BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Babu alamar wasa a tare dashi yace “Me yake faruwa? waye zai rufe shi akan kud’i? Me kuma ya had’a Ammar da Jumare?”
Baki ta saki tana kallonshi da mamaki da kuma rashin jin dad’i, kenan ya ji komai? Oh Allah, cikin taushin murya tace “Ba komai.”
Kafeta yayi da ido yace “Ya zaki ce ba komai, duk da ban ji komai ba amma ai na fahimci inda zancen ya dosa, fad’a min meke faruwa?”
Cike da rangaji tace “Idan mun koma gida zan fad’a maka, amma Abban Ammar ban so kayi hushi.”
“Shikenan, yanzu ya mai jikin?” Dariya ce ta kubce mata ta rufe baki, dan ya bata dariya sosai data tambaya, hakan na nufin baiji abinda aka fad’a anan ba kam, klonta yayi yace “Meye?”
Girgiza kai kawai tayi ba tace komai ba tace “Shigo muje.” Girgiza kai yayi da sauri yace “A’a, idan dai zasu iya ki fad’a musu ina waje, in kuma kwance suke kawai ki gaishe min su sai ki fito mu koma.”
Kamar zata fashe da kuka tace “Lahh, na d’auka fa nan zaka barni da naga mun taho da wuri.”
Hararanta yayi yace “Lafiya kike? A halin da kike ciki kulawa kike buk’ata, sannan hidimar da akayi duk kin gama wahalar min da kanki da baby na, dan haka ba zan barki ba, ki shiga ki fito mu koma daga baya kya dawo ganinsu.”
Juyawa tayi ta nufi ciki har da buga k’afafu take tana kukan shagwab’a, da murmushin birgewa ya bita cike da k’aunar yarinyar. Tare suka fito da kawu Mamu suka gaisa sosai, da zai tafi ma wasu kud’in ya sake bashi, babu kunya babu kawaici ya karb’a yana godiya kafin ya koma ciki suma suka tafi.
Tun a hanya ya sake tambayarta abinda ke faruwa, tsaf ta fad’a mishi amma banda marin da Ammar ya wa Jumare, dan haka yace “To ita kuma Jumare da waccen ya mareta fa?”
Cikin turo baki tace “Jumare fa rashin kunya ta min shine ya hukunta ta.”
Kallonta yayi yace “Ban gane ba? To shi shi ta wa da zai mareta? Ke fa naga alama kin d’aukeshi wani mutumin arzik’i.”
Wani kallo ta mishi mai kama da na tsani kalmar daka fad’a, sake kallonta yayi sai yaga ta k’ura mishi ido tana kallo, d’aga mata gira yayi yace “Lafiya?”
Had’e rai tayi sosai alamar bata ji dad’i ba tare da kawar da kanta gefe, cikin d’an d’aga murya yace “Wai meye? Wani abu na fad’a daya b’ata miki rai ne?”
Juyowa tayi cikin tsananin masifa har ta manta dawa za tayi magana sai ta fara fulatanci tana fad’in “Gaskiya ni na baku kyautawa, d’an da kuka haifa a ciki kuna fad’a mishi duk abinda ya zo bakinku, yanzu meye na wani cewa wai ina ganinshi kamar mutumin arzik’i, to mutumin banza ne dama? Akan me zaka fad’i haka a kanshi?”
Tunda ta fara magana ya saki baki yana kallon nata bakin, yanda ko wane harafi ke fita na bakinta abun birgewa, masifa take amma kuma ta mata kyau, sai dai abun takaicin baiji komai data fad’a ba, bakinta kawai ya gani yana motsawa da sautin harrufan da take furtawa, kallon gabanshi yayi yace “Idan kin gama fad’an saiki fad’a min me kika ce ko.”
Sak’e tayi ta kalleshi, wai dama ba da hausa tayi magana ba? Kawar da kanta kawai tayi ita ma har suka isa gida, katari kam suna shiga sun aje motarsu Ammar shi kuma zai shiga tashi motar, da mutuntawa ta kalli Zeituna yace “Uwa barka, daga pakarey ake?”
Murmushi tayi duk da bata san me yake nufi da pakarey d’in ba, kallon lieutenant yayi yace “Alhaji ya ake ciki?”
Banza yayi da shi zai wuce Zeituna ta d’an rik’o rigarshi, tsayawa yayi ya juyo ya kalleta da alamar tambayar lafiya, saida tayi kamar zata fad’a jikinshi ta kashe murya sosai tace “Magana fa yake maka, dan Allah ka amsa mishi, laifin me yayi maka?”
Cikin fad’a yace “Ke baki ji me yayi bane? Ina ubanshi zai wani ce min ya ake ciki, dallah rabu dani.”
Fizge rigarshi yayi ya juya zai wuce, kukan shagwab’a ta saka tana fad’in “Shikenan nagode da abinda ka min.”
Juyowa yayi yana ganinta ya dawo yana fad’in “Wai ke meye haka? Dan Allah wuce muje.”
Juyawa tayi ta kalli Ammar daya ke daf da shiga mota sannan ta kalle shi tace “Babu inda zanje yau sai na gani da ido na kuma naji da kunnuwa na ka lokacin da zaka sa mishi albarka, inba haka ba kuma yanzun nan na koma inda muka je yanzun.”
Yanda tayi maganar ya nuna rigima take ji, sai dai shi a wurin shi ba wani abu bane da ita take kambama shi har haka, turo baki yayi kamar yaro yace “Kira shi to.”
Take murmushi ya maye gurbin fuskar shanun nan, sam farin ciki yasa ta manta sai ta k’walla kiran sunan Ammar daya shiga mota har ya tayar, bai ji kiran farko ba saida ta kura shi sau uku sannan ya fito daga motar, cike da takon k’asaita ya zo gabansu ya tsaya yana kallonsu.
Kallonshi lieutenant yayi babu annuri yace “…
*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`
✪{T . N}✪️
https://www.facebook.com/101305508365889/posts/101311008365339/?substory_index=0&app=fbl
_Bismillahir rahamanir rahim_
_40_
“Ina zaka je yanzu da dare? Baka san yanzu ka girma bane?”
Wata yar banzar dariya ya bushe da ita kamar da bakin k’warya, galala Zeituna ke kallonshi inda lieutenant ya nuna mata da yatsa yace ” Kin gani? Ina fatan yanzu kin fahimci wani abu.”
Babu alamar wasa a fuskarta ta kalleshi tace “Tambayar daka mishi ai tana nuna damuwarka ne a kanshi, shi kuma abun ya zo mishi a bazata ne, na tabbata abinda ya bashi dariya kenan, idan kuma baka yarda ba ka tambaye shi kaji.”
Kallon Ammar yayi da har yanzu ke dariya har da rik’e ciki yace “Dallah ka mana shiru malam.”
Shirun yayi yana kallonshi, saida ya saisaita nutsuwarsa sannan yace “Zan fita ne Alhaji, asibiti zanje, akwai marasa lafiyan da zan gani nan da minti ashirin.”
D’an jinjina kai lieutenant yayi alamar gamsuwa tare da cewa “Saika dawo, amma karka cika dare ka bar min ‘yata ita kad’ai, kasan har yanzu bak’i ne su.”
Juyawa yayi bai ce komai zai tafi sai kuma lieutenant yace
“Dama ina son ganinka.” Dawowa yayi yana fad’in “Gani.”
Saida ya saci kallon Zeituna kafin yace “Yarinyar da ta zo d’azu gidan nan me yasa ka mareta? Baka san yer uwarta ce ba?”
Kallon daya ma Zeituna yasa lieutenant cewa “To ba ita ta fad’a min ba, yanzu daga gidan muke kuma ran iyayenta ya b’ace, har naji mahaifinta na cewa ma zai zo har gidan nan ya rama mata.”
Wani murmushin yau ga banza ta samu ya ma lieutenant, mayar da kallonshi yayi ga Zeituna yace “Uwa ni kam ina ne gidanku ma?”
“Babu nisa da nan ai, kana shiga kwanar…” A firgice lieutenant ya kalleta saboda jin zata kwafsa, shi fa ya fita sanin waye d’anshi, shi ya haifi abinshi, dakatar da ita yayi da cewa “Ke kuma miye haka? Daga ya tambayeki saiki fad’a masa.”
Kallon ashe ka harbo jirgin ya masa tare da sakin murmushi yace “Abba hak’uri zanje na basu, kace yace zai zo har nan, ku surukai ne bai kamata a samu matsala a tsakaninsu a dalilina ba.”