BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hamna da duk ta fahimci inda kalaman Ummy zasu dosa ne cikin muryarta data disashe tace “Ummy na fahimci me kike nufi, ba sai kin rok’e ni kan nayi shiru ba, nima abinda nake tunanin rok’onki kenan, Ummy ba zan so kowa yasan abinda ya faru dani ba, ba lallai zumuncin iyayenmu ya tab’u ba saboda duka iyayena suna k’aunar shi, amma ni zan ji kunyarsu, sannan bana so Hajia ta sani dan zata tsine min tare da shi, sannan Ummy…”

Fashewa tayi da kukan hakan yasa Ummy k’ura mata ido tana kallo, da k’yar ta tsagaita ta ci gaba da cewa “Ummy yer uwata Amna, ita ce fa wacce zai aura, kuma kinsan Hajia ba canza maganarta take ba, Ummy da wane ido zan kalleta idan tasan…idan tasan mijin da zata aure ne ya min…”

Hannunta Ummy ta kamo tace ” ‘Yata hakan yana nufin wannan ya zama sirri a tsakaninmu kenan?”

Jinjina kai tayi cikin kuka alamar eh, rumgumeta Ummy tayi tana fad’in “Nagode Hamna da kika fahimce ni, nagode da kika yarda zaki rufa masa asiri, tabbas ni uwa ce, amma karki d’auki hakan a matsayin tauye miki hakk’i, nasan an zalinceki sosai ta yanda ba zamu iya dawo miki da abinda ya fizge miki ba, amma lokaci zai zo da zaki gane hakan da nayi shine gatan daya dace na miki.”

D’agota tayi tace “Ki kwanta na dubaki na gani.”

Kunya ce tasa tace “Ba komai Ummy ki barshi kawai.”

Kwantar da ita tayi tace “A’a ba zan yarda ba Hamna, tun yanzu ne ta kamata na dubaki dan nasan waccen d’an banzan ba hankali ne dashi ba, kaca-kaca ya miki da gani ma.”

Sunkuyar da kai tayi wasu hawaye suka zuba kan k’afafun ta, tana ji tana gani Ummy ta bud’eta ta dubata, kuma tabbas akwai k’ari wanda inba d’inki aka mata ba zai iya haifar mata da matsala a gaba, cike da tausayi Ummy ta kalleta tace “Hamna kin k’aru fa sosai, gashi dare yayi yanzun nasan duk inda kawunku yake yana kan hanyar shigowa gidan, dan nasan wannan hidimar ce ta hanashi shigowa da wuri, ya kamata na miki d’inki, bansan ko zaki iya jurewa ba yanzun?”

Cikin zubo da wasu hawayen taysayin kanta tace “Ummy tsoro nake ji gaskiya, kawai ki barshi ma ba komai.”

Cike da gargad’i tace “Hamna akwai komai, ba zaki fahimci haka ba sai kinyi aure ko kuma kin haihu, gaskiya ba zan iya kallonki haka ba.”

Wani kallo ta ma Ummy, sai tayi aure? Kai amma boss ya cuceta, yanzu shikenan fa ya rabata da mutumcinta ta k’arfi? Kuma ya auri yer uwarta ita ma ya moreta, riba biyu kenan, ya jini ya ji yer uwata, k’wank’wasa d’akin Ummy akayi tayi sauri ta dauk’owa Hamna littafinta ta bata a hannu tace “Ki saki fuskarki dan Allah kar wani ya fahimta.”

Mayar da kanta tayi ga littafin ta yanda ma mai shigowa ba zai iya ganin fuskarta ba saita juya ko kuma shi ya shigo har inda take, Ummy na bud’ewa Jamila da ake aiki tare dasu ne tace “Aunty wai ki zo inji Mama.”

Murmushi tayi mata tace “Shikenan kice ina zuwa.”

Murmushi tayi ita ma tana kallon bayan Hamna tace “Yan biyun Ummy wacece a cikin? Ku ba zaku fito muyi aiki ba?”

Murmushin yak’e Ummy tayi ta juya ta kalli Hamna da ko juyowa ba tayi ba tace “Hamna ce, karatu take saboda jarabawarsu gobe.”

Juyawa tayi ta fita Ummy kuma ta juyo ta kalleta tace “Hamna zan tafi naji, dan Allah ki saki ranki kinji, komai dare idan na dawo zan miki d’inkin nan.”

Da kallo kawai ta bita harta fita, juyowa ta sake yi a hankali ta zubawa littafin ido, Ammar ne ya sake dawo mata a tunaninta tun daga shigowarshi har abinda ya faru, fita yayi ma ko bata hak’uri bare ya rarrasheta, a hankali ta furta “Allah ya isa, mugu kawai azzalumi mai bak’ar zuciya, wallahi sai mun tsaya gaban Allah ya mana hisabi.”

Ummy na zuwa naman da aka soya ne Zeinabu ta tambaye ta yanda zasuyi dashi a matsayinta na babba garesu, tana fad’a musu yanda zasuyi tace tana zuwa ta bar wurin, b’angaren su Ammar ta nufa a harzuk’e tayi sa’ar shiga saboda k’ofar a sake, tana zuwa k’ofar d’akin shi ta bud’a da k’arfi ta shiga, zunbur ya tashi tsaye dama zaune yake bakin gadon da towel ya fito daga wanka ya kasa katab’us, yana ganin Ummy ce kuma yanayin fuskarta ya nuna mishi abinda zai faru, shi kuma yau ya yarda yayi laifi kuma zai bayar da hak’uri, dan haka kafin ta k’araso ya durk’usar da gwiwoyinshi k’asa ya sanda kanshi yana jiran hukunci, Ummy na zuwa gabanshi ta d’auke shi da mari har saida ya tangad’a, yana dawowa daidai ta sauke kai mishi wani marin a d’aya kumatun tasa k’afa ta hankad’ashi ya fad’i warwas k’asa, tashi ya sakeyi ya koma yanda yake a farko yana kallonta yace “Ummy ki min duk hukuncin daya dace dani, wallahi zan d’auka, amma dan Allah karki tsine min Ummy, ba zan iya jurar tsinuwarki ba, Ummy kada ki zageni dan Allah, dan bansan inda hakan zai sake kaini ba.”

Cikin zafin rai ta sake kashe shi da mari duk da rad’ad’in da hannayenta keyi, sunkuyawa tayi kamar zata fad’a kanshi ta nuna kanta tace “Ammar me nayi maka? Me na aikata maka da wannan hukuncin ne kad’ai ya dace dani? In haifeka a ciki na amma kullum burinka shine kaga ina zubar da hawaye, akan me Ammar? Meya kaika d’aki na a daren nan? Me tayi maka da sai kayi mata fyad’e ne kad’ai zaka huce? Ammar akan wane dalili ne kake son raba zumuncin dake tsakanin iyayenku? Kasan abinda hakan zai iya haifarwa kuwa? Baka sani ba? Kawai kenan iskancinka ne ya motsa ka kuma rasa inda zaka sauke shi sai akan yer uwarka, yarinyar daka rainesu a hannayenka, yarinyar da kake nuna baka k’aunar ta, babu abinda ka saba mata dashi sai muguntarka, yanzu shikenan ka ida zama dodo a wurinta, kasan irin b’arnar da kayi? Ka lalata mata komai, ka k’wace abu mai daraja a gurinta, tirr da hali irin naka, wai kai kana da zuciya ma a k’irjin ka? Meyasa da bak’ar jarabar taka ta taso baka fita ka nemi matan banzan daka saba bi ba, dan ba zan tab’a yarda da kai ba idan kace min baka tab’a yi ba sai yau, dan ta’asar da kayi tafi k’arfi ta d’an koyo, alamu ne na wanda ya saba kuma a dole yake neman sauk’in jarabarshi.”

K’ura masa ido tayi tana kallo hakan yasa shi kama k’afafun shi cikin kukan jin zafin kalamanta yace “Ummy ki yarda dani, wallahi ni ba d’an iska bane, ban tab’a zina ba, dan Allah Ummy kiyi hakkk…”

Bai k’arasa ba ta fizge k’afafun ta ta juya zata bar d’akin, tsayawa tayi bakin k’ofar ta juyo ta kalleshi tace “Ammar ka tabbatar min kai tantagaryar d’an iska ne na gidan gaba, nagode maka.”

Da sauri ya d’aga kai ya kalleta da tsantsar mamakin jin furucin daya fito daga bakinta tare da jin zafi a zuciyarshi, jinjina kai tayi tace “Eh, saboda kai iskancin naka daya tashi ma a cikin gidanku kayi, a cikin gidanku ma akan k’anwarka, da k’anwar taka ma kuma Ammar cikin d’akina, d’akin mahaifiyarka, akan gadon iyayenka, Ammar wace irin lalacewa ce wannan? Ka kwanta da yarinya akan gadon da iyayenka ke kwanciya, Ammar abinda ya faru ya isa yasa na tsine maka albarka ka shiga duniya, amma ba zanyi haka ba saboda in nayi haka to nasan wata rana ni zaka farmaka.”

Zaro ido yayi da matuk’ar alamun tashin hankali da yanda maganar ta sokeshi, mahaifiyata? Take tunanin na…?

D’orawa tayi da “Dan Allah daga yau karka sake shiga d’akin, bana buk’atar gaisuwa ko samun girmamawa daga gareka, sannan ka fita harkar Hamna, karka nunawa kowa wani abu ya shiga tsakaninku, inba haka ba kuma har ni za’a tsine ma a gidan nan, dan Allah ka min wannan alfarmar.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected