BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Saida ya sunkuyar da kai yace “Allah ya kyauta ya kuma kiyaye gaba.”

Saida ya goya hannayenshi baya ya fara tafiya ya fita daga d’akin, da sauri Junaid ya bi bayanshi da alama kuka ya fashe dashi, ajiyar zuciya lieutenant ya sake saukewa mai k’arfi, shima fita yayi tare da Ummy data baro asibitin suka taho tare.

Ko da aka dawo Jamila tace a mata shinfid’a a d’akinsu na yan mata, a lokacin babu wanda ya kula saboda duk jikin kowa yayi sanyi *gwamnatin* gidan babu lafiya, ga kuma zulumin abinda ya faru da mamakin al’amarin, can aka gyara mata ta zauna ita da jinjirinta, basu kula ba saida Jibril ya zo yana tambayar inda take kad’ai aka gano, Soueiba da Husseina ne sukayi ta bata baki amma ta rufe ido ta botsare tace ita fa ta gama zaman gidan shi, k’yaleta sukayi da tunanin idan ta huce sai a mata magana ta koma. Tunda Zeinabu ta shiga d’aki ta kasa fitowa sai dai colonel ya shiga kawai ya fito, sai kuma Zeituna dake kai mata abinci ta aje ta fito. Haka kuma ita ke kula da Hajia tunda ta farka da la’asar, da taimakonta tayi alwala tayi sallah, da hannunta ta bata abinci tasha magani.

Bayan sallah magriba lieutenant ya shirya cikin kakin shi ya fita, oda ya bayar tare da rahoto akan motar cewa a dakatar da ita, kafin a sanar dashi ganin motar wasu abubuwan ya shiga yi, sai misalin *11:40* aka kirashi aka fad’a mishi ga motara hannu d’auke da kaya, nan yayi umarni aka taho da ita har ofishinsu inda ya fito da kanshi bayan anshiga da ita ciki, saida ya gama kallonta ya ga sak kwatancen da Ammar ne ya masa, nan yasa yaransa suka bud’e motar aka fara fito da kayan ciki, dreban na gani ya fara fad’in “Ba fa komai bane yallab’ai, indomie indomie ce sai madara.”

Wani kallo lieutenant ya masa yace “Ka bari to mu gani da kanmu.”

Pilla pilla lieutenant yasa aka ma kayan nan, sai gashi karton d’in da ake tunanin indomie ce ciki da kwalayan madara an samu tramol a ciki, haba ai sai hankalin dreba ya tashi dan baisan abinda ya d’auko ba, mai kayan aka sa shi ya kira sai ga Jano ya zo ya d’auka kamar yanda aka saba ne, idan aka rik’e kayan ko kuma aka musu awo a caji kud’i masu yawa, sam basu sarara masa ba hannun jami’an tsaro suka mik’ashi tare da dreban, sai dai shi daya rantse baisan menene ba kuma ya fad’i yanda akayi ma har ya d’auko kayan sai suka gamsu, musamman da shi kanshi Jano d’in ya tabbatar musu da babu ruwan dreban, shi ma kuma cewa yayi ba kayan sa bane, abu dai yaja daga an sake dreba Jano kuma yau gashi da kwanan magark’ama.

Da dare tana zaune ita kad’ai a d’akin ta had’e fuska, tunani take irin matakin ma da zata d’auka na wannan cin zarafi da Husseini ya mata, ita zai kunyarta ya wulak’anta a idon duniya, tana kalkad’a k’afa alamar masifa Zeituna ta bud’a k’ofar ta shigo da sallama, saida ta zo har ta aje kwanukan abincin zata fara zuba mata tace “Dakata malama bana so, fice min a d’aki.”

Da ladabi ta kalleta tace “Hajia lokacin shan maganinki yayi fa.”

“Nace bana so ki fitar min a d’aki.” Sake k’asa tayi da muryarta tace “Dan Allah Hajia ki daure…”

Tsaye ta mik’e ta nuna mata k’ofa tana fad’in “Nace ki fita ko, ko saina sa an fitar min dake ne?”

Juyawa tayi cikin sauri sauri ta fita, da harara ta bita duk sai take jin haushin matan ma, kawai ita bata yarda dasu ba, dan haka sai kowace ta fito mata da d’an da ba jininta ba, inba haka ba duk saita kaisu asibiti an gwada uban kowa dan tasan yaran da suka ciyar a banza. Tana cikin safa da marwa Ammar ya shigo da siririyar sallama, tana juyowa ta ganshi ranta ya sake b’acewa tace “Fitar min a d’aki kaji, bana son kowa ya sake shigo min d’aki ina buk’atar zama ni kad’ai.”

Rufe k’ofar yayi ya tako da sauri yana fad’in “Hajia ta nayi kewarki fa.”

Cakumota yayi ya rumgume da k’arfi yace “Kin tsoratani fa sosai, ban tab’a yarda cewa ana jin k’amshin lahira ba sai yau dana kusa rasaki.”

Tureshi tayi daga jikinta cikin tsawa tace “Kana hauka ne? Ammar fice min a d’aki kafin ranka ya b’ace.”

Hannunta ya kamo ya zaunar da ita bakin gadon ya fara zuba abincin yana fad’in “Ba zan yarda ki sake min wasa da lafiyarki ba, Hajia dole sai kinci abinci kafin kisha magani, inba haka ba zansa Alhaji ya rik’e min ke mu miki d’ure.”

Zaune yayi bayan ya gama zubawa ya d’ebo a cokali ya kai bakinta, k’ank’ance idonta tayi tace “Baka da hankali ne Ammar?”

Kai ya d’aga mata yace “Eh Hajia ta, akan ki mahaukaci ne ni.”

“Shin baka fahimtar abinda nake fad’a maka ne?”

Saida ya turo baki yace “Ai ba zan fahimta ba har abada.”

Cike da k’aguwa tace “Akan me to zaka nuna ka damu dani bayan nasan ba so na kake ba kamar yanda bana sonka?”

Murmushi ya mata yace “Saboda bana so na rasaki.”

Kallon idonshi tayi tace “K’arya kake Ammar, nasan zaka fi kowa murna idan na mutu.”

“A’a Hajia, zanfi kowa bak’in ciki.” Ya fad’a shima yana kallon k’wayar idonta, cikin taushin murya tace “Me yasa?”

Ba tare daya d’auke idonshi ba yace “Saboda zanyi kewar masifarki, zanfi kowa damuwa na rasa babbar mai yi min fad’a da zagina da kuma yanke hukunci akaina ba tare da shakku ko shawartata ba.”

Me Hajia zatayi ba dariya ba, ita kanta ji tayi ta taho mata, bata san me yaron nan yake ji dashi ba da har yake iya tunkararta ya fad’a mata abinda ke ranshi ba tare da shakku ba, ita yake kallon idonta yake fad’a mata wai zaiyi kewar *masifarta*, ba tare data tsagaita da dariyar ba tace “Ammar kai mahaukaci ne.”

Yana kallonta yace “Na sani Hajia, haka kuke fad’a kullum.”

Lomar ya mik’o mata sai kawai ta harareshi tace “Ban ci nace ko.”

Langab’e kai yayi yace “Hajia jan ajin ya isa haka mana.”

Wata dariyar ta sakeyi ta kamo hannunshi ta zura lomar bakinta, kallon bakinta yake yanda take tauna abincin yasa yake hango k’uruciyarta, abun mamaki shine karb’an abincin da Hajia ta dinga yi daga hannun Ammar kai kace dama can haka suke, shi kanshi sai yake jin abun na daban bai saba ba, duk da bata ci sosai ba haka ya aje ya bata magani tasha, tana sauke kofin daga bakinta ta kalleshi, haka kawai taji kamar kunyarshi na son lullub’eta ba gaira a dalili, aje kofin tayi a hankali ta d’ora goshinta kan gwiwarshi ta sauke ajiyar zuciya tace “Ammar kaga abinda kawunka ya min ko? Kaga irin k’ask’ancin daya ja min? Kana ganin irin tozarci da zubar da mutumcin daya min? Wane irin mataki ne zai d’auka akan shi? Akan me zasuyi min haka saboda kawai ina son kare iyalina.”

Cikin murmushi ya k’ara jawo kanta saman cinyarshi yana wasa da yatsun hannunta yace “Hajia na fahimci duk k’ok’arinki na son karemu ne daga aikata abinda bai dace ba, amma kuma tsananin da kikayi ne yasa iyalinki ke matuk’ar tsoronki, Hajia idan kana son yaro ya saba da kai ya dinga jin maganarka ba tsanani ke sa haka ba, jawo shi a jiki da wasa da shi da kuma durmiya cikin al’amuranshi, shi ke sa ba mace ba har namiji ya saki jiki da kai yana fad’a maka sirrinsa, Hajia ni baki gani ba har yanzu bana iya wani sirri da mahaifiyata ba, Abba ma yanzu ne kad’ai na fara fad’a masa damuwata, ke ma hakane Hajia ya faru da ke, da ace tun farko kinsa iyayenmu a jikinki kin nuna musu so da k’auna wallahi da sanda abin nan ya faru kawu zai sanar dake ko da yasan ranki zai b’ace, kiyi hak’uri Hajia idan abinda na fad’a ya b’ata miki rai.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected