BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tashin hankali ne k’arara ya bayyana a fuskarshi, shi kad’ai yasan irin k’aunar da yake yiwa mulkin garin basraba, dole sai ‘yarshi ta shigo gidan zai cika burinshi, dan haka a shirye yake da yayi komai akan duk wani mai son shiga tsakaninshi da mulkin nan, d’an b’alle botir d’in rigashi yayi da yake jin ya shak’eshi sosai kafin yace “To idan har aurensu ya tabbata ya zamuyi?”

A harzuk’e tace “Ba mai zai tabbata ba, kawai kayi wani abu a kai.”

Wani kallo ya mata mai fassara da dama yace “Kamar me kenan uwar d’aki?”

A tsanake ta kalleshi tace “A matsayinka na namiji baka san me zakayi ba da zai hana auren nan? Sai ni ce kake so na samo maka mafita? Bayan kuma ‘yarka ce zata shigo gidan, nifa babu wata riba da zan ci, kawai waccen tsinanniyar matar ta shi ce bana son ganinta ita kad’ai a cikin gidan nan.”

Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleta yace “Zanyi duk abinda ya dace a matsayina na namiji, amma ki ban izinin yin komai.”

Ba tare da tunanin komai ba tace “Kawai ka je kayi koma meye banda matsala da hakan, auren ne kawai bana so ya tabbata.”

Murmushin gefen labb’a yayi yace “An gama ranki shi dad’e, za ayi komai kamar yanda kika ce.”

Ganin ta jingina a bayan kujerar yasan ta gama magana kenan, cikin girmamawa yace “Ni zan tafi uwar d’aki, sai kin jini.”

K’ala ba tace mishi ba har saida ya kai k’ofa tana kallonshi, cikin dubara yayi kamar labulen d’akin ne ya sark’afe shi harya samu ya d’auki wayar ya fice, yana fita ya shigar da d’aukar da yayi ya fara tsare tsaren abinyi.

*Da rana*

A falonsu Ammie suke zaune bayan sunyi sallah sun ci abinci, suna tsaka da hira téléphone d’in dake kan wani k’aramin teburi dake tsakiyar kujeru yayi k’ara, Rauda ce ta d’auka ta kara a kunne, jim ta d’an yi kafin ta kalli Sameera tace “Ammie kina da bak’o a waje.”

Juyowa tayi ta kalleta tace “Who is that?”

D’auke wayar tayi a kunnenta tace “Saleem, k’anin uncle Abbakar.”

Da murmushi a fuskarta tace “Ok, ki ce ya barshi ya shigo.”

A wayar ta sanarwa da mai gadi ya barshi ya shigo, baifi minti biyar ba sai ga Saleem ya shigo da fara’a a fuskarshi, Sameera da murna tace “Saleem, dama kana gari? Kwana biyu ka b’uya.”

Saida ya k’araso ya zauna kujerar da Jabir ya tashi ya bashi kusa da Abdul yana murmushi yace “Aunty ina nan wallahi, abubuwa ne sai a hankali.”

Murmushi tayi tace “Good, ina Abbakar da jiki kuma?”

Saida yanayin fuskarshi ya canja kafin yace “Jikinshi da sauk’i.”

Hannu ya bawa Abdul suka gaisa da Jabir, har Khalifa da Usman ma, Diya’u ne ya taso yana turo baki yace “Ni baka gaisa dani ba, dan ban girma ba ne?”

Dariya Saleem yayi ya bashi hannun yana fad’in “Sorry my Man, ai kai ma babba.”

Khalifa ne yace “Kaji yaron da ko gemu bai fara ba zai ce ba’a gaisa da shi ba.”

Ammie ce ta rik’e baki tace “Ikon Allah Khalifa, to kuma ita gaisuwar dole sai mutum yayi gemu?”

Imranatu ce tace “To Ammie ki fara tambayarshi ma shi ina nashi yake?”

Cike da kuri Khalifa yace “Ai naga man da Dadyna yake anfani da shi gemunshi na k’ara yawa, da nace zan shafa yace na bari zai soyo min wanda suka fi na shi zama original.”

Juyawa Sameera tayi saida ta kalli duk ‘ yan matan d’akin tace “Yanzu dukaninku babu mai wayon da zata kawowa bak’o ruwa? Yaushe kuka zama marowata haka?”

Raihan ce tayi saurin mik’ewa saboda shakkar uwar da take tana fad’in “Sorry Ammie.”

Da harara ta bita harta shiga kitchen d’in su Ammie ta d’auko ruwa da lemu har kala uku, tunda ta tashi Saleem ya bi bayanta da kallo, a ranshi yace “Tabbas ke ce *target* d’ina.”

Su Bilkis ne suka ce mishi sannu dan shi ba niyyar gaishe da su yake ba saboda hankalinshi baya nan, cike da kunya ya gaishesu har Raihan ta dawo ta dire farantin gabanshi, tunda ya d’ora idonshi a kanta ya kasa d’aukewa, har ta zuba mishi lemun ta mik’a mishi ta mik’e ta koma inda take ta zauna yana kallonta, Fadila ce ta lura da kallon dan haka a ranta taji ita da zai so Raihan d’in ma ya taimaka mata saita samu Abdul ita kad’ai, yana d’an kurb’a lemun ya aje ya mik’e yace zai tafi, godiya Sameera ta masa tace ya gaishe da Abbakar da jiki, kuma insha Allahu zataje ta duboshi dan ta jima rabonta da can, Abdul ne ya mik’e ya d’an taka mishi har k’ofar gida ya shiga motarshi kafin ya bar unguwar.

Yana fita wayar Sameera tayi k’ara, d’auka tayi ta duba sunan taga sarki Imran ne, d’auka tayi tana murmushi da zolaya tace “Allah ya taimaki sarkin Basraba, k’anena ya kake?”

D’aga b’angaren Imran ne yace “Yarinyar nan fa kin gama raina ni, shekara uku na baki amma har kike kirana da k’aninki.”

Cikin dariya tace “Amma dai kasan k’anwata kake aure ko?”

Saida ya kalli Ameera wacce ke mik’o mishi smootie d’in ayaba yace “And so what? Ni kuma yayanki ne.”

Cikin dariya tace “To ya garin na ka mai martaba?”

Imran ne yace “Muguwa, ban sani ba to, kina son sanin yanda garin yake da aka ce za’a baki mulkinshi kika ce ba kya so? Gashi kinsa duk an takura ni ta ko ina.”

Tunda ya fara magana take dariya saida ya tsaya tace ” Ai na fad’a muku ba zan iya mulki ba, amma ko yanzu bata b’ace ba ai, idan ka samu labarin wata masarautar zata kawowa taku hari to kayi gaggawar sanar dani dan mu shirya dakaru ni kuma zan jagoranci yak’in.”

Murmushi Imran yayi yace “Ke ‘yar bala’i ko? To bama fatan tashin hankali mu.

Kafin tace wani abu yace “Ina mamana take da yarana?”

Saida ta kalli Ammie tace “Duka lafiyarsu k’alau, ina yaran nawa da yar uwata?”

Katseta yayi da fad’in “Dakata dallah ki saurare ni, serious magana fa na kiraki muyi.”

Mik’ewa tayi daga wurin ta shiga bedroom d’in Ammie ta zauna bakin gado tace “What’s the matter?”

Nan ya kwashe komai ya fad’a mata duk yanda ake ciki kafin ya d’ora da “Yanzu haka ban fad’awa Umma ba, dan nasan halinta ba wani farin ciki zatayi da zab’in na takawa ba, haka ma sistern ki ban san ta yanda zan fara fad’a mata ba, please Sam tell me what do i do now, wallahi i’m confuse.”

Dariya Sameera tayi tace “Hey! What trouble in this issue? Listen to me brother, maganar nan babu wata matsala ko tashin hankali, ka samu aunty ka fad’a mata komai dake faruwa, sannan ka jira abinda uncle da liman zasu tattauna, idan har maganar ta fad’a shine saika samu Ameera ka fad’a mata, i hope zata fahimce ka d’ari bisa d’ari.”

Ajiyar zuciya ya sauke yana hangen Ameera dake gyaran kayanshi yace “Ok, yanzu zanyi abinda kika ce, but make me sure k’anwarki ba zata d’aga min hankali ba.”

Dariya tayi tace “I’m verry sure, kai dallah rago wallahi ka cika tsoro, kamar dai ba jinin *Ali zaki (Haidar)*.”

Wata sayayyar ajiyar zuciya ya sake saukewa yace “Babu abinda ke kayar min da gaba a duniyar nan kamar idonki dana Ameera, sometimes bana iya kallon k’wayar idonku na fad’a muku abinda ke raina.”

Tashi tayi zata fito tace “Matsoraci, u know me ai tha’s why u scrad me.”

Daga inda yake yace “God forbid na ji tsoronki, kema duk iskancin ki ai kina shakkar wannan yaron.”

Zaro ido tayi tace “La la la la, mijin nawa ne yaro? Kai amma sarkin nan baka da mutumci aradu, amma ba komai kai da yallab’ai ne, zai sameka har Basraba dan kayi repeatn abinda ka fad’a.”

Yasan tsaf Abbas zai titsiyeshi kan ya maimaita kamar yanda tace, shiyasa yace “In dai kina k’aunar iyayenmu karki fad’a masa, abinda ma a daren nan jirgi na zai tashi zuwa Belgium (ya fad’i hakane dan tayi tunanin zai bar garin).”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected