BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
A k’ufule tace ” Wa fa idan ba boss ba.”
Kwance tayi saboda tafasar da zuciyarta keyi ita kuma shiru tayi ta mik’e ta ci gaba da cire kayanta, ban d’aki ta nufa tana fad’in “Wallahi saina d’aukar miki fansa, ba dai ya dake ki ba, bak’in mugu kawai azzalumi.”
Tab’e baki tayi a ranta tace “Ga ki gashi ai idan ke ma kina son ganin fuskarki kamar ni d’in ne.”
*Washe gari* da safe Hajia na zaune a falo sai Husseina gefenta amma babu mai kallon wani, Hajia ce cikin yamutsar fuska tace “Ki fad’awa jikanki daga yau zuwa gobe ina son fara had’a kayan auren jikokina, dan haka ina so naga yayi bajinta ta hanyar kashe kud’i sosai, dan Jamila yar dangi ce mai nasaba da asali na k’warai.”
Murmushi Husseina tayi tace “Gashi kuma anyi sa’a mahaifin Jibril ya tara masa dukiya, kuma shi kanshi ma zai iya d’aukar nauyin duk wani caji da zaki mishi akan auren jikarki, dan haka karki damu kanki indai akan matsalar kud’i, akwaisu kuma za’a kashe ko nawa ne.”
Tab’e baki tayi ta harareta ta ci gaba da danna wayarta, Ummy ta fito a shirye zata tafi wurin aiki, sunkuyawa tayi wurin Hajia ta gaisheta, amsa mata tayi ta juya zata fita tace “Auren mijinki za ayi gobe, bai kamata ace kin d’auki hutun aiki ba?”
Tsayawa tayi ta kalleta sai dai kuma bata da abun fad’a, idan ma tace ta bayar da uzuri zata ce ai asibitin tasu ce, dan haka Ummy ta girgiza kai alamar to ta juya jiki a sanyaye zata koma d’aki kuma ta sake cewa “Yau zuwa gobe yaranku su had’a min akwatinansu, sannan babu maganar dangantaka ko alak’a, komai ina so naga anyi na bajinta yanda zai nuna harkar manya.”
Ummy da Zeinabu ne suka jinjina kai daga inda suke tsaye kafin Ummy ta koma d’aki, Hamna ce ta fito tare da Amna cikin shirinsu na makaranta, gaishe da Hajia sukayi suka nufi k’ofa, suna fita Hamna ta fito da powder ta ruwa daga jakarta ta matsa a hannunta sosai, kallon Amna tayi tace “Ki fitar da moton ina zuwa.”
“Ina zaki je?” Cewar Amna, komai ba tace mata ba tana kallo ta nufi b’angaren su Ammar, ita ma bayanta tabi dan nemo izini wajen boss, suna kusan kaiwa Amar ya fito daga d’akin shigarshi sam bata bambamta data Ammar ba, sai dai kuma fuskarshi babu annuri a tare da ita, gashi ya saka farin gilashi a ido wanda yasa ya k’ara fitowa sak Ammar, Hamna na ganin haka tayi murmushin mugunta ta tunkareshi da sauri ta sanda kanta k’asa ta fara lalube lalube a jakarta kamar mai neman wani abu, da gangan ta kaiwa Amar karo tare da saka hannayenta bibbiyu ta damk’o rigarshi tana sakin yar k’ara alamar bata lura ba, kallon juna sukayi ta kalli rigarshi da powder ta fito a rigar mai hasken sararin samaniya, ido ta zaro alamar tsorata tasa hannayen ta matsa kusa dashi ta fara kakkab’e mishi amma a zahiri k’ara damuk’a rigar take tana fad’in “Wayyo Allah na boss kayi hak’uri, kayi hak’uri dan Allah ban kula ba ko kad’an, wai ni a ina ma na samu dattin nan?”
Ta tambayi kanta tana kallon hannayen nata, Amar da ido kawai ya zuba mata kasa magana yayi sai karantar fuskarta da yake, ganin kallon da yake mata yasa ta ja baya ta fara tattare siket d’inta, yana lura da haka yayi saurin cewa “Karki bawa kanki wahala, ga boss d’in can.”
Ya fad’a yana nuna mata Ammar dake bayansu jikin motarshi tsaye duk yana kallon abinda ke faruwa ya rumgume hannayen shi a k’irji, a hankali ya taso ya fara takowa ya zuba hannayenshi cikin aljihun wandonshi yana tunkarosu, tana ganin haka da gudun tsiya hijabin daya tilasta mata sakawa yana tashi sama shima ta fita a gidan har tana bangaje mai gadi, da kallo ya bita inda Amar ya bita da dariya, kallon Ammar yayi yace “Allah ya isa wallahi, akwai muguntar daka mata wacce tasa ta rama a kaina.”
Tab’e baki yayi ya mayar da kallonshi kan Amna yana fad’in “Kai ka siya da kud’in ka, ni nace kayi shiga irin tawa?”
K’wafa Amar yayi ya juya ya koma ciki dan sake shiri, Ammar kuma matsowa yayi kusan Amna wacce tayi saurin cewa “Ina kwana yah Ammar.”
Ba tare daya d’auke idonshi daga kan fuskarta ba yace “Izinin fita ne kika zo nema?”
Da tsoro fal a idonta ta jinjina masa kai alamar eh, matsowa ya sake yi daf da ita ya zuro hannayenshi ya shafi gefen fuskarta inda ya kumbura, bud’a ijiyarta yayi yaga yanda tayi ja sosai, kallon fuskarta yayi yace “Kan ki yana ciwo ne?”
Girgiza mishi kai tayi kafin ya d’ora da “Ki daina b’ata min rai kinji ko, ba son raina bane na daki mace, amma kinga wannan banzan ko yanzu da zan ganshi saina kikkifar dashi.”
Jinjina kai kawai tayi hakan yasa shi kama hannunta yace “Muje yau da kaina zan kaiki makaranta, ki rabu da waccen kankanar.”
Tsoro ne ya bayyana a fuskarta dan ita a yanzu kam bata fatan sake fita tare da shi, juyowa yayi ya kalleta yana ganin yanayinta ya had’e girar sama da k’asa yace ” Meye? Ba kya so na kaiki ne? Ko mamaki kike? To ki saba ma dan in akayi aurenmu da kin samu ciki ba zan bari kiyi tuk’i da kanki ba, dan ni ba sakarai bane nasha wahala na d’auki tsawon awanni na zuk’urk’ula miki ciki amma cikin minti d’aya ki zubar, ba zai yiwu ba.”
Hannu tasa ta rufe baki ita dai tana kallonshi har ya bud’e motar ya zaunar da ita, rufewa yayi ya juya ta bishi da kallo, ga mamakinta sai gani tayi kuma ya nufi falon Hajia, gyara zama tayi dan tasan sai wanda ya ga fitowarshi, da shigarshi kamar yanda ya saba babu sallama, d’akin Ummy ya nufa yana kallon Hajia ya d’aga mata hannu yace “Hajajju barka da zama.”
Kallonshi tayi da harara tace “Wai kai wane irin kunnen k’ashi ne da kai? Na fad’a maka indai wannan yar iskar gaisuwar ce bana so ka daina.”
Murmushi ya mata yace ” Me yasa kika k’i fahimtar ina son fara jin muryarki ne a kowace safiya kafin ta kowa?”
Da mamaki ta kalleshi tace “Ina masifa ko?”
Murmushin ashe kin fahimta ya mata yace ” To ai ita ma d’in kyau take miki ko?”
“Ita masifar?” Ta fad’a tana zaro ido, shiru kawai ya mata nufi d’akin Ummy, da sauri Hajia tace “Kai.”
Tsaye yayi amma bai juyo ba dan ya k’osa da maganar fa shi, ganin bai ko kalleta ba yasa tace “Uban waye zai siya min tv ta daka fasa jiya?”
Juyowa yayi ya saka hannu d’aya a aljihu yace “Ki ce kawai na siyo miki tvnki amma ba ki tambayeni wa zai siya ba, idan fa nace lieutenant ne zai siyo miki sai kuma kice nayi rashin kunya?”
Yana fad’a ya juya cikin takon k’arfi ya bud’a d’akin Ummy ya shiga ba tare da sallama ba, Ummy dake tsaye gaban madubi tana gyara dogon gashinta juyowa tayi cikin tsoro, tana ganinshi ta sauke ajiyar zuciya ta juya tana fad’in “Dama waye inba kai ba, ko Kamal kafin ya shigo d’akin nan sai yayi sallama ya nemi izinin shigowa an lamunce mishi, amma banda kai.”
Kujerun dake farkon shigowa d’akin na roba mai gautsi masu kyau ya zauna a tsakiyar yana kallonta, kafin yayi magana tace “Bai kamata ba ma na b’ata yawun baki na, dan haka kamar a addininka ne aka koya maka shi, ko kuma dai matsalar da kake da ne a k’wak’walwarka tayi tasiri har a sallamarka.”
Wani d’an iska ya furzar yana sake had’e fuskarshi ya kalleta yace “Ummy zamu iya yin magana?”
Juyowa tayi tana murmushi ta zauna kan kujerar gaban madubin tace “Ina kwana Baba Ammar, fatan dai ka tashi lafiya?”
Ba tare daya kalleta ba ya d’an k’ikk’ifta idonshi alamar fa ya gaji da zancen nan, shirun da yayi yasa Ummy sanin ba fa zai iya gaisheta ba kenan, girgiza kai tayi tace “Kafin nan muyi magana akan kayan lefenku, ya kamata ku fito da kud’i dan had’a lefenku, Hajia na buk’atar shi yau zuwa gobe.”