BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani murmushin mugunta ya sakar mata tare da jerawa kusa da ita ya kama hannunta, a tare suka ji wani shocking ya baibaiye su, sororo take kallonshi tana zubo da hawaye tana ci gaba da bashi hak’uri, hankalin mutane ma baya kansu Hamna kuma har juyowa take taga ko da wanda zai iya rabata dashi, amma wak’ar da aka saka yasa hankalin kowa ya koma kan yaran dake rawar, suna fitowa ta kan matantakalar dake k’ofar shiga da ba tafi uku zuwa hud’u ba, yana saukowa daga na d’aya dana biyu ita kuma ta cije ta k’i gusawa, juyawa yayi ya kalleta, haushi ne ya sake kama shi wai akan me zata dinga fita haka tana tallar kanta a waje, k’wafa yayi tare da zagaya hannunshi ta bayanta kan cinyoyinta, d’aya hannunshi kuma ya kamo nata hannun ya wurgashi kan wuyanshi, cak ya d’auke ta ya d’ora kan wuyanshi ya nufi mota da ita, ihu take tana wutsil wutsil da k’afafu tana so ya sauke ta, boot taga ya bud’e ya nufi nan da ita, ai kuwa yana zuwa ciki ya watsata kamar buhun shinkafa, k’ara ta saki tare zunbura ta taso zaune zata mishi magana d’if ya rufe ta ya koma mazauninshi ya tayar, bubbuga k’ofar ta fara yi tana k’walla kiran yayi hak’uri dan Allah amma ina, dan ita tunaninta wani wurin zai kaita, shi kuma takaicin yanda ya sameta a wurin har tana bawa wani lambarta ne yake k’ara tunzura shi.

Bai kula da tsiyarta ba har suka iso gida ya paka motar, fitowa yayi ya bud’e mata yana hararanta, tayi sharkaf da zufa ga hawaye ga majina, da k’yar ta durko ta fito takalmi d’aya a hannu da wayarta dan ky d’in moto dama yana hannun Nafi, rufe boot d’in yayi yana kallonta sai wani tank’warewa take kamar tsohuwar data gaji da duniya yace “Maza yarinya tattare min wannan shegen siket d’in zakiyi ki min tsallon kwad’i a wurin nan.”

Zaro ido tayi tace “Kwa me?”

Dak’uwa ya mata yace “Kwad’i.” Belt d’in shi ya k’ok’arin zarewa yana fad’in “Ko ba zakiyi ba?”

Da sauri tace “A’a ni na isa? Zanyi wallahi.”

Cire takalmanta tayi d’aya ta aje gefe ta fara tattare siket d’in da k’yar saboda ya kamata, cikin jin haushi yace “Yanzu wannan da zaki saka shi uban wa ya kama miki? Duk kibi ki d’aure jikinki haka ki hana komai numfasawa, mtsssss.”

Ita dai ta gefen ido take kallonshi harta tattare, d’an matsawa tayi daga kusanshi ta duk’a kamar gaske zata fara, tana d’aukar takalminta sai kuwa tayi wuf da iya gudunta, kallonta yake yanda take gudun abisa gaskiyarta mazaunanta su ma na neman tsira, abun mamaki wanda ni kaina banyi zatonshi ba shine dariyar da Ammar yayi, domin kuwa duk dariya ko murmushi da yake na iya shege da da iskanci, amma wannan dariyar ta abune ya baka dariya ainin, gyara belt d’in shi kawai yayi ya sake shiga mota ya bar gidan.

➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️

An idar da sallahr isha’i kenan Alhaji ya fito daga d’akin shi zuwa falon cikin wata dakakkiyar farar shadda da taji kud’i, hula agogo da takalma duka farare ne, Hajia na zaune a kujerarta yara na ta yar hayaniyarsu amma cikin nutsuwa, inda matan kuma ke falon sama da yan mata, lieutenant ne ya shigo da alama yanzu ya dawo daga masallaci, kallonshi Alhaji yayi yace ” *Babba* kaje ka shirya ka fito yanzu zamu je wani wuri.”

Da ladabi lieutenant ya amsa da “To.”

Ciki ya shiga Hajia kuma ta kalli Alhaji tace “Ina kuma zuwa da wannan shirin?”

Cikin sigar zolaya yace “Neman aure zan je, ki tayani da addu’a wannan karan na samu.”

Wani murmushi ta saki tace “Allah na tuba ka yafe ni, macen da zata iya zama da kai a hakan nan ai sai ni.”

Juyawa yayi dan bar mata falon yana fad’in “Dama kuma ke kika mayar da ni hakan.”

Had’e fuska tayi a ranta tana fad’in “Wallahi duk da mun tsufa ko yanzu ka ce zakayi aure saina maka tijara, dan kuwa ina k’aunar ka kuma dan ni kad’ai aka halliceka.”

Bai jima sosai ba ya fito cikin shirin dogayen kaya shadda kalar maroon da hula da takalmi, k’aninsu Ammar mai shekara sha hud’u wato *Kamal* lieutenant ya kalla yace “Ka fad’awa Ummynku na fita tare da Alhaji.”

Shi fa yayi hakane tunda sun rabu da cewa zai tafi masallaci, tunda baisan ina zasu je ba da tsawon lokacin da zai d’auke su shiyasa yace a fad’a mata, amma Hajajju sai tayi mamakin abun da ganin kamar Sa’ada na son shiga hancinta da duk’unk’une ne, da kallo ta bishi har yace mata sun fita amma ko tanke, yana zuwa ya samu Alhaji na jiranshi jikin mota, shiga sukayi suka fita daga gidan sannan Alhaji yace “Gidansu yarinyar nan Zeituna zaka kaini.”

Da mamaki ya kalleshi dan shi dai bai ma san gidan ba, Alhaji ne yace “Muje zan nuna maka, na tambayi Iya ta kwatanta min.”

Ba tare daya daina mamaki ba yace “Alhaji me zamu je yi a gidansu? Wani abu ya faru ne?”

Murmushi ya masa yace “Alkairi ne zai kaimu, kuma ina fatan ba zaka watsa min k’asa a ido ba.”

D’aurewar da kanshi yayi yasa bai iya cewa komai ba sai kwatancen da Alhaji ke mishi yake bi kawai, da haka suka iso dama kuma ba nesa bane da su, sunyi sa’ar samun kawu Mamu a k’ofar gidan zaune ya gama cin abinci, shi ya d’auka ma Jano ne ya dawo har ya mik’e dan gaishe shi cikin girmamawa, amma duk da haka ganin manyan mutane ne saida ya gaisa dasu cikin mutumci da basu girmansu, har zai shiga dan d’auko musu kujeru suka ce ya isa nan ma, zaune sukayi suka sake gaisawa kafin Alhaji yace “…

16/06/2020 à 13:21 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*SANIN MASOYI*
_(sai Allah)_
*BAYA DA K’URA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

_*MASOYA NA*_

_Bismillahir rahamanir rahim_

*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`

_10_

A cikin kwana biyu su Raihan sun gama shirye shiryen tafiyarsu tare da su Ma’awa, Abbas da kanshi ya kaisu airport saida ya ga tashinsu kad’ai ya juyo ya dawo, a kwana biyun nan kuma Ma’arufa na nan ta rasa yanda zatayi hak’arta ta cimma ruwa, bata samun wata dama ta keb’ewa dashi, da safe ma sai dai su had’u a kan dinning da dare ma haka, kuma tun anan suke saida safe sannan kowa yaje ya kwanta, hakan yasa take jin haushin Sameera sosai saboda a kwana biyun nan kuma wata irin soyayya da kulawa suke kulawa junansu, wanda hakan ya samo asali ne saboda Abbas na cewa Meerah yi kaza za tace to, a wajen Harira ma hakane sam babu fuska daga gurinshi amma duk da haka bata karaya ba kwalliyarta take cab’awa, haka kuma ya karb’o sakamakon gwajin da akawa Abdul wanda ya nuna baya d’auke da wata cutar.

Yau dai Ma’arufa tayi waya da Salma kuma ta fad’a mata abinda zatayi, dan haka yau a shirye take kuma ta saka ido sosai, amma sai sauk’i ya samu saboda yamma lik’is Sameera ta fita zuwa compagninta yin wani business, kafin ta fita kuma saida ta tura yaran wajen Bilkisu dan karsu damu Ammie kafin ta fita, sam babu wanda ya tsammaci dawowarshi wannan lokacin, daga yanda yake sauri zaka san abu na gaggawa ne ya dawo dashi gidan, tunda Ma’arufa taga shigowarshi ta tafi d’akin ta da sauri dan gani tayi ba ma zata bari daren yayi ba kamar yanda Salma tace mata, tana shiga kayanta ta cire ta d’aura towel ta shafa turare sosai, wayar da suka killace domin aikin nan ta fito da ita, k’arama ce sai dai akwai d’aukar hoto rad’am ya fito ko da daga nesa ne, saisaita mata zama tayi ta yanda zata iya d’aukar komai dake kan gadon kafin ta fara sakin k’ara.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected