BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Alhaji na tashi daga nan d’akin baccin tsohuwar nan ya shiga, zaune ya sameta cikin tsananin damuwa, sam bata san ya shigo ba har saida yace ” Duk wannan damuwar akan maganar auren ce?”

Da sauri ta kalleshi, tana ganinshi ta ja k’aramin tsaki ta sake kawar da kanta, shi kam ko a jikinshi dan ya ga fiye da haka ya kuma yi hak’urin fiye da haka, dan haka ya d’ora da ” *Zeeya’atu*, tsawon shekaru hamsin da bakwai da aurenmu, na saka miki ido kina juya yaran nan yanda kike so, dayawa daga cikinsu suna rayuwa babu farin ciki saboda kin tauyesu ta wani fannin, hatta aikin da sukeyi duk ke ce kika zab’a musu shi haka ma matan da suka zama uwayen yayansu, akwai wanda kina kallonshi zaki san baya farin ciki da zab’in naki , amma saboda biyayya sun hak’ura suna yi, to ya kamata ki sani zmanin yayan da kika haifa da zamanin yayan da suka haifa ma’ana jikokinki ba d’aya bane, yanzu ba’a tirsasa yaro yayi abinda baya so, nasan kin fara fahimtar hakan daga yanda Junaid ya miki magana yanzun nan, da wannan nake shawartarki da ki janye wannan kud’irin na cewa ba zai auri yarinyar nan ba, dan na mishi alk’awarin zai aureta kuma babu abinda zai hana hakan.”

Har ya juya zai fita ta mik’e tace “Wallahi baka isa ba, indai ina numfashi a doron duniyar nan Junaid ba zai tab’a auren yarinyar dake yawon ta zubar ba, ba dai a dangina ba, sannan da kake maganar babu mai farin ciki a ciki amma ai suna zaune lafiya.”

Juyowa yayi yace “Babu wanda yasan abinda ke b’oye cikin duhu, ki zuba ido zakiga auren Junaid da Maryama, tunda Allah bai haramta mishi ba mu ba zamu hana mishi ba, indai har zatayi tuban gaske to wannan ba matsala bane.”

Cike da rainin wayo tace “Idan ya aureta ya shigo da ita cikin gidan nan harta haifa mishi ‘ya’ya, ya’yan wa zamu kirasu? Kana so ace ai uwarsu tsohuwar karuwa ce suma kamar yanda Jibril ya kasance jika ga tsohuwar karuwa?”

Da k’arfi ya juyo ya k’ura mata ido, zuciyarshi ce ke bugawa da k’arfi yana ji kamar ya mata bugun mutuwa, saidai kuma abinda baiyi da k’uruciya ba shiyasa ba zai iya yi yanzu ba, haka ma baya so yayi magana ta hanyar bankad’o sirrin da yake ta rik’o a ranshi tsawon wannan shekarun, murmushi ya mata yace “Hum! Tabbas ba k’arya kika fad’a ba, ki sani nata karuwancin ne ya fito fili, na wasu kuma bai fito ba watak’ila talala ubangiji ya musu su gama gurza rashin mutumcinsu.”

Yana fad’a ya sa kai ya fita dan fad’an su ba k’arewa yake ba, shiru tayi tare da tunanin me yake nufi da abinda ya fad’a, ta jima a haka tana wannan tunanin kafin ta d’auki gabjejiyar wayarta ta dannawa Amar kira, dan daga kallon kayan dake jikinta da yanayin shigarta da kwalliyar fuskarta zaka san tsohuwar wayayya ce ta gidan gaba, yana d’auka cikin sanyin murya tace “Jikalle kana ina? Ka fita?”

Cikin gatsali yace “Me kike so kuma yanzu? Ni bana gida.”

Murmushi tayi har saida yaji sautinsa tace “Jikalle kuma guduna kake yanzu? Me ya sa kake haka?”

Cike da k’aguwa yace “Kinga Hajia, ni na fad’a miki bana gida, sai anjima.”

Kashe wayar yayi ita kuma ta aje gefe tana kallon wayar tace “Allah yasa ba wajen wata shed’aniya kaje ba, amma idan ma da wani abu zan gano koma menene.”

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

Jibril ma yana fita bai jima ba ya dawo gida, fitowa yayi daga motarshi mai shegen kyau da tsada, cikin falon ya tunkara ya bi ta inda zai sadashi da d’akin baccin kakarshi, saman bene ya kalla inda hayaniyar yara ke tashi sunata wasa da guje guje, yana kusa da kaiwa ya tsaya cak saboda tuna wani abu daya riga ya zamar masa jiki, a hankali ya rintse idonshi yana kallon fuskar a hoton k’wak’walwarshi tare da tuna wasu maganganu da suke gigita tunaninshi, duk da idonshi rufe suke amma saida hawaye suke zubo mishi saboda tuna wasu maganganu na k’arshe da macen take cewa ” *Idan fa ciki ya shiga jikina sakamakon hakan? Ya kake so nayi? Wai kai baka da imani ne?*”

Da sauri ya bud’a ido ya goge hawayenshi ya d’aga kai ya kalli sama yace “Allah ka kareta a duk inda take, Allah kasa bata samu ciki ba a dalilin wauta da mahaukaciyar sha’awata ta k’uruciya.”

K’asa yayi da kanshi tare da fad’i a zuciyarshi “Ameen.” Cikin sanyin jiki ya k’arasa k’ofar d’akin yayi sallama, amsa sallamar akayi daga cikin d’akin kuma harda muryar mahaifiyarshi, shiga yayi ya samu wuri ya zauna kusa da kakarshi yana fad’in “Mama sanunku, hira kuke ke da yar tsohuwa?”

Dukanshi Husseina tayi tace “Ubanka ne tsohon, ni matsa can ka bani wuri.”

K’ara lafewa yayi a jikinta yace “Ina zan matsa ni da na zo miki da muhimmiyar magana.”

Mahaifiyarshi mai sunan *Soueba* ce tace “A k’alla ka d’auki sama da wata d’aya kana fad’a min zamuyi magana amma ka kasa nutsuwa ka fad’a min.”

Sosa kanshi yayi yace “Mama yau dai zan fad’a muku tunda na samu k’arfin gwiwa daga abinda Junaid yayi yau.”

Zaro ido tayi tace “Kai duba ka kiyaye ni wallahi, kai ma rashin kunyar zakawa mutane? To babu ruwa na ni dai, Mama ku zama shaidata.”

Murmushi Husseina tayi tace “To ki barshi ya fad’a mana muji me yake tafe da shi, fad’i ina jinka.”

Kallonsu yayi dukansu yana murmushi kafin yace “Ni fa dama ina so na fad’a muku ne nima na samu matar aure.”

Dogon tsaki Soueba tayi tace “Aikin banza, dama wannan maganar ce zaka fad’a.”

Husseina ma dariya tayi tace “Wannan wacece haka zata kwashe min wannan rigimamman mijin?”

Nan ma k’asa yayi da kai cikin kunya ya kalli kakarshi ya jawo kanta yace “Zo na fad’a miki a kunne.”

Cikin kunne ya rad’a mata ita kuma ta bud’e baki tace “Iyeee, to kai ai duk gida ne, ah gaskiya nayi farin ciki da jin hakan.”

Soueba ta kalla tace “Kinji fa ke, tuwo na mai na za ayi, dan yace dai *Amna* (kamar k’anwa take gareshi saboda mahaifinta da mahaifinshi yayan wa ne da k’anwa, ma’ana ita jikar alhaji ce daya haifi ubanta, shi kuma jikan Husseina ne wacce suke ciki d’aya da alhajin) yake so.”

Tashi yayi ya fita wai shi kunya yake ji, ita kanta Soueba taji dad’i daya kasance Amna ce yake so ba ‘yar uwar haihuwarta ba *Hamna*, duk da ciki d’aya suka rayu kuma uwa d’aya ta haifesu, amma Hamna idonta a tsaye suke ga wayewa da kuma k’awaye masu ido bud’e, mahaifiyarsu *Hadiza* bata gidan yanzu shiyasa ba wani saka musu ido ake ba sosai, har ma gwara Ammar da basa shiri da ita shine ke ci mata uwa idan tayi ba daidai ba, dan akwaita da shegen yawo kullum ita ce a tafiye gidan sabuwar k’awa, musamman da mahaifinsu ya siya musu moto, ga yawan biki na k’awaye da sauran shagulgula, dan kowane wata akwai wacce zatayi bikin k’arin shekara ko kuma murnar samun wata jarabawa a makaranta, Hamna bata saka kayan kati sai atamfa, amma wani d’inkin da zaka gani a jikinta na atamfa har gwara riga yar kantin, domin kuwa bata saka kaya inba ji tayi sun kama jikinta ba sosai, bata saka zane sai siket ko doguwar riga, haka Hamna bata fita wajen biki ko wani shagali ba tare da tayi k’arin gashi na kanti ba, ko tayi kitso ko ta saka shi hakanan, indai ba sallah take ba ko zata tafi islamiyya to baka ganinta da hijab duk inda take ko zataje, yanzu haka sun shiga ajin lycée shekara biyu data wuce, rawar kanta da rashin kunyarta yasa basa shiri ko kad’an da Ammar, tana da rashin kunya da fitsara da mayar da martani, shi kuma baya d’auka hakan yasa yake mata dukan mutuwa inya samu dama, dan in mahaifiyarsu ko mahaifinsu na nan basa bari su ke d’aure mata gindi, domin kuwa a hannunsu suka tashi tun suna k’anana sosai, hatta filin sada zumunta na ahalin *Gaga* da aka bud’e akafar sadarwa ta WhatsApp Ammar fita yayi saboda Hamna kawai, saboda ko hira ake muryarta ce tafi ta kowa fitowa, ga tsokanar mutane wanda ya girmeta da wanda ta girma, ga yawon turo hotuna na sallama daban na barka da rana daban na barka da dare daban, shiyasa ranshi ya b’ace ya fita saboda haushinta yake ji sosai, duk abubuwan nan da Hamna ta had’a sab’aninsu ne ke ga Amna, dan ita ko magana ma bata cika son yi ba, ba tada kwarmniya ko kad’an, dan inma Hamna ta tsokaneta sai dai tayi banza da ita, to fa da wannan ne yasa ko murmushin Ammar baka gani a gidan, ga haushin hana shi aikin da yake so, ga takaicin rashin kunyar da Hamna ke mishi in tana cikin mutane.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected