sosai wai babu inda zata je, abu da gaske sai kuwa tasa kuka ita sai dai ta tafi da ita, ita ma rumgumeta tayi tana fad’in “Saurare ni auta, kina ji na da kyau?”

Kai ta d’aga alamar eh, cikin fitar da kowace kalma take fad’a mata “Kiyi hak’uri ki koma d’akinki ki zauna, na miki alk’awarin zan sake dawowa ba da jimawa ba, wannan kukan yasa dama tun farko ban zo ba, amma idan kikayi shiru yanzu to zan sake dawowa kuma na taho miki da abinda kika fi so, zuwa lokacin nasan Hamna ta dawo kinga ita ma na ganta.”

Turo baki tayi tana d’aga kafad’a da fad’in “Um um, um im, ban yarda ba ni gaskiya, kuma Hamna ma wa yasan ranar dawowarta.”

“Au ba zaki hak’ura ba kenan?” Cikin turo baki tace “Na k’iya.”

“Shikenan to nasan maganinki.” Ta fad’a tana kallon inda Ammar ke tsaye, cikin d’aure fuska tace “Yarona zo ka min maganinta tunda bata jin rarrashi.”

Takowa ya fara yi da k’arfi yana fad’in “Ai kuwa tanti bari kiga yanda zanyi da ‘yar banza.” Takalmanshi ya ciro yana shirin wurga mata da gudu ta koma d’aki tana rusa kuka, dariya suka saka mata inda tanti tace “Ai maganinki kenan, da kin kwantar da hankalinki da munyi sallama cikin farin ciki.”

Suna nufa k’ofa Ammar yace “Tanti karki damu, insha Allahu zan kawo miki ita tayi sati d’aya, dan yanzu ta fara kumburo min baki kenan har illa masha allahu indai ba ganinki ta sake yi ba.”

Dariya tayi tace “Auta ce ku barta tayi rigimarta, amma zaka iya barinta tayi sati d’aya ko?”

Kallonta yayi sai yaga ita ma kallonshi take kallo mai nuna na fa sanka ba zaka iya ba, sunkuyar da kai kawai yayi yana murmushin jin dad’in yanda ta san shi sosai tare da fatan ina ma mahaifiyarshi ce ta mishi wannan fahimtar, fita sukayi inda ya kaita gidansu dan ta gaisa da yan uwanta.

Kamar yanda ya fad’a kam ya cika alk’awari, ba tare daya fad’a mata ba kawai yace ta shirya, sai kawai ganin tayi sun d’auki hanyar garin, tunda ta ga haka ta fara murna tana jin dad’i sosai, da suka je saida ya wuni kafin ya juyo ya barota, murna a gurin Amna ba magana yau zata kwana tare da ummanta, ba ita kad’ai ba ita kanta tanti tayi farin ciki sosai, da dare da sukayi waya da Hamna ta fad’a mata gata nan ita kanta sai taji kamar tayi hira, anan take tambayarta me yasa yanzu ta b’oye lambarta in aka kirata sai dai ya nuna numéro unkwnon sannan me yasa bata Whastup? Haka kawai shine abinda ta fad’a mata, a wajensu Hamna ma da Ummy komai yana tafiyar musu daidai, sai dai basa cikin kwanciyar hankali, kullum Hamna tana fad’a ma Ummy idan fa asiri ya tonu tana jin tsoron abinda zai faru, ita ma kuma ta sani akwai gagarumar matsala, amma a ganinta lokaci ya k’ure musu.

Tanti Hadiza ta ga abinda yafi k’arfinta, bata san yaushe kuma a wane lokaci Amna ta zama marar kunya ba, dan tunda ta zo idan yau bai zo ba gobe zai zo, a gabanta saita rumgume shi ko ta sumbace shi, idan suka shiga d’akinta duk da babu abinda ke shiga tsakaninsu, amma irin yanda yake jin dariyarsu da maganganu k’asa k’asa abin nasa kanta girma, idan kuma dare yayi suna waya wani abun idan ta fad’a saita kalleta da mamaki, shiyasa yanzu daya shigo gidan ita kuma saita shiga mak’ota ko kuma ta shige d’akin mijinta ita ma, a haka ta kammala sati d’ayan nan suka koma gida.

Lieutenant ya fara mata k’orafi kan rashin dawowarta kan lokacin data fad’a mishi, amma sai take fad’a mishi basu gama bane ya k’ara hak’uri, har saida Hajia ta fara fad’a wanda Ummy tace kamar wak’a take jin fad’an nata, tunda dai har ta riga data tafi to anyi mai wuyar, a haka har lokaci ya k’ara kwararawa.

*Bayan Wata Biyar*

*France*: tunda ta shiga watan ta dama aka basu lokacin da za’a kawota kafin ta fara nak’uda, dan haka k’arfe *11: 54* suka shiga da ita d’akin haihuwa, Ummy bata san tana kuka ba saida wata banasariya ta dafa ta tace mata ta dinga mata addu’a zata haihu lafiya, tunaninta a lokacin shine idan fa aka samu matsala ya zatayi? Alwala ta d’auro ta shiga fad’awa Allah kukanta, bata matsa daga kan sallayar ba misalin *12:38* aka sanar da ita haihuwar Hamna lafiya, yaron bai dameta ba sai mahaifiyar da take tambayar ya take? Lafiya lau ita ma aka fad’a mata, saida tayi sujadar godiya ga ubangiji kafin ta shiga ganinta, murmushin daya sub’uce mata ne yasa Hamna dake kwance kallonta tace “Ummy lafiya?”

Dake tsaye inda take kusan gadon jaririn ta sake dariya taja hancin yaron tace “Ya rantse saiya zo duniya, gashi dai ya zo yanzu kuma *BADAK’ALAR* zata fara musamman mahaukacin ubansa yasan dashi.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected