BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Alhaji dake tsaye ne cike da nuna rashin jin dad’i yace ” Dan Allah magana mai dad’i ta dinga fitowa daga bakinku zuwa kanshi, ba kusan komai k’aramtar kalma kuka fad’eta tasiri take akan yaranku ba, kuma ya kamata ace kuna hak’uri dashi, yanzu nan kunsan dan kwana uku ba zai kula kowa ba.”
D’an k’aramin tsaki yayi ya nufi d’akin shi inda Hajia ta bishi da harara da gunaguni kuma daga lieutenant har colonel babu wanda bai gani ba, duk da hakan bai musu dad’i ba amma hak’ura sukayi, Sa’ada ma da sauri ta tashi ta shiga d’akin ta tana ci gaba da kuka inda lieutenant ya bi bayanta, Hajia ma mik’ewa tayi ta nufi d’akin Alhaji dan suyi magana, hakan ne ya bawa Amar damar fita ya bi bayan d’an uwanshi da tunanin shi kawai ke kan hannunshi daya rotse yake zubar jini amma shi yaga bai ma damu ba, colonel kuma kallon Junaid yayi wanda shi dama tunda aka fara magana tsaye yake yace “Saika wuce ka d’auko min rigata d’aki, dan inhar zan shiga babu abinda zai hana ni gota uwar nan taka.”
Da sauri Junaid ya juya ya shiga d’akin, akan gado ya d’auko rigar ya fito har lokacin Zeinabu na ban d’aki, yana kawo masa ya saka fita yayi ya bar gidan shima.
Yana shiga kai tsaye d’akin magungunanshi ya shiga, zaune yayi akan gadon marasa lafiya dake tsakiyar d’akin ya duk’ar da kai k’asa ya rik’e hannun dake fitar jini, har yanzu ya kasa tsayar da hawayen dake zubo mishi, tafarfasa kawai zuciyarshi keyi na k’una da k’unci, iyayen da suka haife ni, amma kullum babu kalma mai dad’i tsakani na dasu, tun ina yaro na fahimci me kalmar d’an iska take nufi, menayi da suka tsaneni tun ina yaron da bansan daidai da rashin daidai ba? Mena aikata gare su haka dayasa suka k’ini? Shin na zo musu ba yanda suka so bane? Ko kuma guda suka so haihuwa sai ni na fara fad’owa duniyar? Ko kuma dai ni wani sirri ne tare dani da yasa kowa na gidan nan ya tsane ni? Menene shi? Wa zai fad’a min dalilin tsanar da suka min? Iyaye na su hantare ni, kakanta ta zageni ta koreni daga wajenta, da irin haka suka raine ni a gidan nan, babu wanda ya tab’a rarrashi na, babu wanda ya tab’a tambayata damuwa ta ko matsalata, akan me? Akan me! Ya fad’a da k’arfi har da saka k’afa ya ture doguwar kujerar dake gaban gadon saida tayi baya.
Saukowa yayi ya d’auki alcohol ya bud’e ya rintse ido sosai ya dararawa hannun, wani rad’ad’i ne ya ziyarce shi amma a hankali ya bud’a ido ya kalli hannun yace “Wannan rad’ad’in bai kai rabin wanda nake ji a zuciyata ba a duk sanda suka kira ni da d’an iska.”
Wasu hawaye ne suka sake taho mishi hakan yasa shi fad’awa kan gadon ya zaune yasa bandeji yana laulaye hannun yana fad’in “Kuna kirana d’an iska a kullum, shin baku tunanin na zama d’an iskan ? Namiji ne fa ni, ina da sha’awa da son jin dad’i, ba kwa tunanin tasirin addu’arku wata rana ya kaini ga aikata b’arna? Idan haka ta faru shima saik ku sake kirana d’an iska?”
Amar na tsaye k’ofar d’akin ya gagara shiga, yasan halin kayanshi ba zai tab’a bari ya rarrashe shi ba, abinda yaji kuma sai yaji kawai bari ya bashi wuri ya fad’i abinda ke ranshi ko yaji sauk’i, dan haka ya bar wurin cike da tausayin d’an uwanshi da kuma jin lallai iyayensu basa kyautawa.
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Suna tafiya kawu Mamu ya tattaro kud’i ya shigo gidan afujajen kamar wanda zaho ya koro ya shiga bukkarshi, kud’in ya aje ya fito yana k’wala kiran Zeituna, ita ko tana can wajen yan bisashen da ake kiwo a gidan tana d’aure su, da sauri ta zo ta sunkuya gabanshi cikin fulatanci tace “Kawu gani.”
Shima a fulatanci yace “Me kikeyi?”
Kallonshi tayi tace “Ina d’aure bisashe ne.”
Juyawa yayi ya kalli Jumma dake cin tuwo yace “Innar Jumare, daga yau Zeituna karta sake aikin komai a gidan nan, ko da d’auke kara ne daga nan zuwa can, aikinta a gidan nan karya wuce yin wanka ta ci abinci ta zauna ta huta, kinji ko? Har wurin aiki ma surukinta yace karta koma zuwa.”
Ya fad’a yana kama kunnenshi alamar taji, shek’ek’e Jumma ta kalleshi cikin k’warewa a harshenta tace “To me kenen zatayi idan batayi aiki ba? Ko mu bayinta ne da zamu dinga mata bauta?”
Cikin d’aga murya yace “To sai me idan kun mata bautar? Ku shekara nawa ta d’auka tana muku bautar? Ke bari kiji wallahi, tuwon ma idan har tana buk’ata a saka mata shi a baki to sai an saka mata ko da hakan na nufin zan biya kud’in hakan ne, idan kuma kika bari na kamata a gidan nan kin sakata aiki, to wallahi zan iya sakinki saki har uku, in yaso in auro yar birni ke kuma ki koma rigarku.”
Kallonshi tayi tace “To wai meya faru ne? Akan me zaka ce zaka sakeni akan wannan mayyar yarinyar?”
Cikin karsashi yace “Saboda aure zan mata nan da kwana uku, yarinya mai k’ashin arzik’i ce, yau ma daga babban gidan da take aiki ne aka zo neman aurenta.”
Tunda ya ambaci aure Zeituna gabanta ya fad’i ta d’aga kai ta kalleshi tace “Aure kuma kawu?”
Yanda yaga firgici tare da ita yasa yace “Ke kwantar da hankalinki, ba zan had’a ki da wanda ba kya so ba, zab’inki ne zan had’a ko da shi wanda yake sonki kuma kike son shi, ni ban damu da tsufanshi ba tunda dai kina son shi.”
Kalamanshi sun k’ara sakata a duhun kai, Jumma kuma cewa tayi “Hum! Ayi dai mu gani Baffan Jumare, wurin son kud’in ka saika kaita inda za’a halakata.”
Da k’arfi yace “To ba bakinki ba, yarinya dai mai goshi ce wallahi, ke kinma san waye zai aureta? To Alhaji Hassan ne, babban d’an Alhaji Suley Gaga, nan gaba kad’an nima zakiji na zama Alhaji.”
Zeituna tsaye ta mik’e ta dafe k’irji tace “Kawu lieutenant?”
Kallonta kawu yayi yace “Ke ba lantanan ba nace Hassan, tare da babanshi suka zo suka nemi aurenki, ke har ma na amshi sadakinki mun tsayar da ranar juma’a za’a d’aura auren.”
Sam ta kasa fahimta komai a zancen, lieutenant kuma? Ya zo neman aurenta? Anya kuwa! Me yake shirin sake faruwa kuma? Jin tana neman fad’uwa a wurin yasa ta juya ta shiga bukkarsu, Jumma kam dariya ta dinga yi tana fad’in “Ikon Allah, yanzu kuma abun ga tsoho ya kuma? To Allah ya kyauta maka.”
K’wafa yayi irinta haba dai zaki gama dariyarki ne idan kika ga na shigo gari nima, juyawa yayi ya bar gidan shima zuciyarshi fes saboda yana da kud’i aje a d’aki, sam ya manta da maganar wani Jano, yau ma Zeituna yanda taga safiyar nan haka taga wannan dare bata rintsa ba, tambayoyi ne birjik a ranta amma babu mai amsawa, gashi ma ance kar taje wurin aiki bare tasan abinda ke faruwa, ta rasa me zatayi da jin labarin nan, farin ciki? To akan me domin kuwa bata da tabbas, har yanzu gani take mafarki take ko kuma kawunta ne ya shiga shuhuba, bak’in ciki? To shima akan me? Da haka har asuba tayi mata bata rintsa ba saida tayi sallah bacci ya d’auke ta.
*Washe gari* sammako sosai Ammar yayi ya tafi d’aurin auren Abdullahi, ana idar da d’aurin auren kuma ya d’auki hanya sai Madarunfa, awa d’aya ta kaishi a hakan ma dan baya gudu sosai ne, kamar haifaffen garin haka ya ratsa har ya isa gidan daya saba zuwa, paka motar yayi kai tsaye kuma ya shiga gidan yana sallama, matar dake k’ulla ruwa zaune bakin panpo ta amsa da farin ciki dan ta gane ko waye, mik’ewa tayi ta nufi wajen kujera ta d’auko tana fad’in “Ammar yau kaine da safiya haka? Amma dai sammako kayi sosai?”