BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
D’aga kafad’a yayi irin ohon nan yace “Ki tambayi *uwar Shureim*.”
Wani galala Ummy ta kalleshi a ranta tace “Kaji wani wai uwar Shureim, to wannan ya ma bari har a gama fad’a ma wanda ya dacen kafin ya fara kiranta da wannan sunan?”
A fili kuma cewa tayi “A gaskiya bana tunanin zata fad’a mata, amma kuma abun da mamaki sosai.”
Bud’ar bakinshi cewa yayi “Ummy karki ba kanki wahala wajen sanin yanda akayi taji, kawai share zancen.”
Hajia ce tace “Kunga, hak’uri zamuyi mu daure a fad’a mata, kamar yanda na fad’a muku ko saboda halin rayuwa, abinda nake so ku fahimta shine idan yanzu bata sani ba a k’arshe kuma ta ji a wani wurin aka tabbatar mata da gaskiya, to fa ba zata ji dad’i ba kuma mummunan abunda ba ayi tsammaninshi ba zai iya faruwa.”
Jinjina kai yayi yace “Gaskiya ne, na yarda a fad’a mata amma ba yanzu ba gaskiya.”
Ummy ce tace “Eh gaskiya kam, bai kamata ba dama a fad’a mata yanzu, saboda har yanzu ni dai jikin nan naya yana bani tsoro.”
Hajia ce tace “Shikenan yanda kuka ce, a jira ta samu lafiya sai a sanar da ita.”
Ammar ne ya mik’e tsaye ya kama hannun Shureim yace “Zan fita mu dawo.”
Da murmushi Ummy tace “A dawo lafiya.”
Da kallo suka bisu har suka fice, Ummy ma godiya ta ma Hajia ta fita tana jin kamar ta taka rawa tsabar farin cikin da take ciki. Wani ikon Allah suna fita farfajiyar zasuyi wajen ajiyar motoci suka had’e da ita ta dawo daga wajen kitso, cikin murna ta bud’e hannayenta zata d’auki Shureim, baya yayi da shi yana kallon fuskarta, kallonshi tayi fuska a had’e tace “Shureim zo nan.”
Wani murmushi ya mata, bayan tsawon lokaci rabon da bakinsu ya had’u yau sai gashi dalilin Shureim yace mata “Fita zamuyi.”
Bata kula da abinda ya fad’a mata ba ta zura hannu zata jawo shi, k’ara baya yayi dashi yana kallonta shi ma fuska a had’e yace “Na ce fita zamuyi dashi yanzu, ko kuma ban isa bane?”
Wani kallon rashin mutumci ta masa tace “To miye na tambaya ta bayan gashi ka bawa kanka amsa.”
Kai tsaye take nufin bai isa ba kenan, matsowa yayi kusanta sosai har numfashinsu ya fara gauraya ya kalli k’wayar idonta kamar yanda take kallon na shi babu rusunawa yace “Wallahi *kinci albarkacin yaron nan dake tskaninmu*, ba dan haka ba da saina na zubar miki da k’ananan aljanunki, marar kunya kawai da baki iya girmama mutane ba.”
Zaro idon da tayi alamar ya akayi haka yasa shi saurin katse mata lissafi da cewa “Eh, na sani, sai kuma yaya yanzu? Shashasha kawai.”
Wucewa yayi har ya fara tafiya sai kuma ya tsaya ya juyo, duk da bata juyo ba saida yayi murmushi yace “Zaki iya tuna na tab’a fad’a miki sau d’aya nake aika d’an sak’o na kuma ya isa inda nake da muradin yaje? Ki kama kanki yarinya ko kuma…”
Wucewa yayi rik’e da hannun Shureim ya barta tsaye, saida taji sun tayar da mota tayi saurin wucewa ciki kamar zata tashi sama, bata kula ba tayi karo da Ummy dake niyyar zuwa b’angaren Amna, suna had’a ido ta kama hannunta da k’arfi ta jawota suka k’arasa fitowa daga falon, saida ta juya ta ga babu kowa tace “Ummy, waya sanar dashi maganar nan?”
Dariya Ummy tayi ganin tsoron dake fuskarta duk ta furgice tace “Kwantar da hankalinki to? Ni ai ke zan tambaya wa kika fad’awa har ya fad’a ma Amie maganar nan?”
“Me? Amie kuma?”
Cikin mamaki tace “Ummy ni ban tab’a maganar nan da kowa ba.”
“To ya akayi Amie taji har ta fad’awa Amna?”
Gaba d’aya idonta ta k’walalo waje ta dafe k’irjinta dake bugawa da k’arfi, dafata Ummy tayi tace “Kwantar da hankalinki mana.”
Girgiza kai tayi tace “Ummy Amna fa kika ce? Taji wannan maganar? Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un, Ummy na shiga uku na lalace, Amna da shegiyar zuciya.”
Murmushi ta mata tace “Yanzu dai ki fara nutsuwa tukuna sai kiji abinda ya faru.”
Cikin saurin maganar da bata san ta iya shi ba tace “Ummy ina maganar nutsuwa kuma kawai ki fad’a min komai.”
A hankali Ummy tace “Shi ya fara samu na da maganar yace Amna ce ta fad’a masa, ita ma kuma wai Amie ce ta fad’a mata, amma fa ita ta d’auki maganar da wasa, muna cikin maganar kuma Hajia ta fahimci akwai matsala ta ja mu d’akinta.”
Shirun da tayi ya ba Hamna damar d’ora hannayenta saman kanta tace “Na shiga ni Hamna, na mutu shikenan, Ummy sai me ya faru?”
D’orawa tayi da “Magana mukayi ta fahimtar juna, Hamna idan kika ga yanda Hajia ta fahimce ni har ta bamu shawara wallahi zakiyi mamaki.”
Da sauri ta rik’o hannayenta tana fad’in “Ummy kina nufin ba tayi fad’a ba?”
Girgiza kai tayi tace “Ko kad’an in fad’a miki.”
Kamar zata fashe da kuka tace “Amma kuma Ummy Amna fa? Ina tsoron ranar da zata ji da abinda zata iya yi wallahi.”
Cikin taushin murya tace “Insha Allah ita ma zata fahimce mu fiye ma da Hajia, abinda kike tunanin tayi ba zai tab’a faruwa ba, Amna tana da hak’uri sosai.”
“Amma kuma tana da zuciya Ummy.” Ta fad’a tana sako siraran hawaye, hannu tasa ta shafe mata tace “Dan Allah karki d’aga hankalinki Hamna, ki nutsu ki shiga ki samu kiyi wanka ki ci abinci, karki yarda wani ya gane kina cikin damuwa, muyi addu’a yanzu Allah ya bata lafiya, ke baki ji abinda ta fad’a ba kwana uku da suka wuce, kallon mahaukaciya ma take wa Amie fa.”
Jinjina kai tayi tace “Shikenan Ummy.” Shigewa tayi ciki Ummy ma ta nufi b’angaren Amna.
Ko da taje ta samu an ba wa Amna maganin zazzab’i tasha, d’aki suka ce taje ta kwanta ta huta da kwaramniyar nan, da shigarta d’aki baifi minti sha biyar ba Hamna ta shiga dubata, kwance ta same sai rawar d’ari take, ko da ta tab’a jikinta taji zafi sosai kamar garwashin wuta, idonta sunyi jawur da su kamar ba nata ba, Ummy ta fito ta fad’a ma suka shiga tare, ko da ta ga jikinta tace kawai su kaita asibiti, ba b’ata lokaci Hamna ta jasu dan Ammar ya riga da yayi nesa da gida, acan ya samesu har san jona mata k’arin ruwa. Tsananin zafin jikin baya raguwa sai sama yake, cikin d’an lokaci k’ank’ani ta canza ta fice a hayyacinta, da fari an k’ara mata ruwa sai aka nemi jini ma aka k’ara mata.
Allah da ikonsa kafin gari ya waye ba zaka tab’a kallon Amna kace ita ce ba, ta gigice ta canza duk ta disashe ta zama abar tausayi, gashi tayi kamar ta kumbura a jikinta, zuwa wayewar gari saida aka saka mata wani tiyo dake kai mata ruwa, a hannayenta k’arin ruwa da jini, n’aurar taimaka mata wajen numfashi abubuwan kamar ba a jikin mutum ba.
*Sai daren ranar* kad’ai likitoci suka d’an samu kan matsalar, Ammar ne zaune gaban likitan ya k’ura masa ido inda zuciyarsa ke dukan uku uku, ya kasa had’a yawu ko alama sai tattarasu yake yana son turasu mak’ogoronshi amma sun k’i wucewa, likitan ne ya mayar da hankalinshi kanshi cikin nutsuwa yace “Docteur ya kukayi sakaci haka da marar lafiya? abu ne dake matuk’ar wuya samun irin haka a lokaci d’aya, kuma da an ankara da wuri da an cire mata d’aya a barta da d’ayar, yanzu gashi lokaci ya k’ure mana sosai.”
Ammar dake kallon bakinshi kamar kurman dake fahimtar yaren leb’e ne yace “Ban cika fahimtar ka ba fa, ka min gwari gwari zan fahimta.”
Saida ya dan furzar da iska ya kalli tsakiyar idonshi yace “Duka sun lalace, k’wadarta.”
Da sauri ya dafe kanshi da hannu biyu, sosai yake matse kanshi yana so yaji ya daina sara masa amma abun ya ci tura, da k’yar ya d’aga kai ya kalle shi yace “Ta yaya? Duka biyun zasu lalace lokaci d’aya? Ta yaya dan Allah? Me ye abunyi yanzu?”