BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Anyi bridel a rana ta biyu inda yan mata ne zalla da amarya, sai kuma rana ta uku da angaye ne suka shirya tasu didimar, ya jima da shiryawa ya fita saboda kai da kawonshi yawa gare shi, lokacin da suka zo yana k’ofar gidan da ake gwangwajewar tare da wasu abokinsu suna shigar da ruwan roba ciki, yana juyowa motarsu ta danno wajen, ta glishin motarta ya fara hangosu suna fitowa daga ciki, su hud’u babu mai k’asa da shekara ashirin da biyar a cikin, sun rik’a sun tumbatsa sai haniniya suke, in ba wanda yasan su ba kai kace ba girman garin musulmi bane, dogaye riguna ne duka jikinsu iri d’aya, kalar pink ce sai yar kwalliyar da aka musu a tsakiyar k’ugun rigar, sun kama su sosai a jiki sun fito da duka hallitinsu, dogayen takalmi ne k’afar kowace sai k’ananan poshet a hannayensu, biyu daga ciki haka suka zuba atach d’in babu kitso babu d’an kwali, Amie kuma kitso ne na atach mai kamar na roba, sai Hamna dake da korde a kanta kitson yayi kyau sosai, kallabin Amie a hannunta yake ta rik’e, Hamna kuma ta d’an d’aura shi ne tsakiyar kan wanda kamar jira yake a tab’a shi ma ya b’are, dukansu sun sha uwar kwalliya mai d’aukar hankali. Har sun fara d’aukar hotuna ko da ta ganshi sai kawai ta shige ita ma, Amie ce ta zo kusanshi tace “Namijin duniya barka.”

Juyowa yayi ya kalleta yace “Barkanki.”

Yana fad’a ya wuce ciki shi ma ya barta, bin bayansu tayi suka shiga ciki, anata shagali ba kama hannun yaro, kowa na farin ciki da dariya amma banda shi, kujera ya samu ya zauna ya buga tagumi yana kallonta, rawa suke tare da k’awayen inda angayen ke musu lik’i suna jin dad’in kallonsu, jikinta ya bata yana kallonta shiyasa ma bata yarda sun had’a ido ba, shi kuma yana mamakin yanda take son zama, ke da za ayi aurenki amma gida suka bari ta fito, wannan wace irin rayuwa ce akayi a gidan nan? Tab’e baki yayi alamar ba ruwanshi matsalarsu ce.

Mutum mugun icce (ina yawan fad’in haka), duk abin alkairi sai wani ya kawo cikas, daren yau dai ko da Hamna ta dawo gida ta riski tashin hankalin da bata tab’a tsammaninshi ba, jin kunya tozarci k’ask’anci duka taji a wannan rana, sati uku ya rage aurenta amma yau an turo manya daga gidansu Habib wai an fasa, abun takaici shine wai mahaifinshi yace “…

*Alhamdulillah*
14/10/2020 à 00:58 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_60_

Wai babanshi yace “Sai dai in bayan ranshi zai aureta, amma da ranshi dai har abada kam.”

Habib fa abun bai masa dad’i ba, amma danginshi da matarshi su abun ya musu dad’i, a ranar haka aka kwana ana jajanta wannan magana kowa na fad’in albarkacin bakinshi, kowa yana son gano bakin zaren dan yaji dad’in fad’a, Amna kwana tayi tana kukan fasa auren yar uwarta, amma ita Hamna ko a jikinta dan sai taji wani sanyi ma.

*Da safe* bayan ya dawo daga d’aurin aure ya shigo falon dan gaishe da Ummy, Soueiba Zeinabu da Hassana ya samu suna hirar abinda ya faru, abun mamakin kuma kowace hasashenta take fad’i wanda ya janyo fasuwar auren nan, shigowa kawai yayi bai kulasu ba, saida ya gaisheta ya fito ya gaishe su ya fita, zai nufi b’angarenshi ya kira wayar Amar, yana d’auka yace mishi “Har yanzu kana cikin grp d’in ahalin gaga?”

“Eh.” Amar ya fad’a a tak’aice, d’orawa yayi da “Ka fad’a musu akwai taro gobe a gidan margayi Alhaji Suley, idan mutum ba zai samu damar zuwa ba ya turo wanda zai iya wakiltarshi.”

Da sauri Amar yace “Taro kuma? Na me?”

“Kayi abinda nace.” Yana gama fad’a ya kashe wayar, kamar yanda ya fad’a haka Amar yayi, ya kira taron da babbar murya inda kowa ya amsa da zai zo, kowa tunaninshi da hasashenshi bai tab’a hasaso mishi abinda Ammar d’in ke shirin yi ba.

*K’wansu da k’wark’watarsu* haka suka taru amma banda yara, d’akin ya kaure da hira kowa na jiran yaji abinda zai masa dad’i, yasan kowa zai zo shiyasa ma yake kwance yana shan baccinshi hankali kwance, cikin abokan wasansu ne wata ta kalli Amna tace “Wai ke ina wannan d’an rainin hankalin ne? Ko kuma gadinshi zamuyi ne?”

Cikin murmushi Amna tace “To miye a ciki ma idan kunyi gadin na shi? Ai ya isa har ya batse.”

Cikin uwaye ne wata tace “Ki dai taimaka ki nemo mana shi tunda ance yana ciki bai fita ba, muna da abunyi nan da kike ganinmu.”

Mik’ewa tayi tace “To bari naga idan zan iya.” Fita tayi tana tunanin kalar mutanen da zata samu sun hau kanshi yau idan ta tashe shi, sun dai kwanta lafiya lau, amma yanzu zata iya tashinshi ya burma mata ashar yace waya aiketa? Wani iska ta furzar data tuna ai gata zai mata idan ita kad’ai ma ya kunyatar d’in, ko da ta shiga har d’akin na shi ta wuce, yanda ta barshi haka ta same shi, a hankali ta k’arasa ta kwanta bayanshi tana shafa bayanshi, ta jima haka kafin tasa harshenta cikin kunnenta tana karkad’ashi, a hankali ya fara motsa kanshi tare da mimmik’e k’afafunshi, juyowa yayi idonshi rufe ya k’ara matseta jikinshi, ganin abinda take mishi yana ratsa shi sosai yasa ta cire harshenta ta kalli fuskarshi tana murmushi tace “Barka da safiya.”

Kallonta yayi ya k’ara matsota kusa dashi ya fara sinsinar wuyanta yana shafa bayanta har ya zura hannunshi cikin rigarta, a hankali taji ya fara b’alle bras yana son kaiwa wani wurin, rik’e hannunshi tayi ta kalleshi tace “Duniyata bak’inka fa sun iso tun tuni kai kad’ai suke jira.”

Lumshe ido yayi ya jawo kanta ya rad’a mata a kunne cewa “Je envie de toi chérie.”

Kallonshi tayi tana dariya tace “Daga tashinka daga bacci?”

Turo baki yayi yace “Ce toi qui ma attaqué.”

Murmushi tayi tace “Ok, yanzu ka tashi ka shirya sai mu tafi.”

Ajiyar zuciya ya sauke ya tashi zaune, sauka yayi daga kan gadon ya d’auki doguwar rigarshi fara tas ta saka, turare ya fesa kafin yaja hannunta suka fita, cikin takon isa da mulki da izza dake nuna wannan yaron na Hajia ne ya shigo, murmushi yayi ganin cikin k’ank’anin lokaci wai suka taru haka, bai gaishe da kowa ba ya tsallaka ya zauna kujerar da Hajia ke zama kasancewar bata fito ba saboda hayaniyar mutanen, kamar tasan da zuwanshi kam sai gata ta fito, kanshi tayi gadan gadan dan son zama kan kujerarta, gyara zama yayi ya shige cikin kujerar sosai ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya yana shafar gemunshi da hannu, ko da Hajia taga haka kawai tayi shataletale ta zauna kusa da su Hassana da Husseina, dan tasan in tace ya tashi zai fad’i wani abu ne da zaisa a mata dariya, kowa kallonshi yake cikin rashin mutumci da jin haushi, saida ya gama kallon kowa ya d’ago daga jinginar da yayi yana kallon kowa.

Cikin taushin murya da girmamawa yace “Barkanku da safiya iyayena kakanni na da yayuna da k’annaina na kaina.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected