BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Saida sukayi nisa da gida kuma basu kai ko rabin gidansu Amie ba mota ta tsaya cak, ko da Hamna ta duba wajen dake bayyana idan mai ne babu taga tanki cike yake, nan ta shiga tayar wa amma mota shiru, tsayawa tayi tana girgiza kai tana murmushi a hankali take fad’in “Amna, Amna, amma zan ci uwarki, ni zaki wa iskanci.”
K’wafa tayi ta kalli Amie tace “K’awata, hak’uri zakiyi ki samu adaidaita ki hau, in dai ina tare dake to babu inda zan gusa.”
Da mamaki ta kalleta tace “Me yasa? Wani abun ne ya faru?”
Murmushi ta mata tace “Ba zaki gane ba, kawai ki samu adaidaita.”
Bud’e motar tayi ta fita ta kalleta tace “To ke ya zakiyi?”
Saida ta kalli titi tace “Karki damu, idan ma bata tashi ba zan kira a zo a d’auke ni.”
“Ok, ki kula da kanki.”
Jinjina kai tayi tace “Ok, saida safe.”
Nan ta samu adaidaita ta tafi, tun a hanya data shiga WhatsApp d’inta ta kasa hak’uri ta tab’o sauran k’awayenta su biyu, gulma ajali inji yan magana, haka suka jima suna tattaunawa suna fad’in ashe ta ma fisu iskanci, shine in taga suna rayuwarsu saita dinga nuna tana k’yamar abun, ashe ita har shege ma gare ta kuma da mijin yar uwarta.
Saida ta ga tafiyar Amie ta kira Amna a waya, har ta kusa tsinkewa sannan ta d’auka tace “Lafiya? Har kin kaita d’in?”
Dariya Hamna tayi dan su rabu lafiya kar ta jawa motarta kwana akan titi, cikin muryar rarrashi tace “Dan Allah yar k’anwata taimaka min ina so na koma gida kinji, dare kayi kar Abba ya min fad’a.”
Cikin kumburo baki Amna tace “Na k’i d’in, bani kika rainawa hankali ba?”
Sake mak’ale murya tayi tace “Dan Allah fa nace.”
“To shinenan, ki bani hak’uri yanzu.” Cewar Amna.
Saida ta gyara murya tace “To aunty Amna kiyi hak’uri.”
Murmushi Amna tayi tace “Shikenan to kiyi sauri ki dawo gida kar wani ya sace min ke.”
Dariya tayi tana wa motar key tace “An gama zuciyata.”
Ko da ta kunna ta kama tana murmushi tayi baya baya ta d’auki hanyar komawa gida.
*Da safe* Hamna na ta kai da kawon gyara falon an gama ma bébé wanka, duk inda tayi sai Amna tabi ta da kallo, tun bata lura ba har ta ankare, tun abun bai tsaya mata akai ba har ta fara tsarguwa da kallon, tsayawa tayi tana kallonta tace”Wai ke lafiya?”
Sai kawai ta bushe da dariya kamar mahaukaciya, kallon mamaki Hamna ta bita dashi ta girgiza kai ta ci gaba da aikinta, Ummy na shigowa cikin shirin tafiya aiki da Shureim a hannunta, hannu ta tarawa Shureim tace “Zo nan.”
Takawa yayi ya je wurinta ya tsaya, rik’e hannunshi tayi tana mishi wani kallo kamar yau ta fara ganinshi, sai kawai ta matso dashi kusanta ta sumbaci goshinshi, saida ta d’auke bakinta ta sake kallon fuskarshi sai tace “Kai ni fa sai naji na fi sonka da aka ce yar uwata ma ta haifeka.”
Wani yamutsawar hanji Ummy da Hamna suka ji a lokaci d’aya, Husseina dake karin kumallo kallonta tayi irin kallon anya kuwa Amna, da sauri suka kalli juna suna zazzaro ido na alamar tambayar me ke faruwa, kallonsu Amna tayi a tare saida ta gama kallonsu sai tayi dariya ta nuna Hamna da hannu tace “Sakarya, ji yanda kika zaro ido kamar mahaukaciya, ko ke ma kin haukace irin na k’awarki?”
Da sauri suka saisaita nutsuwarsu, sai Ummy data kalli Husseina tace “Anya Hajia kuwa lafiyarta k’alau?”
Cikin murya k’asa k’asa tace “Ni ma dai abinda nake tunani kenan.”
Amna kam kallon Shureim ta sake yi tace “Baka tafi islamiyya ba kai?”
A hankali yace “Yanzu Ummy zata kaini.”
Murmushi ta masa tace “Yawwa, kana ji ko? Ka dinga karatu sosai saboda ka zama babban malami, kana so ka zama kamar wannan kai ma?”
Ta fad’a tana d’aukar wayarta, wa’azin *ustaz Rayyadun* (Allah k’ara girma malaminmu) ta nuna masa na vidéo tace “Ka gani ko? Ka zama kamar wannan kaima, kana so?”
Kai kawai ya d’aga mata irin shi dai yana saurarenta, su dai kallonta suke har Ummy ta mik’e ta kama shi suka fita, hankalin Hamna ya kasa kwanciya duk a takure take jin kanta, ta k’i yarda su had’a ido da Amna wacce ita kuma take ta binta da kallo har yanzu, idan ta ga Hamna ta k’i kallonta sai ta bushe da dariya, duk wanda ya zo gidan haka zai iskota a wannan yanayin, gashi kuma Hamna babu damar da zata barta dan wani abun sai tace dole Hamna ce kawai zata mata, haka suka dinga wannan zama babu dad’i babu hira tsakaninsu, sai dai ita Amnar tayi ta nata maganganun masu kama dana mai shirin barin duniya.
*Kwana uku* yau da faruwar wannan lamari, shirin biki ake ta yi sai dai ba wani da karsashi ake yinshi saboda yanayin jikin mai jego, kullum cikin taka tsantsan ake kan d’inkinta, ana yawan kwakwafarta kan rage magana da dariya mai k’arfi, amma abun sai a hankali in tayi wani abun kamar dai k’walwarta ce ta fara samun matsala. Yanzu ma Ammar ne ya shigo da babbar leda a hannu, ko da ya gaishe da mutanen d’akin ya nufi nashi d’akin, kamar daga sama aka tsinci muryar Amna tace “Ammar.”
Cak ya dakata ya juyo ya kalleta, *Ammar*? Tunda yake da ita daga k’uruciya har girmanta bai tab’a ji ta kama sunansa ba haka, dama dai waccen marar kunyar ce, su kansu mutane mamaki ne ya kama su jin yanda ta kira sunan nashi kamar sunan Ammar k’arami, shi kanshi Ammar k’arami saida ya juyo ya kalleta, har ya cire hannunshi daga abincin da yake ci zai taho tace “Ba kai ba zauna.”
K’ok’arin mik’ewa ta shiga yi hakan yasa Ummy taimaka mata ta tashi, saida taje kusanshi ta kalle shi tace “Muje ciki.”
Kallon Ummy yayi daga nesa, ita ma shi take kallo kallon nima bansan komai ba, wucewa yayi d’akin ta bishi a baya, sua shiga ta zauna kan gadonshi tana kallonshi tace “Kana ji ko? dan Allah ka kula min da yarana, ka dinga kaisu makaranta kan lokaci, kaji ko?”
Shi mamakin yanda take masa magana kamar wacce ta haife shi ne ma yake, ganin bai ce komai ba yasa ta amso ledar hannunshi tana fad’in “Kawo to, watak’ila kallon nan da kake min dan ban karb’a bane.”
Aje ledar tayi kan gado ta mik’e zata fita sai kuma ta juyo ta kalleshi tace “Kasan wannan k’awar ta mu Amie?”
Kai kawai ya jinjina mata yana ci gaba da kafeta da ido, dariya tayi sosai tace “Baka san ta hauka ce ba? Kasan haukan data zo min dashi gidan nan?”
Kai ya girgiza mata kawai dan jin maganarta yake kawai a sama, wata dariyar ta sake yi tace “Wai a haukanta cewa tayi kai da Ummy da yer uwata kuna cin amanata, kasan me ta fad’a min?”
Ajiyar zuciya ya sauke ba tare daya daina kallonta, jinjina kai tayi ta matso kusanshi cikin rad’a tace “Wai cewa tayi Shureim d’an ka ne, kaji fa mahaukaciyar, ta manta Ummy ce ta haife shi, to kuma ni ko wa ma ya haife shi ina son shi, inda yer uwar ta wa ta haife shi wallahi da naji dad’i.”
Kallon fuskarshi tayi da kyau sai tayi dariya tace “Kai ma ka girgiza ko? Karka damu ci gaba da abinda kake.”
Ko da ta fad’a ta juya a hankali ta bar d’akin, shi fa tunda ta fad’i haka gabanshi ya yanke ya fad’i, kawai bata aje hankalinta bane data fahimci tashin hankalin daya shiga jin wannan magana, ita dai ta d’auki abun wasa da k’arya da kuma hauka, amma shi baya da dalilin da zai k’aryata Amie, hasalima zai iya cewa ya yarda da abinda ta fad’a d’in, yana da gamsassun dalilai da hujojji.
Yanda ya zazzare ido haka ya zauna bakin gado, tunani ya durmiya yana tuna faruwar komai sala sala, tabbas bayan faruwar al’amarin ne cikin Ummy ya bayyana, lokacin daya ga canji a jikin Hamna har ya so fallasawa Ummy ta jijjiga sosai har ta mare shi, sannan ta matsa sosai har saida aka mata hanyar data shiga sahun masu tafiya France kuma ta k’ara kan lokacin daya kamata ta dawo, kuma ai Hamna bata nan a lokacin, to kenan taya haka ya faru? Girgiza kai ya shiga yi yana ta tunanin abubuwa da dama, ji da yayi kamar kanshi zaiyi bindiga yasa shi mik’ewa da sauri ya fito.