BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Gyad’a mishi kai tayi tace “Yaron nawa ma yana zuwa yanzu zan bashi ya siyo.”
Murmushi ya mata wanda ya ba Ummy mamaki, tana tsaye tana kallon shi ya d’an dafa kafad’ar ta yace ” Da kyau kaka, Allah ya sawak’e ya kara afuwa.”
Kallon Ummy yayi yace “Madame idan yaron nata ya zo ku tabbatar kun bashi ya siyo maganin, idan ya kawo ku nuna mishi yanda zatayi aiki da shi babu jinkiri, daga bisani sai ku sallame ta, amma zata dawo nan da sati biyu.”
Ummy ita tasan kawai bura uba ce yake mata, amma haka ta daure tayi murmushi tace “Ok docteur, za ayi yanda ka ce.”
Wani d’aure fuska yayi yace “Haka nake so.”
Cikin takon k’arfi ya fita ya shiga motarshi, da kallo tsohuwar ta bishi tayi murmushi tace “Allah sarki likitan babu ruwanshi, Allah ya mishi albarka.”
Kallonta Ummy tayi a ranta tace “Bala’i, tsohuwa dan baki san shi bane shiyasa kika ce haka.”
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Ana idar da sallah la’asar Hamna ta shirya cikin kayan makaranta da kuwa jakarta, saida ta sake jadaddawa Amna tsarinsu tunda ita ba zata tafi ba, a tsorace dai Amna tace “Dan Allah karki jima kiyi sauri ki dawo, kinsan fa in suka gane zan sha masifa a gurin Hajia.”
“To naji dan Allah.” Ta fad’a alamar matsuwa, fitowa sukayi falon Hajia na zaune, ganin kayan makaranta a jikinta yasa Hajia ta bita da kallo kawai bata hanata fita ba, Amna dake nesa da Hajia zaune tana kallo ne ta kalla tace “Ke kuma ba zaki je makarantar ba ne kome?”
Murya a tausashe tace “Hajia yau zamuyi hadda ne na alk’ur’ani, ni kuma kwana biyu kenan bana tab’a Alk’ur’ani shiyasa ba zan je ba.”
Shiru tayi mata Hamna kuma na jinsu amma ta fice abinta, a motonta ta tafi ba jimawa ta isa gidansu k’awarta *Nafi*, tana zuwa ta cire kayan makarantar nan ta shiga tsarawa kanta kwalliya, sun d’auki lokaci suna shiryawa kafin suka gama suka d’auki hotuna, yamma lik’is suka hau moton dan zuwa wajen kamun k’awarsu da akeyi yau wanda gobe ne d’aurin auren, a cikin *hotel jangwarzo* ne dan haka basu wani jima ba suka iso.
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Sai bayan sallah azahar ya dawo gidan bayan ya ci abincinshi a waje, dan rabon da yace ya ci abincin gidan nan harya manta, yana zuwa kayan jikinshi ya cire ya watsa ruwa ya kwanta, ba jimawa kuma bacci mai dad’i ya d’auke shi, kiran sallah ne ya farkar dashi dayake akwai babban masallaci wanda ya kasance na gidan ne dake kallon juna da gidan, a kasalance ya tashi yayi alwala ya tafi masallacin ya dawo, yana zuwa ya samu kira a wayarshi rutu-rutu, baiyi tunanin mayarwa ba ya nufi ban d’aki dan yin wanka, wani kiran ne ya sake shigowa wayarshi ya dawo ya d’auka yana tsaki, daga can b’angaren aka ce “Anyi walk’iya mun ganku, yanzu Ammar mu zakawa rashin mutumci?”
Saida ya zauna bakin gadon cikin muryar bacci yace “Idan kana son gani na ni ko ba ayi walk’iya ba zaka iya haskani da fitila, rashin mutumci kuma yanzu na fara darza muku shi, kafin nan fad’a min dalilin kiran nawa?”
*KB* da yasan halin kayanshi ne yace “D’an iska kana nan da halinka, indai za’a fad’a to sai ka fad’a kai ma.”
Kamar bashi da lakka yace “Ai ni na wuce ka kirani d’an iska, sai dai d’an rai-rai (sahara), malam muryarka na damuna fad’a min meya faru.”
Kb ne yace “Domin Allah Ammar tun yaushe muka fad’a maka da bikin *Abdullahi* ya taso? Tun shekaran jiya aka fara k’unshi amma bamu ga k’eyar ka ba, yanzu ma muna shirin tafiya wajen kamu ne nace bara na kiraka dan naga iskancin naka ba mai k’arewa bane.”
Yana d’an tattausa wuyanshi ya lumshe ido yace “Ni ne zaku gayyata wani wai k’unshi? Kawai muyita yawo a rana wai zamu je d’aukar abinci kamar ‘ya’yan da aka haifa lokacin hamada (yunwa), sannan yanzu kamun me zanje? Idan naje uban wa zan kama? Amaryar ko ango? Kaga malam nifa bana cikin wannan salon ‘yan banzancin, ranar d’aurin aure naje na shafa fatiha dani.”
Tab’e baki Kb yayi yace “Shikenan, idan baka zo ba ai nasan ‘yer uwarka ta zo ita, dan duka k’unshin da akayi na ganta har ma tana kirana da yayanta, na d’auka ma kai ka fad’a mata ni abokinka ne.”
Ba tare daya bud’e ido ba ya d’an saka hannu ya murzasu yace “Saboda ubanka ne shugaban k’asa saina zauna ina fad’awa mutane kai abokina ne? Ni na ma tab’a fad’a maka ina da yer uwa a duniyar nan?”
Jin dariyar da Kb keyi yasa ya kashe wayar ya mik’e ya shiga wankan shi, amma yana shiga sai zuciyarshi tace mishi “Wacece kenan?”
Tunani ya fara kan wacece a cikin yan matan, wani dogon tsaki yayi jin zuciyarshi ta mishi katsalandan da fad’in “Indai ba Hamna bace can su suka sani.”
Tsakin da yayi yasa yace “To ina ruwanka inma ita ce? Can ta k’arata mana, wannan dama ai kullum cikin yawon biki da gidajen k’awaye take.”
A haka ya fito daga wankan ya shirya cikin bleue riga da bak’in wando, yana d’aukar makulli da waa ya fito ya tunkari wurin aje motoci, amma sai ji yayi yana son yasan wacece a wurin taron, dawowa yayi ya shiga yar farfajiyar da zata sadaka da falon Hajia, tun anan ya ga Jamila tare da Zeinabu da kuma Soueiba da kaka Husseina, wucewa yayi yana fad’in “Barka.”
Inda Jamila ta bishi da “Ina wuni yah Ammar.”
Kamar bai ji me tace ba haka yasa kai falon, yana shiga kuma yayi daidai da fitowar Umaima da alama bata jima da dawowa daga aikin ba wanka ne tayi, ita ma bai sake bi ta kanta ba duk da tana fad’in “Ina wuni yah Ammar.”
Saida ya wuce ta murgud’a baki tace “Surukantaka da irinka ai asara ce wallahi.”
Hajia na zaune kan kujerar da kullum anan kake ganinta tana kallo da remote a hannunta tana canza tasha, kallon tvn yayi ya ga film ne na turanci tsagwaronsa amma ko ta kafe tvn da ido, murmushin jin haushi yayi ya wuce yana fad’in “Ki ba kanki lafiya, ke ba ji kike ba kuma ki tsura musu ido kamar mai ganewa.”
Da kallon banda lokacin ka ta bishi tace “Uwarka nake jira ta zo ta fassara min.”
Wayarshi dake hannunshi ya nuna mata yace “Na kira miki ita ne tayi sauri ta k’araso?”
K’wafa tayi dan tasan yanzun sai ranta ya b’ace a banza a wofi, ganin ya tunkari sama inda d’akin su Amna yake yasa ta d’aga murya tace “Kai me zaka je yi musu a d’aki? Jarabarce ta motsa ko? To fito daga nan kaji na fad’a maka, duk gaggawar ungozuma ai ta bari a haihu.”
Wani murmushin shak’iyanci ya sake mata yace ” To Hajajju mutan makka banda abinki jaraba ta motsa ai dole na samu inda zan d’ura ta, addu’arki kawai nake buk’ata ina zurawa na zura kan daidai ta yanda ba zan fito daga d’akin nan ba saina samo miki sabon shalele, ko ba komai kinga kya rabu da waccen gardin da kike kira shalele.”
Hajia rasa amsar da zata bashi tayi sai kawai tace “Zan iya d’aga maka k’afa kan duk iskancin da zakayi a gidan nan, amma wallahi karka kuskura kayi gigin kawo min d’an gaba da fatiha, ba zan lamunci haka ba, kuma dama na jima da sanin cewa kana hassadar soyayyar da nakewa shalele, ka ka ci kanka wallahi.”
K’ala baice mata ba ya k’arasa ya bud’a k’ofar d’akin kawai ya shiga ba tare da neman izini ba, Amna da fitowarta daga wanka kenan tana zaune bakin gado zata shafa mai, duk da towel d’in jikinta kakkaura ne kuma ya sauko har kan gwiwarta, amma tsananin tsoratar da tayi ba kad’an bace, yanda ya shigo d’akin take mamaki, a saninta dai anyiwa samarin gidan kashedi (interdit) da shiga d’akin yan matan haka kawai, suma kuma yan matan basa zuwa b’angaren su saida dalili, shi kanshi saida ya shigo d’in yaji yayi nadamar shigowa, dan kuwa mutanen k’asan nan da Hamna ta so tayarwa tunda safe sune yanzu Amna ta tayar daga kwanciyarsu, amma dayake masifa ce ta kawo shi sai yayi kamar bai wani damu ba ko yasa abun a kai, k’arasowa yayi ya rufe k’ofar ya tsaya gabanta, Amna data kasa tashi sunkuyar da kai tayi gabanta na bala’in bugawa da k’arfi, wata irin tsayuwar rashin d’a’a ce ya mata ta yanda da zai sunkuyo to fa kansu na iya had’uwa, tun daga nan ya tabbatarwa kanshi da Hamna ce dan wani lokacin baka iya tantance su duk da akwai d’an banbanci amma ba mai yawa ba, amma danya kamata sai yace “Ina Kankana.”