BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Su Amar banda dariya babu abinda suke, amma Ammar kamar baisan sunayi ba sai tuk’i da yake, a *Ague* sukayi sallah magriba suka sake wucewa, wannan karan ba jimawa suka shigo cikin gari sai dai anata sallah isha’i saboda tsakanin lokacin dama ba wata tazara ake samu ba, sannan gashi Ammar ba wani gudu sosai yake ba da zai kawosu gida cikin k’ank’anin lokaci, suna kaiwa *immeuble Gago* ya taka birki ya juya yana kallonsu, Junaid dake gaba ne ya washe baki saboda hango mai gasa kaza da yayi ya kalli su Amar yace “Kai ‘yan uwa, babban yaya fa kaji zai siya mana mu ci, kai Allah dai ya k’ara girma yayanmu.”
Wani jan kallo Ammar ya mishi yace “To jikan kura, kazar uwar wa zan siya muku? Sai kace na d’auko karuwa a mota zan tsaya siyen nama a hanya?”
Jibril ne ya kece da dariya yace “Wato ita karuwa idan aka d’auko ta sai an siye nama?”
Ko kallonshi baiyi ba sai gani da sukayi ya bud’e ya fita ya zagaya mazaunin Junaid, da sauri Junaid ya fito ya dawo mazauninshi ya tayar da motar suka fara tafiya, cikin masifa Ammar ke fad’in “Shegu ‘yan banza, ai dama zura muku ido nayi naga mai hankalin da zai iya karb’ar tuk’in nan a hanuna, ashe duk k’ananan marasa mutumci ne ku.”
K’wafa yayi sai Amar da yace “Yi hak’uri yaya, ni wallahi in so na karb’a amma a raina kuma nace watak’ila dan kana babba ne shiyasa ka hutashe da yan uwanka ababen soyuwarka.”
Wata ashar ce ya malmalo irin ta yan zamani yace “Na soya mata…”
Gyara zama yayi ya jingina tare da lumshe ido yace “Ku tanadi abinda zaku fad’awa tsofaffin can, dan ni nan banga abinda zai sani magana ba.”
Kallon kallo suka fara, ai kuwa sai suka fara shiga k’irk’iro labarin da zasu fad’a a gida wanda zai dace da hankali, suna tsaka da haka Ammar da idonshi ke rufe yace “Ya kamata kusan cewa da Allah yana so ku zama sakarkaru to fa daya halliceku babu baki, akan me zaku musu k’arya? Duk cikinku akwai wanda zai tsireku ya rataye? Ko kuma akwai mai wutar da zai saka ku a ciki? Kunga, ban yarda na biku ba saida na tabbatar aikin alkairi muka je yi, amma kuna so ku mayar da kanku lusarai kamar ba maza ba, a hakane yanzu kuke so kuyi aure, to ya zakuyi da matan?”
Cikin turo baki irin na shagwab’a Junaid yace “Yanda kowa yake yi da su mana.”
Tsaki Ammar yayi ya bud’e ido ya kalleshi yace “Shin ko kasan a cikin maza akwai mata-maza? Sannan akwai muna-maza, kamar yanda ke akwai mun rako maza duniya, to zaku kasance d’aya daga cikin ukun nan ne in kuka ci gaba da haka.”
Amar ne yace “Ammar zafa mu baka mamaki wallahi, ai namiji zai amsa sunanshi ne a lokacin da yake iya ciyar da matarshi, yake mata sutura iya iyawarshi, yake kula da lafiyarta da addininta, sannan yake gamsar da ita a shinfid’a.”
Murmushi yayi wanda Junaid dake gaba ne kad’ai ya gani kafin yace “To ko ita gamsarwar da kake magana a kai tana buk’atar zarra, sai ka zama namijin gaske kafin ka gamsar da yan matan yanzu, idan kuma ba haka ba wallahi kaine zaka wahala har ka zubar da hawaye, dan irin kayan da suke anfani dasu wajen gyara jikinsu sunfi k’arfin tunaninka.”
Jibril ne ya d’an lek’o kai ya dafa kafad’ar Ammar yace “Babban yaya ince dai in zamuyi aure kai zaka zama malamin mu?”
Bige hannunshi yayi ya juyo a harzuk’e yace “Saboda d’an iska ne ni?”
Kwashewa sukayi da dariya, suna tsaka da dariya yace musu “Billahil-azeem duk wanda ya fad’a musu k’arya saina tona asiri, dan ni ba zan yarda ayi k’arya dani ba.”
Da haka dai suka iso gida suka danna ham () mai gadi ya bud’e musu suka shiga, a wajen ajiye motoci suka paka ta su kafin suka fito cike da gajiya, cikin wani takon izza da k’asaita Ammar ya nufi b’angaren su, Junaid ne yace “Ammar ka zo mu fara shiga ciki dan Allah, ni nafi son ayita ta k’are.”
Tsaye yayi ya juyo ya kalleshi yace “Kai ne uban tafiyar ai, ka fara shiga ciki ka fara d’aukar naka rabon, ni daga baya na shigo bayan nayi wanka.”
Jibril ne yace “Amma dai da mun fara shiga a mana bala’in, in ya so daga baya ma huta gajiyar.”
Rai had’e yace “Na ce wanka zanyi ko.”
Amar daya d’an lek’a kusa da falon Hajia ne yace “Ka zo muje dan Allah, wallahi nasan mu suke jira dan ayi magana.”
Juyawa yayi ya fara tafiya yana fad’in “To duk wanda ba zai iya hak’ura na fito daga wanka ba kuce su sameni a ban d’akin sai muyi maganar.”
“Kana wankan?” Cewar Jibril yana zaro ido, ba tare daya juyo ba yace “To meye a ciki, su d’in iyayena, ku kuma yan uwana ne maza, hallitar iri d’aya ce, ko kun kalla babu abinda zaku ji a ranku, wannan tsohuwar ce ma kawai bana so ta ganni babu kaya, kallon data min ina yaro ma ya isa haka, taje ta kalli mijinta.”
*Ma Sajida sai kin taimaka min da lema (para-pluie) wacce zan dinga kare wannan katob’arar fa, dan wani abun idan ya murguzo kasa duk’ewa nake.*
Lieutenant da yake son fita amma Hajia tace babu inda zashi sai yaran sun dawo taji daga inda suke, yana jin k’arar motar ya fito ya duba, ai kuwa a lokacin da Amma ke tafiya zai bud’e k’ofar b’angaren su suka ji yace “To ku wuce muke ciki.”
Take suka fara rarraba ido suna kallon kallo, kamar wanda k’wai ya fashe ma a ciki haka suka fara tafiya, murmushi Amar yayi yace “Abba barka da dare.”
Dak’uwa ️ ya watso mishi tare da nuna musu hanya su wuce gaba, Ammar dake kallon abinda ke faruwa baida niyyar tahowa, lieutenant ne yace “To ubana, sai nayi magana ko?”
Wani farrrr yayi da ido kamar mace na son karb’ar kud’i hannun mai gida kafin ya taho ciki takun k’arfi, saida ya kawo daf dashi zai wuce lieutenant ya d’aga hannu da nufin bugunshi a k’eya, da sauri ya duk’e tare da ja baya ya d’ago yana kallonshi yace “Abba wai sau nawa zan fad’a maka ka daina sarar dukana a kai? Kayi karatu fa, ko dai ka manta abinda ka karanta ne a cikin aji game da abubuwan dake cikin kai?”
A hassale lieutenant yayi kanshi ya zura hannu zai shak’o wuyanshi ya sake zillewa, tsaye yayi yace “To wai yanzu dukana ne kake so kayi ko me? Kasan dai na wuce wannan matakin ko?”
Saida ya nuna shi da yatsa yace “Dan Allah ka zo nan ka gani idan ban dake ba, Ammar ni zaka raina ka mayar wani mahaukaci.”
Saida yayi nesa dashi ya ya wuce ya nufi falon Hajia yana fad’in “So ne kawai yake a kafa min mugayen hak’ora, ya bini a guje ya fad’i shikenan ace na kashe ubana, haba, tsofi sai jaraba bakinsu ko ciwo baya yi.”
Yana dosowa falon ya canza salon tafiya da yanayin fuska irin ba magana kuma ba wasa bare dariya, yana shiga ya samu su Junaid sunyi cirko cirko zaune a k’asa kowa kanshi k’asa, gefenshi ya kalla inda Ummy, Soueiba da Zeinabu suke zaune, sai gefe guda su Amna ne da Umaima ke ta latsar wayar amma banda Hamna dake shan kankana da cokali mai yatsu, “Wato dan raini a gaban yaran nan za’a musu fad’a? Kai ba zai yiwu ba gaskiya.”
Kallonsu yake yana so su kalleshi ko zasu fahimci kallon amma rashin sa’a babu wacce ta kalle shi har kankanar ma, a hankali ya cire takalmi ya k’arasa kusansu Junaid, amma saboda iko sai yayi zaune akan kujera yana kallonsu su dake k’asa kamar sun zo d’aukar karatu, Ummy ya kalla wacce idonta ke kanshi kamar ta zundumo mishi zagi, kallon Husseina yayi dake zaune kujera d’aya da Labaran da kuma Alhaji, hannu ya d’aga musu ba alamar fara’a yace “Barkanku da dare.”