BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Yaji dad’in gaisuwar data mishi dan haka ma ya saki murmushi ya sunkuya ya d’agota ta mik’e tsaye, saida suka k’arasa bakin gado ya zauna sannan ya zaunar da ita kan cinyarshi yana kallon fuskarta, yanda take sunkuyar da kai kamar zata nitse k’asa, d’ago hab’arta yayi ya juyo da kallonta kanshi yace “Wai ke yaushe kunyar nan zata k’are ne? Ba zan iya tuna ranar da muka had’a ido dake ba fa? Ya kamata ace ance yanzu kin saba ko dan igiyar data d’aure mu wuri guda ni dake.”
Zeituna dai k’ala ba tace ba sai sunkuyar da kai da take, ba tare daya daina mata kallon nan ba yace ” Na zo duba jikinki ne fa, to ya kike ji yanzu? Ba kya jin ciwon komai?”
Da sauri tasa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta saboda tsananin kunyar data kamata, dariya yayi tare da k’amk’ame ta sosai a jikinshi yana sumbatar ta, (Harkar fa ta manya ce, nayi nan ni dai♀️).
Zeinabu na zuwa suka duba tukunya sai suka ga har dambun ya fara rusuna alamar zai d’auki dahuwa, ajiyar zuciya ta sauke tace “Ikon Allah, duk da ana cewa a daina yarda da canfi amma wani abun idan ka ganshi dole ka amince, to Allah ka gafarta mana.”
Lieutenant bai jima ba ya sake fita dan baya son Hajia ta saka masa na jiyamu, fitarshi kuma ta bawa Zeituna damar zuwa madafa aka k’arasa sauran aiki da ita, suna cikin jera kwanukan abincin Ummy ta dawo, wanka tayi ta fito lokacin har Hajia ta ci nata abincin ita kad’ai akan makeken teburin daya had’a kujera goma sha biyu, fitowar Ummy suma matan da su Hamna suka zauna suka ci na su abincin, a wurin ne Ummy ta dannawa Amar kira, bayan ya d’auka tace “Kana cikin gida ne?”
Daga b’angarensu ya amsa da “Eh Ummy, kin dawo ne?”
“Na dawo, ka jira yanzu za’a aiko miki da abinci.” Amsawa yayi da “To Ummy.”
Tana aje wayar ta kalli Kamal dake kusa da ita tace “Ka shiga madafa abincinsu na nan a kula ka kai musu.”
Soueiba ce ta kalli Kamal tace “Daga nan ka duba ka gani ko Jibril yana nan sai su ci tare.”
Da kai kawai ya mata alamar to, Zeinabu ce ta kalleta tace “Yana ciki ai, na ga shigowar motarshi kuma har yanzu tana nan, tare da Junaid ma suka shiga.”
Soueiba ce tace “Ah to shikenan, ka kai musu kawai, kace idan ma bai ishesu ba sai su zo a k’ara musu, dan yau kowa ya wuni da yunwa saboda Amna yau ta hora mu.”
Dariya suka kwashe da ita banda Zeituna da tayi shiru tsananin mamaki ya k’ara rufeta, sai yanzu ne data shigo gidan ta fara fahimtar wata b’oyayyar rayuwa da suke, kowa d’an shi kawai ya sani bai damu dana d’an uwa ba, sannan ita kuma Ummy da take da yara biyu d’ayan kawai ta damu da shi, amma Ammar dake babban d’an ta bata nuna kulawa a kanshi ba, kuma ta tabbatar yana gidan dan ya riga sauran ma zuwa gidan, hakan yasa taji ba dad’i sosai ta mik’e daga kujerar ta nufi madafa, wani kwano ta samu madaidaici mai kyau ta zuba dambun ciki sannan ta samu k’aramin shi ta zuba had’in nik’akk’en naman da petit poit sannan ta fito, kai tsaye hanyar waje ta nufa ta kuma sa’ar had’uwa da Kamal ya dawo, kwanon ta bashi tace “Kamal, ka kaiwa yah Ammar kaji.”
Kallonta yayi yace “Aunty Zeituna, har yanzu yah Ammar zaki ci gaba da kiranshi?”
Dariya tayi tace “To ya kake so na kirashi? Ai yayana ne a zahiri, ka je ka kai masa ka dawo.”
“To.” Ya fad’a yana juyawa ya koma b’angarensu, yana zuwa wata sallamar ya sake yi ya shiga, kai tsaye d’akin Ammar ya nufa har Amar na fad’in “Autan Ummy ina zaka je?”
“Wajen babban yaya.” Ya fad’a ko juyowa baiyi ba, k’wank’wasa k’ofar d’akin yayi tare da turawa ya shiga, kwance yake yana kallon sama yayi nisa a tunani, har ya tsaya gabanshi ya aje kwanon k’asa bai kalleshi ba saida yace “Yah Ammar ga abincinka nan.”
A hankali ya kalleshi ya tashi zaune, kallon kwanon yayi ya sake kallon Kamal yace “Abinci na kuma?”
“Eh.” Kamal yace ya juya da niyyar fita, sake cewa yayi “Abinci fa? Wa yace ka kawo min?”
Juyowa yayi yace “Aunty Zeituna ce, amaryar Abba.”
Bushewa yayi da dariya kamar mahaukaci sabon kamu, irin dariyar da yake yi ce yasa Kamal cewa “Yah Ammar lafiya?”
Tsayawa yayi ta kalleshi yace “Ko da nace, ni nasan inba bak’o ba babu wanda zai aiko min da abinci, to naga dai ko uwar data haifeni bata damu da ci na ba bare kuma wanda suke kewaye da ita.”
Jinjina kai yayi yace “Amaryar Abba, amma me yasa zata aiko min da abinci?” Kamal ne yace “Ni ma ban sani ba.”
Da mamaki Kamal yace “Zaka ci kenan?”
K’uri ya masa da ido yana kallo hakan yasa ya fita ya rufe mishi d’akin, yana ganin fitarshi ya shafa cikin da har kukan yunwa yake masa amma kasala ta hana shi fita ya je ya ci abinci, murmushi yayi yace “Zan ci mana Kamal, har na manta kalar d’and’anon abincin gidan mu, ina ma Ummy ce ta aikoka da abincin nan, da na ci da farin ciki da kuma karsashi ko da bana yanayin cin abincin, amma gashi matar data shigo gidan nan jiya wacce nayi mata kashedi akan uwata ita ce ta zubo abinci wai akawo min, duk da bansan manufarta na yin haka ba amma dai hakan yasa na ji kamar an kula dani ne.”
D’auko kwanon yayi ya bud’a, take yaji yawunshi sun tsinke, tashi yayi yaje ban d’aki ya wanko hanayyenshi ya fito, saida yayi bismillah tare da fad’in “A’u’zu bikalmatillahi tammat-min sharri ma kalaq.” Duk yayi hakane dan aniyarta ta koma mata wai idan ma abinda ya mata jiya ne zaisa ta fara gaggawar d’aukar mataki akan shi.
*A gurguje*
Da magribar wannan ranar aka kawo kayan Amar ma, shi ma dai kamar yanda Ammar yayi haka ya kawo, sai dai ba shine ya kawo ba, wasu daga cikin yan uwa na dangin mahaifinsu da kuma abokan lieutenant ne suka kawo, anan kuma take kafin su tafi Hajia ta shaida musu nan da kwana goma sha hud’u sati biyu kenan za ayi bikin, dan haka a shirya da kyau kafin lokacin, da haka labari ya riski kowa inda aka shiga shirya ma wannan rana.
Wani ikon Allah kuma tun daga wannan ranar kullum akayi abinci na rana da dare sai Zeituna ta fitarwa da Ammar, duk yaron daya tarbi gabanta shi take bawa yana kai mishi, lokacin da lieutenant ya fahimci haka kuma sai yace ta rabu dashi mana shi fa ba yaro bane, akan me ma zata damu da shi ne? Dariya kawai tayi tace tana yi ne saboda Allah, kuma taga shi bai damu da ya zo ya karb’a ba, Hajia ma baida habaici da cewa neman gurin zama ne babu abinda take fad’a mata, haka ma Ummy gani take wahala ce take ba kanta, indai Ammar ne wata rana ya gwasaleta, wannan shine abinda take fad’a, Ammar kuma kuma yanzu ya daina cin abincin waje inba na safe ba, ya sakankance yana cin wanda Zeituna ke aika musu, dan lokuta da dama tare da duka sauran yan uwan take aika musu musamman da dare lokacin duka sun dawo, Ummy da kanta ta shirya tare dasu Amna suka je madarunfa aka kaiwa Hadiza kayan Amna ta gani tasa albarka, data tambayi Ummy abinda za ayi ko ya rage sai tace babu komai da suke buk’ata daga wurinta, alfarma kawai ta nema na ta zo ran damu taga d’akin yarta hakan zaisa taji dad’i, a haka kuma ake ta shirye shiryen biki dan lokacin ya taho sosai.
Wajen amare ma sun gama jarabawarsu sosai aka zage ana ta gyaransu kamar hauka, dan Hajia da kanta tasa ake musu gyaran, da farko suna zuwa ne a musu, amma daya rage sati d’aya sai mai musu gyaran take zuwa gida tana musu, kuma a haka yaran zamanin suma amaren suke k’arawa kansu wani had’in wanda suka koya, Ummy ma haka ta zage tana dafa musu kaji tunda ta ga sauran sati d’aya, da haka har aka riski daren da za’a saka amare lalle.