BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
K’arfe *03:47* na dare Ameera ta farka, madarar da take sha babu ita kusanta kuma babu kowa a tare da ita, tasowa tayi ta fito falon ma babu kowa, a cikin fridge yana aje madarar saboda ya san suna buk’ata yaran, amma sai ba tayi tunanin bud’awa ba ta d’auka, haka kuma bata tsaya nemansa ba saita tunkari k’ofa, uwarta kawai take son gani taji dad’i, dama bai rufe k’ofar ba saboda tunanin Hamna zata zo, ko da taji ta bud’e saita fita ta nufi b’angaren, amma matsalar shine k’ofar shiga falon Hajia a rufe take, jijjigawa ta shiga yi amma shiru ga kukan tsintsaye dake tsoratar da ita, sulalewa tayi ta zauna manne a jikin k’ofar, a hankali ta saki fitsarin da take ji a wurin.
Ganin dai babu motsin kowa kuma babu mai shirin zuwa saita fara rera kuka,Tsawon wannan lokaci Haka tayi shi zaune ita kad’ai tana kuka tana son yin bacci, kiraye kirayen sallah yasa mai gadi ya fito dan yin alwala, amma duk kai da kawon da yayi Allah bai nuna masa ita ba saboda akwao duhu ma.
Firgigit ta farka kamar wacce tayi mummunan mafarki, ko da ta bud’a ido juyawa tayi inda yarinyar ke kwanciya bata ganta ba, ganin lokacin sallah ma ya kusa saita ta tashi ta shiga ban d’aki tayi alwala ta dawo, har ta bud’a wajen kayanta da niyyar sake na jikinta na bacci, a hankali a hankali sai take jin kamar sautin kuka k’asa k’asa, shiru tayi tana saurarawa har dai ta fito daga d’akin, a lokacin da Ameera ta farka ta k’ara fashewa da kuka mai gadi ya ganta, matsowa yayi yana dubawa da kyau, cikin tsoron ko dai ba yarinyar bace yace “Wacece nan?”
D’aga kanta tayi ta kalleshi fuskarta duk tayi jina jina da hawaye da bacci a idonta, cike da mamaki ya sake cewa “Hajia k’arama ce? Me kike yi anan?”
Cikin kuka da maganarta bata ko fita tace tace “Wajen Ummy zani.”
Sai lokacin ya saki jikinshi ya matso sosai ya fara buga k’ofar, daidai lokacin Hamna ta fito taji ana buga k’ofar, take a wurin ta sawa ranta Ammar ya dawo da Ameera ta tashi a bacci kenan, sam mantawa tayi da riga da wandon dake jikinta, wando iya gwiwa yake na sojawa ne sai rigarshi bak’a mai k’ananan hannu amma ba sirara ba, da sauri ta shiga saukowa zata nufi k’ofar sai ga Labaran shima ya fito tare da yaranshi maza ya iza k’eyarsu gaba zuwa masallaci, karo suka ci sai Kamal da shima ya fito daga nashi d’akin daga sama, rage saurinta tayi ta kalli Labaran da yace “Ina zaki tafi kike sauri haka?”
Cikin girmamawa tace “Naji ana buga k’ofa ne.”
“Nan?” Ya fad’a yana nuna k’ofar, da “Eh.” Ta bashi amsa tana kallo ya hanzarta zuwa ya bud’e, mai gadi ya gani tare da Ameera a hannunshi, Hamna na tsinkayarsu bata bari wani cikinsu yayi magana ba ta daka a guje ta finciko Ameera ta rumgume a jikinta, kallon fuskarta take tana share mata hawayen da har sun fara bushewa, kallon mai gadi tayi tace “Ina Abbanta yake? Daga ina ka d’aukota?”
“Wallahi nima anan na ganta ita kad’ai tana kuka, tace wajenki zata tafi.”
Cike da tausayi ta kalleta tace “Abbanki ne ya kawo ki?”
Girgiza mata kai tayi hakan yasa tace “To yana ina?”
Cikin shahsek’ar kuka tace “Ban ganshi ba.”
“To ya akayi kika taho nan Ameera?” Ta fad’a cikin yanayin tashin hankali, murya k’asa k’asa tace “Ban ga Abba na ba kuma ban ganki ba, shine na taho wurinki kuma k’ofar ta k’i bud’ewa.”
Cikin d’aga murya kamar za tayi kuka tace “Tun yaushe Ameera? Kin jima anan d’in?”
Yarinya da babu hankali sai tace “Tun da daddare.”
Zaro ido tayi da matuk’ar tsoro ta sako da hawayen tausayi tace “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un, yanzu Ammar nan ya bar min ke kikayi kwana.”
Labaran ne yace “To shiga da ita ci…” Bai gama fad’a ba ya ga Hamna ta aje Ameera ta wuce da sauri ta nufi b’angaren Ammar, Kamal ne ya kalli Labaran yace “Tonton muje muyi sallah, gobarar nan ubangiji ne kawai zai iya kashe ta.”
Wucewa sukayi sallah har da mai gadi, tana zuwa da k’arfi ta bud’a k’ofar falon ta shiga, ba tsayawa komai ta tunkari k’ofar d’akin baccinshi, tana daf da kaiwa shi kuma ya bud’a ya fito zai tafi masallaci shima da doguwar riga, kamar wata zakanyar da aka cinyewa ya’yanta suna had’a ido taga shine kawai tasa k’arfinta da hannayenta ta tura shi baya da k’arfi, k’ofar d’akin ya kaiwa karo yana kallonta da mahaukacin mamakin lafiyarta.
Cikin kuka kamar an ce mata Ameera rasuwa tayi da d’aga tace “Ammar me yasa zaka min haka? Me yasa zaka bar min yarinya ta kwana a tsakar gida ita kad’ai kamar wata marar gata, me yasa baka kira ni na zo na d’auketa ba in kai ba zaka iya kai min ita ba? Haka kawai ka maidata kamar wata *marainiya*.”
Cikin rashin fahimtar inda kalamanta suka dosa ya matso kusanta yace “Wace yarinyar wai? Ameera kike nufi? Amm…”
“Amma me?” Ta fad’a da k’arfi, d’orawa tayi da “Saida na kiraka nace ka kawo min ita, ko ban kira ka ba? Kasan ba zaka iya kula da ita ba shine ka k’i kawo min ita tsabar mugunta, kuma ai kasan ba wajenka suke kwana ba, amma tsabar fitina da nema na da magana ka rik’eta wajenka.”
Sake matsowa yayi kusanta yace “Ke yi k’asa da muryarki, d’anki ne ni da zaki zauna kina min fad’a, dan fa yana asuba ne bana masifa a irin wannan lokacin.”
“To kayi mana, na ce kayi, ni ita nake nema da kai.” Duk tayi maganar ne tana turashi baya da k’arfinta, saida ta ga ya dangane da bango ta nuna shi da yatsanta mai d’auke da doguwar afaifa da bak’in lalle tace “Ya zama na k’arshe kenan da zaka k’ara k’ok’arin rabani da yarana, wannan ba samari bane da zanyi shiru idan ka shiga tsakani na dasu, akan ‘ya’yana saina dafaka da ranka kuma na shanye romon.”
Ido ya zaro tare da bud’e baki irin firgicin nan cike da shak’iyanci yace “Mayya ce ke dama? Yaushe kika fara cin naman mutane?”
Sama da k’asa ta daddala masa harara tace “Tun ranar da bak’in bakinka ya rairaye min k’iba ta.”
Juyawa tayi zata fita yace “Ki nemi abinda ya ramar dake kankana, amma ba bakina ba, kuma nasan kema kinsan ko a ina matsalar take.”
Tsayawa tayi ta juyo tace “Babban matsalata a rayuwa kai ne Ammar.”
Sake juyawa tayi zata fita abinda zata iya cewa bai tab’a faruwa ba, indai kaga jikinshi a hannunta to mugunta ce zai mata, amma sai gashi ya rik’e hannunta kuma ba da k’arfi ba, hasalima yatsunta ne ya rik’e yana mammatsa su a hankali a hankali, matsowa yayi kusanta saida ya tsaya gabanta yana kallon fuskarta, tayi shiru alamar abun ya ratsata, babu wani yanayi a tare da fuskarta na bak’in ciki ko b’acin rai, fuskarta dai kamar tana bacci yanayin nutsuwa sosai.
Yana kallon fuskarta cikin yanayin fahimta shima yace “Hamna kina son yaran nan sosai, rabaki dasu abune da ba zaki ji dad’inshi ba, amma me yasa kika k’i amince da maganar iyayenmu na son had’a aurenmu?”
Da sauri ta kafe tsakiyar idonshi da kallo, kasa d’aukewa tayi kuma ba tace komai ba, shima ba tare daya rusunar da idonsa ba duk da hakan kuwa na galabaitar dashi yace “Hamna kina da girma da mahimmanci a zuciyata fiye da tunaninki, ni mai iya mallaka miki yarana ne har abada sun zama naki, amma matsalar d’aya ita ce idan kika auri wani, ba fa lallai ya barki tare da su ba kamar yanda kike so, kuma na tabbata iyayenmu ma abinda sukayi la’akari dashi kenan suka so had’a aurenmu, amma da yake mahaukaciya ce ke lamba d’aya sai kika kawo wani mai suffar yan tsaki wai shi kike so.”