BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Turo baki tayi tace “To ai idan na fad’i sunan ne saina dinga tunawa da baya, lokacin da bana iya kallon idonka kullum kaina k’asa ina fad’a, good morning sir, good evening sir, sir your food is ready, sorry…”

Bata k’arasa ba ya dakatar da ita yace “Heee, ya isa to naji, fad’a min abinda zaki fad’a min, idan ba haka ba zaki sa Ammie ta ji kina tuna baya yanzu zata fara mita akan bautar da ke da akayi a baya.”

Dariya tayi tace “Kai kuma shine baka so ko a tuna baya? Saboda kasan baka da gaskiya.”

Saida ya sumbaci bakin Ameer yace “Indai ba fad’a kike so muyi ba a daren nan to ki fad’i abinda zaki fad’a.”

Tab’e baki tayi tace “Tunda na tuna baya kuma ai kaima kasan dole muyi fad’a, dan kasani dai ba tsoro nake ji ba.”

Sai lokacin ya kalli k’wayar idonta cikin k’ara k’asa da murya yace “Na gano ki munafuka kawai, wato neman hanyar fad’a kike dan na biye miki muyi bala’i a daren nan, dan kinsan a k’arshe kowa zai kwana d’akin shi ne ko kuma ki kawo mana Ameer a tsakiyarmu ko, to ba zanyi hushi ba kuma ba zanyi masifar ba can kiji da abarki.”

Tashin su Naseer da iyalensu ne yasa suka kallesu Abbas na fad’in “Ya dai malamai naga kun mik’e?”

Bashir ne yace “Yaya wallahi bacci muke ji, zamu je mu kwanta ne saida safenku.”

Hararanshi yayi yace “Ku d’in ne zaku kwanta tunun yanzu?”

Wani kallo Sameera ta masa tace “Yallab’ai, miji da matarshi yace bacci yake ji, meye na ka a ciki dan Allah?”

Bilkisu ce tace “Yafi so muyi ta zama anan ke kuma saboda gobe da ace ya makara bai tashi ba yace surutun mu ne ya hanashi bacci.”

Kallonta yayi yace “To ba surutun naku ke hanani baccin ba? Musamman ke da wannan mai…”

Ya fad’a yana nuna Sameera wacce ta tilasta mishi yin shiru saboda kallon data masa, fuska a had’e tace “Ka k’arasa mana kai nake sauraro.”

“Shikenan kawai abar maganar.” Ya fad’a yana sunkuyar da kai, mayar da kallonta tayi garesu sukayi ban kwana kusan duka yaran saida suka zo suka bata hannu suna fad’in saida safe, su Abba ma tashi sukayi suka musu saida safe, Abbas ne cikin shafar kai ya mik’e ya tari gaban Ammie da Ameer yace “Ammie na ce ko zaku tafi da Ameer wajenku ne yau dai kam ya tayaki hira har kiyi bacci.”

Wani kallo ta masa tace “Ban gane ba? Ni na fad’a maka ina son ya tayani baccin? Me zaisa ba zai kwana tare da yan uwanshi ba kamar kullum?”

“Eh to Ammie, da yake wai naga kamar baku tashi bacci bane yanzu.” Yana fad’in hakane dan yasan Ameer da rigima zai iya cewa a wajensu zai kwana, ko kuma idan suka samu sab’ani da uwarshi tace anan zai kwana tare da su, shi kuma yau kam yanda yake jinshi babu abinda zai hanashi sukuwa idan har ya samu filin nan.

Kallon Ameer tayi wanda keta latsar wayar Abbas bai ko san sunayi ba tace ” Wannan sarkin had’iyar ne zan tafi dashi ya kwana wuri na, ai kafin gari ya waye duk ya cinye min katakon dake d’aki na.”

Su Raudat da suma suke shirin tashi ne suka bushe da dariya, sai Raihan da murmushi kawai tayi wanda ya bayyanar da hak’oranta, Abba ne ya kamo hannu Ameer d’in yana fad’in “Yanzu takwaran nawa ne kike fad’a ma wannan maganar? Lallai ma matar nan kin samu wuri dayawa, aboki muje d’aki na ka kwana kaji ko.”

Abbas ne yace “Kuma fa Abba madarar ma da yake tashi yasha cikin dare yanzu ya daina, tunda yayi yawu kunga ai baya zauna wuri d’aya ba.”

Ammie ce ta tab’e baki tace “Ai ina d’aga mishi k’afa ne ma saboda yana da sunan na ka, amma badan haka ba ai daya gane kurenshi.”

Kamar daga sama Khalifa yace “Wai ke da duka mazanki sai kinyi fad’a ne? To idan kika b’ata mana dukanmu ya zakiyi kenan?”

Da yatsa Ammie ta nuna shi tace “Kai rufe min baki a wurin nan, ina shirin bacci ne zaka sani cacar baki, kai idan za’a kwana a hantse ba gajiya zakayi ba, parrot kawai.”

Hararan ta Khalifa yayi yace “Zan kama ki ne tsohuwa.”

Nuna Abbas tayi tace “Kaga tsohon nan bani ba.”

Kallonta Abbas yayi yace “Ammie maganar mata ce fa, ai da Ammienshi kika kira tsohuwar ko.”

Wani kallo ta masa tace “Kai yanzu waccen ta maka kama da tsohuwa a ganinka? Ko dai ba kya duban madubi ne?”

Abba ne yace “Kai kuwa ina zata kira ‘yar gwal da tsohuwa, ai sai kai data raina kuma da bata haifa ba, amma ai abin a fili yake kowa yasan waye tsoho a cikinku.”

Sun jima tsaye wuri d’aya suna wannan gardamar da cacar bakin kafin kowa ya nufi makwancinshi, da k’yar Abbas ya karb’i wayarshi a hannun Ameer wanda yace da ita zai tafi ya kwana, saida Sameera ta shirya cikin kayan bacci ta nufi fita dan zuwa d’akin Abbas, a k’ofa suka had’u wanda ya kasa jira yake ganin kamar ba zata zo ba, yana shigowa ya rufe d’akin ya rage hasken wutar d’akin, rumgume juna sukayi a cikin kunne ya rad’a mata “Kinsan da nayi kewarki?”

“Uhmmm.” Ta fad’a cikin mak’oshi, cikin salo ta fara tsotsar bakinshi har tayi nasarar kama harshenshi, salon da take masa yasa ya fara jin kamar bashi ba, ana cikin haka ta raba bakinsu ta zura harshenta a kunnenshi ta fara wasa da shi a ciki, wata sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da k’ara k’amk’ameta, daga nan komai ya canza abun ya girmama zuwa kan gado.

*Bayan awa biyu* dukansu bacci ne ke son d’aukar su, cikin taushin murya Abbas yace “My Meera ina son haihuwa dayawa har cikin zuciyata, shin kina ganin nan gaba zaki iya haifo min yara shida? Kinga idan aka had’a da wanda muke da sai su zama goma sha biyu cif.”

Zunbur ta tashi zaune tana kallonshi tace “Da gaske kake yallab’ai? Amma fa ni na d’auka zamu barsu ne daga guda shidan, kaga nima na huta ai.”

Lumshe ido yayi ba tare daya tashi zaune ba yace “Wallahi iya gaskiyata nake fad’a miki, ina so naga kin haifa min yara dayawa, amma idan ba zaki iya ba saina…”

Kafeshi tayi da ido tace “Sai kayi me? Ka k’ara aure kake nufi?”

Bud’e ido yayi a kanta yace “Eh mana, tunda ke ba zaki iya ba.”

Gyara zama tayi ta d’auki pillow ta soma dukanshi dashi tana fad’in “Je kayi auren dan Allah ga wurin nan, wallahi kana aure zan koma basraba da zama, ba zan k’ara saka kaina a had’ari ba saboda kai tunda kuskurenka ne.”

Da k’yar yayi sa’ar rik’o ta ya had’a da jikinshi sosai ya sake lumshe ido yana murmushi, ita kam k’ok’arin raba jikinta da nashi take amma ya matseta sosai, masifa take tana fad’in “Rabu dani malam ka tashi ka koma d’akin ka, ‘ya’yan ne ba zan haifa ba kaje kayi auren, naga ma ko Salma ai zaka iya dawowa da ita ta haifa maka yaran tunda har yanzu baka saketa ba, humm, wallahi kana bani mamaki mutumin nan, na ce ka saketa ka ce kayi tun tuni, na tambayeka saki nawa ka mata amma ka gagara fad’a min, nasan ma baka saketa ba saboda kana sonta har yanzu, watak’ila ma kana zagayawa wajenta ban sa…”

Da k’arfi ya matseta sosai ya danna bakinta a nashi yana mata wata mahaukaciyar tsutsa, shiru tayi tana saurarenshi saida ya saketa da kanshi kafin ya kalleta da idonshi kamar zaiyi bacci yace “Mai sunan mamana surutunki ya fiki yawa, idan kika fara bala’i ba kya tsayawa ko numfashi ki sauke.”

Zata yunk’ura ta tashi ya sake matseta yana shafa gashinta yana fad’in “Shiiiii, yi bacci kinji ko, yi baccin abinka.”

Kamar zatayi kuka tace “Amma fa na fad’a maka tun tuni cewa zamuyi magana.”

Cikin magagin baccin dake fizgarshi yace “Ki bari da safe zamuyi maganar kinji.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected