BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mota ce ta zo wucewa ta haskasu hakan yasa ya ga fuskar Ammar d’in, amma a tunaninshi Amar ne dan shi kad’ai ya sani, ajiyar zuciya ya sauke ya saki jikinshi yace “Sannu ko, Alhaji kana lafiya? Kaine a gidan yau? Ai kuwa yanzu mahaifin naku ma suka bar nan.”

Baice mishi komai ba sai kallonshi da yake dan haka yace ” Ai ban samu damar zuwa d’aurin aurenku saboda bana jin dad’i lokacin, ya hidima kuma?”

Wani kallo ya masa yace “Ka sanni ne?”

Kallonshi yayi da mamaki, d’an murmusawa yayi yace “Alhaji ai…” Ji yayi kalmomin sun tsaya kuma ya tabbatar bashi ya tsayar dasu ba, hannun da Ammar ya d’ora akan bindigar dake k’ugunsui ce ya tsorata shi, cikin firgita yayi niyyar komawa cikin gidan yana fad’in “To sai anjima.”

Zai koma ciki Ammar yace “Dakata, ba kaine mahaifin yarinyar nan ba? umm wa take ma? Juuuuu…k’arasa min mana.”

“Jumare, Jumare, Jumare take, amma ni ban santa ba.” Duk yayi maganar ne cikin razani, sake had’e fuska yayi yace “Mu shiga daga ciki mana baba, magana na zo muyi.”

Ai da sauri ya shiga cikin gidan yace “Taho taho.”

Saida ya k’ara bud’a k’irji cikin tafiya irinta sojawa masu ji da k’arfi ya bi bayanshi, kawu da jiki ke ta rawa ya tattara yara ya turasu d’aki, Jumma ya ma tsawa yace “Ke baki da wayon kawo tabarma idan kinga mutane?”

Tana d’ago kai ta kalli wanda ke bayanshi ta hasken fitilar dake wajen gida da sauri ta tashi ita ma, d’aki ta shiga d’aukar tabarmar amma gabanta da zuciyarta bugawa suke, haka ta d’auko ta shinfid’a musu ta koma d’aki, ba tare daya cire takalmin ba ya zauna a tank’washe k’afafu amma wajen takalmin a k’asa, saida ya d’aga kai ya kalli kowace kusurwa kafin ya kalli kawu dake gefenshi tsaye ya had’e hannaye yana kallon ikon Allah, a kaikaice yace “Fulani ne ku ko?”

“Eh Alhaji.”

Kallonshi yayi ya saki fuska yace “Za’a samu nono?”

Kallonshi kawu Mamu yayi, nono kuma? Lallai yau farar rana ce a wurinshi, basu cika aiki da fura da nono ba sosai, amma yau saiya aiki Jumare ta siyo mishi fura da kuma nono mai yawa har da sukari (sugar), da sauri yace “Eh akwai, Alhaji ai ba’a rasa nono a wurin bafulatani.”

Murmushi ya mishi yace “To a kawo min, sannan a sa sukari.”

Da sauri ya shiga bukkar Jumma ya sameta, a k’warya yace ta zuba dan watak’ila bafulatani ne shima, dan duk da tsoro bai bari ya mishi kallon tsaf ba yaga sufarshi, yana zuwa ya kawo mishi ya juya zai koma ciki yace “…

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`

✪{T . N}✪️

https://www.facebook.com/101305508365889/posts/101311008365339/?substory_index=0&app=fbl

_Bismillahir rahamanir rahim_

_41_

“Zauna mana Abba, ai wurinka na zo.”

Dawowa yayi ya zauna jiki na ci gaba da mishi rawa ya d’an zauna kan turmin dake kwance yana kallon Ammar, saida ya kifa k’waryar nonon nan bakinshi yasha kafin ya sauke ya kalli kawu yace “Abba, Abba na ya fad’a min ‘yarka ce na mara d’azu da safe, kuma ya fad’a min ranka ya b’ace sosai har kana cewa ma zaka je ka rama mata, shine na hutar da kai ta hanyar kawo kaina.”

Zaro mishi ido yayi yace “Ni? Yaushe akayi haka! Allah yaro inaga dai bai fahimce ni bane, ni kam ina ni ina tab’a jikinka yallab’ai.”

Wani kakkausan kallo ya masa yace “Kana nufin Abba na k’arya ya min kenan?”

Da sauri yace “A’a Qur’ani, gaskiya ya fad’a, amma bani na fad’a ba Jumma ce, uwar yarinyar.”

Jumma na d’aki tana jinsu gatsal tayi daga d’aki ta fito tana fad’in “A’a Baffan Jumare, kaji tsoron Allah fa.”

Kallonta Ammar yayi, wani irin juya mata kai yayi alamar ta koma ciki kamar maciji, juyawa tayi ta koma tana kallon kawu Mamu, shi kuma binta yayi da fulatanci kafin ya kalki Ammar wanda shima ke kallonshi, saida ya sake kallon bukkokin sannan yace “Ina yarinyar take ne?”

“Tana ciki, ai bata jin magana ne.” Murmushi ya masa yace “Ko zan iya ganinta?”

Da sauri ya mik’e yana fad’in “Ba damuwa, yanzu kuwa.”

D’akinsu ya shiga ya sameta kwance, murya k’asa k’asa cikin harshensu yace “Kin jawo mana bala’i, to tasoyana nemanki kema, kuma karki kuskura naga kina juya bakin nan ko a b’oye ne, ki barmu mu rabu dashi lafiya dan naga ba mai hankali bane.”

Fitowa sukayi tare inda ya zauna inda yake ita kuma ta durk’usa k’asa tana kallonshi, wannan mutumin ne, hakan yasa ta k’ara shan jinin jikinta, kallonta yayi yana kurb’an nonon shi yana mata murmushi yace “Jumare ya kike?”

A tak’aice ta kalleshi ta kuma yin k’asa da kanta, murmushin gefen labb’a ya mata yace “Jumy.”

Da sauri ta kalleshi, Jumy kuma? Murmushi tayi saboda sunan ya mata dad’i ita kam, ganin kallon da take masa da murmushi yasa shi cewa “Sunan ya miki dad’i?”

Murmushi ta sake yi ta rufe bakinta hakan yasa yace ” Kina sona Jumare?”

Rufe fuska tayi da hannayenta ta mik’e tsaye ta daka da gudu d’aki, binta yayi da kallo yana murmushin mugunta, dawo da kallonshi yayi kan kawu da shima ke murmushi cike da kunyar yaron, wani murmushin ya sake mishi yace “Idan ta amince ai kaga ni da Abbana duk mun zama surukanka.”

D’an kawar da kai kawu yayi irin fa shi har ya fara jin kunyarshi ma a matsayin suruki, yana ganin haka ya tab’e baki ya sake kurb’an nononshi, aje k’waryar yayi ya tashi tsaye yace “Abba ni zan tunda kun yafe min.”

_Yaushe suka ce sun yafe?_

Gyara zaman bindigar nan yayi tare da nufa hanyar fita, bin bayanshi kawu yayi suna kaiwa k’ofar gidan yayi daidai da zuwan Jano, Ammar ya sanshi farin sani, yasan ba mutumin kirki bane, mamakin abinda ya kawo shi gidan yake yi, dan haka ko sallama bai yi wa kawu ba yace “Kai kuma fa?”

Kamar yanda ya sanshi haka shi ma ya sanshi dan dukansu matasa ne masu ji da kud’i, babu alamar sakin fuska ya bashi hannu alamar suyi musabaha yana fad’in “K’alau.”

Bai bashi hannun ba sai kallon kawu da yayi yace “Ka san shi ne?”

Jano d’auke idonshi yayi daga kansu yana kallon titi yana murmushi, yasan bala’i ne yake nema dashi kawai, shi kuma bai shirya wujijjiga kanshi ba bare ya biye mishi, kawu kuma da baya so Ammar yasan abinda ke faruwa da k’arfi ya kama hannun Jano suka koma gefe yana waiwayen Ammar dake binsu da tuhumammen kallo, yana kallo kawu ya fito da kudin da lieutenant ya bashi ya damk’awa Jano yana fad’in “Gashi malam, na biyaka dan Allah ka shafa min lafiya yanzu, karka sake zuwa gidan nan.”

Wani kallo ya mishi yana yatsina fuska yace “Ko saboda waccen ne ka hana min ‘yar taka? To ka sani waccen babu abinda zaiyi da ita wallahi, kawai zai yaudareta ne sannan ya mayar maka da ita sunan da zaka gagara kiranta dashi.”

Wani kallon kai kauce kawu ya mishi yace “Kai dallah, ana babbakar giwa wa yake jiyo k’aurin zomo, ai ‘yata tafi k’arfin dukanku wallahi, sai dai uban waccen d’in.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected