BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
_52_
“Yan uku kankana?”
Yawu ta had’e duk tayi alamar rashin gaskiya, ganin bai daina kallonta ba yasa ta juya zata koma d’akinta taji yace “Har d’akin zan sameki wallahi idan baki sauko ba.”
Juyowa tayi ta kalleshi, yamutsa fuska tayi ita kam ba zata iya wannan tozarcin ba, hararanshi tayi tace “Hijabi zan d’auko to, saboda gidan nan ba tsaro gareshi ba, ta ko ina kuraye ke akwai ko ganye suka gani kallon nama suke mishi.”
Da kallo kawai ya bita har ta fito, kallon saukowarta yake da dogon wando sai hijab daya rufe iya cinyarta, saita ta kawo daf da shi suka jera zasu fita yace “Duk kurar da take ma ganye kallon nama lallai lafiyayya ce, shiyasa fa har yanzu nake mamakin yanda akayi baki karb’i sak’on dana tura miki ba bayan kuma ina da tabbaci akan d’an aike na.”
Hararanshi tayi ta murgud’a baki tace “Ta Allah ba taka ba, burinka kenan a kaina kuma ba zai cika ba.”
Suna zuwa Ummy ta fito ta kalleshi tace “Malam muje dan Allah ka kaimu asibiti idan ka gama shiriritar.”
Turo baki yayi gaba ya kalli mutanen dake wurin yace “Yanzu jama’a ba zan iya samun wanda zai kira ni ya danganta yaran nan dani ba?”
Alhaji ne yace “To uban…” Kallon yaran yayi yace “Da fari fad’a mana sunansu? Ko kuma ka bamu zab’i ne?” Da k’arfi tace “A’a Alhaji, haba dai kura da shan bugu gardi da kwashe kud’i, ai yanda nake ubansu haka zan saka musu suna.”
Hamna ce ta kalli Ummy tace “Ummy ina Amna?”
Nuna mata d’akin tayi tace “Tana ciki.” D’akin ta shiga dan ganin yar uwarta, shi kum saida ya gyara tsayuwa sannan yace “Namijin sunan *Ammar*, macen kuma domin nuna farin cikina ga uwarsu na mata takwara, dan haka ita ta ci *Amna*.”
Kallon kallo aka shiga yi harda yaran, lieutenant ne yace “Meye na mayar musu da sunanku to kamar suna ya k’are?”
Murmushi yayi yace “Abba ai duka sunaye ne masu kyau, ina so jarumi na ya zama namiji marar tsoro da fargaba, ya zama babu shakka babu d’aga k’afa kuma zai iya fad’a ko a gaban waye, sannan ya zama wanda baya d’aukar raini, jarumata kuma zan so ta zamar ruwa masu aiki sannu kamar mahaifiyarta, hakan zaisa kowa ya so ta.”
Lieutenant ne yace “Idan na fahimce ka kana so ka saka mishi sunanka saboda kana so yayi komai naka ko?”
“Eh Abba.” Ya fad’a cike da kuri, jinjina kai yayi yace “Har da fitsarar da rashin ta idon ma?”
Kwab’e fuska yayi alamar shagwab’a yace “Abba ni ne marar kunyar?”
Murmushi lieutenant ya masa yace “A’a d’an albarka.”
Husseina ce tace “To wai akan me sai sunayenku za’a mayar ma da yaren kamar wad’anda suka mutu?”
Alhaji ne yace “Dan Allah ku barshi tunda haka yake so ai ya hallata, kawai mu dai ya fad’a mana wani sunan ko da alkunya ce da zamu dinga kiransu dashi, d’an ba zamu kiraku da sunanku ba kuma suma mu kirasu da sunanku.”
Girgiza kai Hajia tayi ta kalleshi tace ” *Shalele* na, fad’a mana alkunyarsu ko kuma na saka musu da kaina.”
Kallon kallo aka shiga yi Hajia ta kirashi shalelenta, basarwa kawai tayi shi kuma saida yayi tsayuwar tata rashin mutumci yace “Eh to shi jarumin Ammar d’in zaku iya mishi lak’abi da *Abu Ahmad*, sunan da zai sawa d’anshi kenan insha Allah, jatumar tawa kuma saiku mata lak’abi da *Ummu Aysha*, idan kuma alkunyarsu kuke so saiku kirasu da *Ameer* *Ameera*, idan kuma a sauk’ak’e kuke so saiku ce *A.A*, ita ma kuma saiku ce mata *A.A*.”
.Cike da k’aguwa Ummy tace “Ba zan iya sauraren wannan shirmen ba, yarinyar can asibiti take buk’ata a bata kulawar data dace, amma kun tsaya kuna maganar sunan yara tun yanzu.”
Juyawa tayi cikin jin haushi ta shiga ciki, Hamna ta samu rik’e da hannun Amna cikin sanyin murya take fad’in “Yer uwa wallahi ban tab’a tsammanin haka haihuwa take ba, ta zo min da sauk’i fiye da tunaninki, sannan yah Ammar ya tsaya kaina har na haihu, gaskiya naji dad’in kulawarsa a kaina.”
Murmushi Hamna ta mata tace “Yanzu ma gashi can sai hauka yake mana a gida wai shi yayi yara, ya hana kowa bacci fa.”
Murmushi tayi tace “Ba hauka bane yer uwa, farin ciki yake ya d’ora idonshi akan ‘ya’yansa.”
Kamata Ummy tayi tana fad’in “A ganinki haka murna ce? Wannan ai hauka ne da shirme, kanshi aka fara haihuwa?”
“Ummy a gareshi shine na farko.” Cewar Amna, da sauri Ummy ta kalli Hamna ita ma kuma ita ta kalla, kamata sukayi ta tashi Ummy ta mata durwa (k’unzugu) sannan suka fito, sun same su tsaye sai zuba musu haukan ko yake ta bakinsu, sunaye kawai yake zana musu idan basu iya fad’in wannan su fad’i waccen, rankaya sukayi zasu fita ya kalli Hamna ya cilla mata makulin mota yace ” Ke b’ukekiya tuk’asu ina zuwa.”
Hajia ce tace “Ina zaka je kuma?” Kallonta yayi yace “Ku dai ku tafi gani nan.”
Hamna da bak’in ciki ke neman kasheta tsabar haushi kawai taji hawaye sun taho mata, lieutenant ne yayi sauri matsowa kusanta yace “Ke lafiya? Meya miki?”
Saida ta nuna Ammar tace “Abba na fad’a mishi bana so yana shammatar min jiki amma ya k’i dainawa, haka kawai kamar maye ya sa min ido.”
Kallonta yayi da mamaki yace “Ke ni banda lokacinki, girma ya zo min yanzu na wuce ajinki wallahi.”
Yana fad’a ya wuce b’angarensu, k’ofar Amar yaje kamar Allah ne ya aikoshi ya shiga jijjiga mishi k’ofa, cikin kasala ya taso ko baccin ma baiyi ba su gama tijara shi da Umaimah kan shinfid’ar gado da bata gyara masa ba, yana bud’ewa Ammar yace “Shege, wato ina can ina bud’ar baki dan murna ku kuna can kuna nanik’e tsakani k’ugu da k’irjin matanku, to fito kaje ka d’ora mana shayi a k’ofar gida zanje na tado sauran matsiyatan.”
Da mamaki Amar yace “Ammar Amna ta haihu ne?”
Cike da isa yace “Biyu, biyu yaro ta haifa min, a halin da ake ciki yanzu zan iya bada ‘ya kuma nima za’a iya bani ‘ya.”
Wani mamakin ne ya sake lullub’e shi yace “Ban gane ba, kar dai yan biyu ta haifa maka mace da namiji?”
Sororo ya kalleshi yace “Ban gane kar dai ba? Bai kamata bane ko me kake nufi?”
Cike da damuwa yace “Kai sarkin masifa, ni ba haka nake nufi ba.”
Hanyar b’angaren Junaid ya nufa yana fad’in “To maza kaje ka d’ora mana shayi.”
Niyyar komawa ciki yayi yana fad’in “Ba uban da zan d’ora ma shayi yanzu ehe.”
Shi dai baisan ya akayi ba saiji kawai yayi har ya shak’o wuyan rigarshi yana fad’in “Sai ni Ammar, ni zaka d’ora ma inba haka ba ubanka zaka ci Allah a cikin daren nan.”
Cikin son k’wak’ule hannunshi yace “Naji to zan d’ora sake ni.”
Sakinshi yayi da sauri ya shige ciki yana fad’in “Sai naga tsiya yanzu in zaka biyo ni ciki ne.”
Saida ya rik’e k’ugu yace “Kai dai kafi kowa sanin waye d’an uwanka, kaine zaka bayar da labari na ba wai wani ya baka ba, k’arami ne a cikin k’ananun aikina na shiga ciki, to miye a ciki? Daga kai har Umaimah a gabana kuka girma, dukanku k’annai na ne to sai me.”
Juyowa Amar yayi ya mayar da k’ofar ya rufe ya tunkari inda yake jin k’arar motoci yana fad’in “Naji dan Allah zan d’ora, je taso sauran.”
A wurin Junaid ma haka abun yake bayan ya gama kiranshi gwauro sannan ya iza k’eyarshi gaba, Jibril ma haka taso shi gaba yayi har da Jamil ma bai bari a baya ba, yana dawowa k’ofar gida ya same su mai gadi na kunna musu wuta a mangal, Jibril ne yayi wata doguwar hamma yana fad’in “Allah gamu gareka, wannan lamari sai kace a mulkin mallaka.”