BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sun jima haka yana rarrashinta kafin yace “Yanzu fad’a min me kike son fad’a min tun jiya?”

Kallonshi tayi tace “Na so fad’a maka tun jiya a lokacin da kake cikin nutsuwa, yanzu kuma gashi zakayi tafiya bana so mu samu mis-understand ka tafi kuma kana hushi dani.”

Shafa kumatunta yayi yace “I promise u ba zan fahimceki ba daidai ba, so teld me what’s going on?”

Saida ta d’an ja baya ta zauna kan kujera kafin ta nuna mishi kusa da ita tace “Please have a sit.”

Zaunawa yayi yana kallonta yana fahimtar yanda maganar ke mata nauyin fad’a, sai dai baisan kome take son fad’a ba haka, dan shi dai abune mai wuya ganinta irin wannan yanayi, babu wani abu da take jin tsoro ko shayin fad’a masa sai dai in bai zo bakinta ba ko tunaninta, da k’yar ta had’a ido da shi kamar marar gaskiya tace “Dama jiya ne, Harira ta zo…nan.tare da yayanta, sun zo neman taimakonka akan iyayensu da ke rufe a cell , n…na…na fad’a musu hakan ba zai yiwu ba., shine sai ta nemi wani taimakon nawa…, kuma nayi mata.”

Wani kallo ya mata kamar mai son gano wani abu kafin yace “Idan na fahimceki daidai kamar Harira tsohuwar mai aiki kike magana a kai ko?”

A hankali ta d’aga mishi kai alamar Eh, d’auke kallonshi yayi aga kanta yana kallon gefe, ya jima haka kafin ya kalleta yace “Wane irin taimako kika mata?”

Ganin yanda yake kallon ta yasa gabanta fad’uwa tare da jin tsoron fad’a mishi, shirun da tayi yasa yace “Na ce wane irin taimako kika mata?”

Nan ma shiru tayi sai k’yabta ido da take, wani kallo ya sake watso mata yace “Are you a deep?”

Girgiza kai tayi da sauri alamar a’a, dan haka yace “To fad’a min.”

Cikin sark’ewar murya tace “À…a..aiki Na…bata…, a gi…ggg.idan.nan.”

Da k’arfi ya mik’e harda buga kujerar yace “What nonsence? What traying to teld me? Harira? A gidana? Harira again.”

Mik’ewa tayi ta kalleshi tace “You promise me.”

Juya baya yayi ya rik’e k’ugu yana sauke numfashi, ya riga daya mata alk’awari, sannan akwai alk’awura da dama daya mata wanda burinshi kullum ganin ya cika mata su, daga ciki kuwa harda mallaka mata gidan nan da duk abinda ke cikinshi, dan haka ya daidaita nutsuwarshi ya juyo gareta yace “Kina ganin hakan ba matsala?”

“Insha Allahu ba za’a samu matsala ba.”

Kallonta ya sakeyi yace “Are you sure?”

Cike da tabbatarwa tace “I’m very sure.”

“Kin yarda tayi aiki a gidanki?”

Nan ma cewa tayi “Na amince da hakan, ina ganin kamar mun taimaka mata dan suna buk’atar taimako, kuma kaga yanzu bazawara ce ita ba budurwa ba, ta k’ara hankali da rayuwa da kuma nutsuwa.”

Ya so nuna mata illar yin hakan, amma yanzu yana kan hanya ne dan haka ya rik’o hannaunta d’aya yana murzawa yace “Falmata.” K’ura mishi ido tayi dan inhar taji ya kirata da sunan Falmata to tabbas abinda zai fad’a yana da mahimmanci kuma iya gaskiyarshi ne zai fad’a, d’orawa yayi da “Sanin kanki ne na miki alk’awari da dama wanda a kullum nake son ganin na cikasu, sannan gidan nan na jima da mallaka miki shi ya zama naki har abada, dan haka banda ikon hanaki yin abinda kike so, ki kawo Harira gidan nan amma da sharad’i d’aya.”

Zaro ido tayi tace “What, sharad’i kuma?”

Murmushi yayi yace “Yeah, da me kike tunani?”

“To ina ji fad’a min.”

Ba alamar wasa yace “Sharad’in shine ko da wasa bana son ganinta a part d’ina bare naga k’afar ta a falon nan, ko da kuwa me ake ko kuma me ke faruwa ko zai faru, kin amince?”

Murmushin jin dad’i tayi tace “Sauk’i kamar shan ruwa, dama ba wannan aikin zatayi ba, dan haka i agreed.”

D’aga kafad’a yayi yace “Then, all the best wifey.”

Rumgumeshi tayi sosai harda kukan shagwab’a tace “Zanyi kewarka mijina.”

Shima saida ya sauke ajiyar zuciya yace “Ba zaki tausaya min ba ni halin da zan shiga babu rigimarki a kusa da ni.”

Ba tare data d’ago ba tace “Oho, kenan ma ni d’in rigimammiya ce ko?”

Matseta yayi yace “Number one ma kuwa in this world.”

Da k’yar suka rabu baya ya mata alk’awarin zai dawo nan da kwana uku da ikon ubangiji kad’ai ta barshi ya tafi, saida suka fito falo sun samu yara na zaune suna jiran break, sai Raihan da ita ma ake had’a break d’in da ita, gaisheda mahaifin nasu sukayi kafin ya fad’a musu zaiyi tafiya, addu’a suka bishi da ita kafin kowa ya fad’i abinda yake so a siyo mishi musamman ma Ameer da Abdul raheem, daga nan kuma part d’in su Ammie suka wuce dan basu riga sun shigo ba, nan ma addu’a yasha kafin ya wuce cikin rakiyar Sameera har zuwa bakin motarshi, drivenshi ne ya bud’e mishi amma saida suka k’ara rumgume juna kamar karsu rabu kafin ya shiga mota driver ya jasu, cikin minti talatin suka isa filin jirgi inda suka samu *captain Ali* ya gama shirya komai shi kawai yake jira, nan ma driver ya bud’e mishi ya fito yabi bayanshi da jakarshi, wata budurwa ce tsaye a k’ofar matakalar jirgin cikin uniforme d’in ta tana ganinshi ta d’an sunkuyar da kanta ta gaishe shi, ko kallon fuskarta baiyi ba ya amsa da “Fine.”

Yana fara takawa ita ma ta karb’i jakarshi a hannun driver ta bi bayanshi, suna shiga ciki matakalar ta d’ago ta rufe a hankali, jirgin dai gashi babba amma cikin inda yake zaune duka kujerun guda hud’u ne, biyu b’angaren dama biyu na hagu suna kallon juna, captain Ali ne ya fara sanar dasu jirgi zai tashi su kimtsa tare da daidaitawa, ba b’ata lokaci jirgin ya haura sama suka fara tafiya, wannan budurwar ce ta fito ta tambayeshi ko da wani abu da yake buk’ata, a tak’aice kawai ya fad’a mata da favorite d’in shi yake so, ba jimawa ta kawo mishi wata fresh milk kalar kad’ai abar kallo ce, haka suka dinga tafiya inda wannan matar duk minti talatin takan zo ta tambayeshi da abinda ya ke so, cikin yardar ubangiji sai ga k’afafun su sun taka k’asa bayan kwashe musu su da akayi, nan ma airport d’in wata motar ce ta d’auke shi zuwa wata babbar hotel ta manyan mutane.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Ko da su Ma’arufa suka sauka gidan masu zaman kansu kai tsaye d’akinta ta bud’a ta shiga, inda Ma’aruf ya shiga nashi d’akin shi ma, kaya ta cire ta fito ta d’ibi ruwa ta shiga wanka babu wanda ta kula duk da habaicin da wasu daga cikin mutanen gidan ke mata, Ma’aruf kuma fitowa yayi ya tsaya akan wasu dake buga karta a kan tabarma yana kallonsu, tana fitowa Ma’aruf shi ma ya shiga ba jimawa ya fito, amma kai tsaye d’akin Ma’arufa ya shiga hakan kuma ya haifar da k’ananan maganganu a wurin, dama dai tun zuwansu gidan basu fad’i alak’ar dake tsakaninsu ba cewa su yan uwane, sai dai wasu sunfi zargin dadiro kawai suke kuma suna rainawa wasu hankali suna karb’ar kud’in wasu mazan, yana shiga ya sameta tana saka bras, bayanta ya tsaya tare da kama hannayenta kamar zai saka mata sai kuma ya b’alle mata, a hankali yake shafa harya zura hannayenshi ya cabko nonuwanta ya masu wata matsa, cike da barikance tace “Ahhhhhh, huhhhhh.”

Juyowa tayi ido a lumshe tasa hannu ta kamo gabanshi tana lasar leb’e tace “Dama ina da haushinka, tsohuwar gurguwar nan ce ta kawo mana cikas.”

Zata had’e bakinsu ya juyar da kanshi ya kai bakinshi a kunnenta yace “Yau kuma zan huce wannan haushin nawa, dama wannan na jima da haushinsu.”

Cikin rashin sanin ciwon kai da rashin kunya da fitsara da rashin albarka suka dinga iskancinsu kai kace mata da miji ne, daga ita har shi ihu kawai suke sun mata a cikin mutane suke, suna cikin wannan bad’alar tasu wayar Ma’arufa ta fara ringing, amma saita zura hannu ta kashe wayar tana ci gaba da ihu, cike da bushewar zuciya take fad’in “Ahhhhh, washhhhh, D’an uwa na, huhhhhhh, wallahi duk kafi min kolayan banzan nan, ashe haka kake dama hhhhhhh, ahhhhhhhh, wayyo, harder.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected