BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi yayi ya k’arasa yana karb’an kujerar data d’auko ya aje ya zauna yana fad’in “Aunty daga wurin d’aurin aure ne kawai na wuce.”

Zaune tayi kan kujerar data tashi ta kalleshi tace “Ina kwana.”

Bai amsa ba shima yace da ita “Ina kwana aunty.”

Sosai suka gaisa kafin ta sake mik’ewa ta bud’a fridge d’in dake cikin runfa ta sana’arta ta d’auko ruwa da lemu, kawo masa tayi ta aje ta juya ta d’auko faranti ta azo kwanonin abinci da duk abinda ya dace ta zo ta aje, saida ta zauna ta kalleshi tace “Ammar ga abinci ko, nasan dai ba lallai ka karya ka fito ba.”

Kallon dattijuwar yayi cike da k’aunarta, hak’ik’a yana son mahaifiyar su Hamna, baiji dad’in rabuwarsu da kawunshi ba amma k’addara ce, ita kad’ai ce suke fahimtar junansu kuma harya fad’a mata wani abinda ya shafe shi, tun yana yaro idan an hattareshi ia ke tarairayarshi tana bashi hak’uri, shiyasa har yanzu bai manta da ita ba duk da tana gidan wani amma yana ziyartar lokaci lokaci, wani lokacin ma idan ranshi ya b’ace ne ko kanshi yayi zafi yake zuwa ta bashi shawara da rarrashinshi, bai mata musu ba domin kuwa kamar gida ya d’auki nan, har mijinta zai iya yin hira dashi hirar da bata tab’a shiga tsakaninshi da mahaifinshi ba, da kanshi ya zuba abinci yana ci suna hira ta duniya harya gama.

Su colonel ma sammako sukayi zuwa Goure, kuma cikin hukuncin ubangiji suka isa da wuri kai tsaye gidan suka nufa dan tare suke da Junaid da kuma Labaran, gidansu Maryama sun sha tarba sosai, kamar dai tarba da ita kanta Maryama ta gani zuwansu jiya tare da ‘yarta da k’awarta, nan suka k’arasa gidan malam Rabi’u inda dama ansan da zuwansu domin su gabatar da abinda ya kawosu, suna zuwa can ma tarba suka samu inda suka samu maza uku bayan malam Rabi’u, tunda Labaran ya kalli tsohon yaji fad’uwar gaban da bai tab’a jin irinshi ba, haka suka zauna suka sake gaisawa sannan malam Rabi’u yace “…

22/06/2020 à 17:26 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K’URA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

_*MASOYA NA*_

_Bismillahir rahamanir rahim_

*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`

_11_

“Nasan zaka gane muryata cikin sauk’i, dan haka ba zan bawa kaina wahala wajen sanar da kai wacece ba.”

Jin Sameera a bayanshi yasa shi juyawa ya kalleta wacce ita ma ke kallonshi saboda son sanin abinda ke faruwa, matsawa yayi sosai nesa da ita amma ita da bata fahimta ba saida ta sake bin bayanshi, domin kuwa jikinta na bata wannan wayar nada nasaba da halin da mijinta ke ciki, ganin bata daina biyarshi ba yasa shi fita daga falon ya rufe k’ofa, yana fita yace “Meyasa kika kira ni?”

Murmushi tayi wanda saida yaji sautinsa kafin tace “Jiya mun rabu babu sallama baka kuma biyani kud’in aikina ba, shiyasa na kira dan na tuna maka karka manta da kud’i na.”

A k’ufule yace “Karki raina min wayo Nasmat, kiyi gaggawar sanar dani abinda yasa kika kirani, idan kuma dan wannan maganar ne to kiji da kyau, karki sake gigin kiran wayata, idan kuma ba haka ba wallahi zansa rayuwarki a had’arin da kaf danginki sai sunyi nadamar kasancewarsu yan uwa a gareki.”

Wata dariya tayi tace “K’arfin halinka na birgeni sosai, amma naga alama ba zaka saurare ni, shiyasa ma na tura maka da muhimmin sak’o a WhatsApp d’inka, zaka iya dubawa saika kirani muyi magana idan har kana son tsira da mutuncinka dana iyalinka.”

Kashe wayar tayi inda shi kuma cikin rawar jiki ya fara dubawa WhatsApp d’in, yana bud’e vidéon nan saida ya saki wayar bai sani ba tsabar firgita, da sauri ya sunkuya ya d’auki wayar ya sake kallon abinda ke ciki, take yaji jikinshi ya d’auki rawa, ya ilahi! Meyasa banyi tunanin haka ba? Ita ce tambayar daya wa kansa, da sauri ya nemi lambarta ya kira tana d’auka yace “Me kike so?”

A tak’aice tace “Kud’i, kasan ku masu kud’in nan ba kwa tunanin talakawa da gajiyayyu, duk da kai kana k’ok’ari, to amma kasan dambu idan yayi yawa baya jin mai, kuma karka d’auka talauci ne yasa nayi abinda nayi.”

Cike da k’aguwa yace “Ki gaggauta fad’a min nawa kike so bana da lokacin b’atawa a tare dake.”

Cike da iko tace “Maganar nan ba zata yiwu a waya ba, mu had’u kawai.”

“A ina?” Cewa tayi “Ni ko a titi zan iya had’uwa da kai, bansan ba kai.”

Cikin jin haushi yace “Ba zan iya had’uwa da karya irinki a titi ba, zan turo miki da adresse d’in guest house d’ina ki sameni acan.”

Dariya tayi tace “Zan so duk inda zaka gayyace ni domin kuwa wannan videon ya shiga hannun d’an uwana.”

Tsaki kawai yayi ya kashe wayar ya tura mata adresse d’in ya shiga motarshi, hangen motarshi da tayi yasa ta fitowa da sauri tana so tayi magana, cike da damuwa ta bishi da kallo tace “Ya Allah, meke damunshi ne?”

Saida yayi jiran minti kusan ashirin kafin ta iso, tana k’wank’wasa k’ofar yayi gaggawar bud’ewa ta shigo, kallon juna sukayi inda yaji zuciyarshi na raya mishi kamar ya mata dukan mutuwa, tana shirin zama yace “Fad’a min nawa kike so na baki da zaisa ki goge wannan d’aukar ba’a iya wayarki kad’ai ba har da k’wak’walwarki ma?”

Tsayawa tayi daga shirin zaman ta kalleshi tace “Ko gaisawa ma ba zaka bari muyi ba?”

A fusace yace “Bana ciki da shirme, karki b’ata min lokaci ke nake sauraro.”

Tsaye tayi da kyau tana kallonshi tace “Ina buk’atar naira million arba’in, yau ba sai gobe ba.”

Da k’arfi yace “What!”

Matsowa yayi daf da ita ya galleta da wani mari saida ta fad’a kan kujerar da tayi niyyar zama ya nuna kanshi yace “Yanzu dama akan naira million arba’in ne kika sa na aikata zina? Akan wannan banzan kud’in kika saka na aikata abinda ban tab’a aikatawa ba tsawon rayuwa ta? Naira million arba’in kike so kika kasa fitowa ki fad’a min na baki? Nasmat kin cutar dani da rayuwata, ba zan tab’a yafe miki ba har abada.”

Mik’ewa tayi tana share hawayen wahalar da suka zubo mata tayi murmushin mugunta tace “Naji, ka tura min kud’in a wannan account d’in yanzu, ba zaka sake gani ba.”

Fizgar takardar data mik’o mishi yayi ya nuna mata k’ofa yace “Get out.”

Murmushi ta sake mishi ta nufi k’ofa, saida ta bud’e k’ofar zata fita ta juyo da murmushi tace “Mahaifiyata, tana gaisheka, baka canza a yanda muka sanka ba, saidai ka k’ara zafi sosai, kayi sukuwa akan mahaifiyata kamar doki tun zamanin k’uruciya, yau gashi ‘yar daka raina kamar ‘yar daka haifa a cikinka ita ma kayi sukuwa akanta, a gaskiya da zan samu namiji kamarka da zanji dad’in rayuwa dashi, dan ka zo min a yanda nake son namiji ya kasance min, see u *Dady*.”

Tunda ta fara maganar nan kanshi ya fara wani bala’in nauyi, mahaifiyarta, yar daya raina kamar yarsa, wa kenan? Yar daya raina har ya mata aure ita ce *Husna* yayarsu Abdul, to amma ai ba komai tsakaninshi da mahaifiyarsu Safeena, sai dai ko…

Cak yaji tunaninshi ya tsaya kanshi ya kulle, sunan da zuciyarshi ta ambata ne yayi barazanar tafiya da numfashinshi, da k’yar ya iya had’a sunan Sss… al..m…a, k’ara waro ido yayi yace “Kenan Ma’arufa ce? Na shiga uku ni Abbas mena aikata haka?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected