BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Kallon kallo suka shiga da tunanin waye zaiyi magana, Amar ne ya fara nuna kanshi yace “Hajia ni sunana Amar, wannan dukansu ‘yan uwa na ne, wannan d’an biyu na ne sunanshi Ammar, wannan kuma Jibril, sai wannan Junaid, dukanmu gida d’aya muke, kuma muna zaune ne tare da iyayenmu dukansu, ‘yan uwane mu da muke k’aunar junanmu, sannan muna yin komai na mu tare, wannan yasa ma yanzu muka rako d’an uwan mu ya zo gabatar muku da kanshi a matsayinshi na mai son ‘yarku.”
Kallon juna kaka da d’iyar baba sukayi kafin su sake kallesu, d’iyar baba ce cikin salon maganarta tace ” ‘Yyar mu kuuuma? Wace ‘yaa?”
Junaid ne ya kalleta da murmushi a fuskarshi yace “Maryama.”
Yana fad’in Maryama saiji sukayi tace “Ashhh.” Suna dubanta suka ga ashe wuk’ar da take yankan yakuwa da ita ce ta yanketa, kaka ce ta karb’e wuk’ar da kwanon tace “Shiyasa tun farko nace ki bari zan gyara da kaina.”
Cikin yanayin hushi ta kalli Junaid tace “Dama wannan maganar ce ta kawo ku? Maganar Maryama kuka zo yi mana? To kunga ni da idonku anbaton sunanta kad’ai abinda ya jawo, idan kuka k’ara anbaton sunanta nan gaba tafasashin ruwan can zata zubawa kanta.”
Ta fad’a tana nuna musu tukunyar dake kan wuta gaban d’iyar baba, cikin b’acin rai ta fara yanka yakuwar tana fad’in “Kalleta ka gani, tana zaune akan kujera ne dalilin wannan yarinyar, ita ta mayar min da ‘ya haka, ta riga data fad’a ai babu ita babu Mari, nima kuma haka ban san wata Mari a rayuwata ba.”
Ammar da kai ka rantse kace baisan tsiyar da suke ba ne ya aje wayarshi gabanshi ya kalli kaka yace “Ke dai baki santa ba, amma ita har yanzu tana so da kuma k’aunar ‘yarta, shin kinsan meyasa ta yanki kanta da wuk’a daga jin an anbaci sunan ‘yarta? Tsoro, fargaba duk sun ziyarceta a lokacin da taji sunan, ba kuma komai ya haddasa mata su ba sai tunanin wane irin labari muka kawo mata a game da ‘yarta Maryama, tana jin tsoron kar ace wani mummunan abu ne ya samu ‘yarta tilo, kaka, kina zaune da ita ne amma kin kasa fahimtar damuwarta, kin kasa kallon cikin idonta ki karanci rubutun dake cikin zuciyarta, baki zama mai adalci a gareta ba, da kuwa kin zama mai adalci a wurinta, to da kina kwatanta abinda take ji da a zuciyarta da abinda ke kike ji a duk sanda kika kalleta a wannan halin, nasan babu wanda yafi ki sonta a duniyar nan, kamar yanda babu wanda ya kaiki son ganin ta samu lafiya, ki daure ki kalli idonta zaki fahimci ciwo da rad’ad’in data jima tana d’awainiya dasu a zuciyarta.”
Mik’ewa yayi ya kalli su Junaid yace “Ina daga waje.”
Da kallo suka bishi dukansu banda d’iyar baba data duk’e kai tana zubar da hawaye, hak’ik’a yaron nan ya birgeta dan ya fad’i abinda shekaru ta kasa fad’a, tabbas ta gane kuskuren da tayi a waccen ranar na yi wa Mari baki, amma ba’a je ko ina ba ta gane kuskurenta, sai dai ina mahaifiyarta ta d’auki zafi sosai dole taja baki tayi shiru, shiyasa ma har idan aka d’auko maganar mari take nuna kamar ita ma ranta a b’ace yake da ita, amma kullum addu’ar ta bata wuce Allah ya dawo mata da ita gida ba, kaka da ita ma sai lokacin ne taji jikinta yayi wani bala’in sanyi har hannayenta sunyi nauyi, tunanin abinda ya fad’a take, a hankali ta juya ta kalli d’iyar baba dake kuka, cikin harshensu tace “Ki kalleni d’iyar baba.”
Saida ta gama shan majina da share hawaye kafin ta d’ago ta kalleta lokaci d’aya kuma tayi k’asa da kanta, juyawa kaka tayi ta kallesu tace “Dan Allah ina Mari take yanzu?”
Junaid ne yace “Tana Maradi.”
“Kenan can ta tafi bayan munyi watsi da ita? To me take yi acan, wurin kakanta take malam Rabi’u ko kuma Khadi?”
Da mamaki Junaid ya kalleta, idan zai iya tunawa Iklima ta anbaci sunan nan, amma kuma a yanda tace ba mazauni ne shi ba, da wannan mamakin yace “Dama kakan nata acan yake?”
Cikin sanyin murya tace “Ba can yake da zama ba, amma yana da iyali acan saboda yana yawan zuwa can wajen harkokinshi.”
D’orawa tayi da “Dan Allah in da gaske kana sonta ka ce mata ta dawo gida, wallahi a yau d’in nan na gane duk kuskuren nawa ne, bai kamata mu mata haka ba, amma ku fad’a min me take yi acan? Wajen wa take zaune?”
Junaid ne ya kalli Amar da Jibril kafin ya kalleta yace “Insha Allahu Hajia zan zan dawo miki da ita gida, na jima ina son Mari ta amince da soyayya ta, amma ta k’i yarda dani saboda waccen abun ma daya faru sam babu laifinta , tayi ne dan ceto rayuwar mahaifinta, da kuma ceton mahaifiyarta daga shiga takaba, yanzu haka ma bata san zamu zo nan ba, wata k’awar ta ce ta taimaka mana har muka zo nan, ina so na koma mata da tabbacin kun bar hushi da ita, idan har ta amince ta dawo to zan zo nan na nemi aurenta, dan nan d’in shi ya fi dacewa dana nemi aurenta.”
Kamar daga sama d’iyar baba ta kalleshi tace “Ya cikin data tafi dashi? Ta haife shi?”
Cikin sanyin jiki yace “Ta haife shi Mama, ‘yarta tana nan mai wayo sannan mai kama da mahaifiyarta, yarinya ce mai shiga rai.”
Sake fashewa tayi da kuka harda rufe baki cikin kukan tace “Dan Allah ku ce ta dawo, ina son ganinta ita da abinda ta haifa, ku bata hak’uri dan Allah, nasan bamu mata adalci ba da muka koreta, bamuyi tunanin halin da zata shiga ba idan ta var gida, watak’ila ma taje ta fad’a karuwanci.”
Shirun da sukayi yasa tayi shiru ta kallesu, ganin babu wanda yace mata komai yasa tace “Zaman kanta ta shiga?”
A hankali Amar yace “Mama karki damu, insha Allahu zata dawo gareki, dama mu abinda ya kawo mu kenan.”
Kaka ce tace “Abinda kukayi ya nuna mana ku ‘ya’yan manyan mutane ne masu dattako, da ace ni na haifi uban Mari wallahi da yanzun nan zan baka Mari halak malak, amma bana da wannan ikon tunda tana da dangin mahaifi, duk da suma sun k’i karb’arta a lokacin da mummunar k’addara ta sameta, amma dole hakk’in su ne mu sanar dasu abinda ke faruwa, anyi sa’a malam rabi’u yana garin nan, dan haka yau ba sai gobe ba zanje da kaina na sanar dashi duk abinda ke faruwa, idan zai yiwu ma sai muje tare daku wurinshi.”
D’an kallon juna sukayi kafin Jibril yace “Ba damuwa Hajia, zamu iya tafiya dan ba anan zamu kwana ba, muna so ne mu sake komawa gida.”
Da mamaki tace “Amma yaran nan kamar ana korarku, wannan doguwar tafiyar kawai dan wuni d’aya.”
Nan dai suka nuna mata eh fa komawa zasuyi, dan haka tace bari ta shirya saita fito su tafi, d’aki ta shiga ta sauya kaya da mayafi ta shafo turare na barebari mai dad’i ta fito, nan suka mik’e suka wa Mama sai sun dawo, suna fitowa Ammar na cikin mota zaune da waya a kunne, Amar dai a zuciyar shi cewa yayi “Mai abun tsiya dana kirki, da kana da budurwa da sai nace da ita kake waya.”
Junaid ne ya bud’e ata gida gaba ta shiga ya rufe, baya suka shiga su uku Ammar yaja motar ba tare da sanin inda zai nufa ba, mutanen da suka fito ganin k’wam ne suka koma tsegumi an tafi da *Magaram*, su kuma suna hanya ta dinga nuna musu wurin da hausarta da basu cika ganewa ba har suka isa dan babu nisa sosai ma tsakaninsu, sunyi sa’a samun malam rabi’u a d’akin shi na soro yana rubutu da allo, nan ma gaisawa sukayi za’a kawo musu ruwa suka ce a’a sun gode, cikin harshen barbarci kaka ta dinga mishi bayani, sun d’an jima suna hira wacce tasa suka fara tsarguwa musamman yanda suka ga malamin yana d’an d’aga murya yana magana cikin fad’a-fad’a, Ammar da ranshi ya gama b’acewa ne yace “Dan Allah ko zaku iya yin yaren da zamu fahimceku? Ko kuma idan maganar bata shafe mu ba ku fad’a mana sai musan inda dare zai mana, amma mu ba k’ananan yara ba, ba kuma jahilai ba mu zauna kuna yi damu.”