BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Kallon Ummy yayi baki bud’e yace “Ummy biyu ne, wallahi yan biyu ne, wayyo Allahna dad’i, Amna nagode nagode kinji, Allah ya saka miki da alkairi.”
Lumshe ido Amna tayi ta kwanta luf, Ummy ce ta kalleshi tace “Ka d’auko mana kayan haihuwarta.”
“To Ummy.” Ya fad’a yana nufa k’ofa rik’e da jinjirin, kallonshi Ummy tayi tace “Ina kuma zaka je dashi a haka?”
“Oh.” Ya fad’a yana dawowa ya mik’a mata shi, aje shi tayi gefen Amna ta yanke cibiya ta fito mata da uwa, hannu tasa ta fito mata da gudan jini, kallonta tayi tace “Amna ci gaba da tausa ciki kina murzawa saboda jini ya fito.”
Ido rufe tasa hannu tana murza ciki tana danna mararta tana ji jini na zubo mata. Yana fitowa ya ga duk iyayen tsaye Zeinabu ce kawai babu, cike da shak’iyanci ya fara taka rawa yana tafa hannaye yana juyawa, takon rawar a hankali mai birgewa, a haka kuma wak’a ya dinga rerawa ta godiya ga Allah wacce shi ya k’irk’ireta yanzun nan, lieutenant ko da yaga haka yasan ta haihu sai shima ya fara tapi yana biyar wak’ar yana gyad’a kai alamar yanayi da wak’ar sun masa dad’i, Hajia ce tace “Kai ta haihu ne?”
Girgiza kafad’u ya shiga yi yana kallon fuskarta ya kwaso shoki daga k’ololuwar k’asa yayi sama da ita ya wurgata fuskar Hajia yana fad’in “Hajia ‘yan biyu ta haifa min, aradu mace da namiji ne Hajia, kai nima fa ashe jarumi ne.”
Murmushi ta masa tace “Hakane, amma duk jarumtarka mijina dai ya fika, shi uku yake haifa.”
Alhaji dake tsaye rik’e da carbi kunya yaji ta kamasa, su lieutenant da Labaran kuma dariya sukayi cike da jin kunya, shafa kumatunta yayi yace “Bari na dawo Hajia Allah yau sai kin taka rawar jin dad’i.”
Da gudu kamar yaro ya nufi hanyar b’angarensu, da sauri ya d’auko kayan ya kawowa Ummy, Ummy da kanta ta gyara yaran ta bashi ya kawo musu, yana dawowa ya samu tana dannawa Amna mararta da jini ke ta fitowa, tana kallonshi tace “Zare nake so zan mata d’inki.”
Kallon Amna yayi ya matsa kusa da ita yace “Wayyo duniyata yarana sun k’ara ki ko, sannu kinji, insha Allahu ladar ta tabbata gareki.”
Rufe idonta tayi a ranta tace “Kai da kan ka ma ka k’ara ni bare su, ai kamar uba kamar ‘ya’yansa ne.”
Da kanshi ya had’awa Ummy zaren ya bata kafin ta fito, namijin dake hannun lieutenant ya lek’a fuskarshi yana wasar masa baki yana fad’in “Kai wanene wannan? Kai yaron babanshi ne, d’an albarka ne, yaron Ammar ne wannan.”
*Allah ya kyauta.*
Soueiba ce ta kalleshi galala tace “Ammar yaron da ko ido bai bud’e ba kake ma wasa?”
Kallonta yayi yace “Ina so ya fara d’aukar sautin muryata ne kafin ta kowa.”
Tab’e baki Hajia tayi tace “Duk tsiyarka kuma sai sun sun gane uwarsu kafin kai.”
“Wannan ba matsala bane Hajia, ta cancanci haka ai, daga yanda naga ta canza d’in nan a yayin nak’udarsu na k’ara mik’o muku jinjinata.”
Kalle kalle ya shiga yi kafin yace “Wai duk ina sauran mutanen gidan.”
Husseina ce tace “Suna bacci mana, *12: 30* ce fa tayi na dare.”
Zaro ido yayi yace “Wa? Bacci a lokacin da yan biyu na suka shigo duniya, ai Qur’ani basu isa ba, duk uban daya tsaya ma mutum ma saiya tashi, bari kuga yanda zan firgita nutsuwar kowa.”
Labaran ne ya bishi da murmushi yace “Mun gode Allah da yasa ubannin gamu nan tsaye.”
Dariya lieutenant yayi ya kalleshi yace “Kar ya baka wahala mana.”
Suna kallonshi ya nufi wajen mai gadi kai tsaye ya fara bubbuga mishi k’ofa, yanda yaji buga k’ofar yasa shi fitowa da sauri da makullai a hannu yana tunanin fitar gaggawa ce, yana ganinshi ya tsaya yace “Alhaji k’arami wani ne ba lafiya? Bara a bud’e k’ofar.”
“Kai tsaya dallah.” Ya fad’a yana turashi baya, kallonshi yayi zuru da ido kafin yace ” Ina bokitin nan naka da kake wanki?”
Saida ya had’e gira tsabar mamaki yace “Bokiti? Yana nan ciki?”
“D’auko min.” Ya fad’a, shiga ciki yayi ya d’auko bokitin robar ya kawo mishi yana fad’in “Yallab’ai lafiya dai ko? Allah yasa ba laifi nayi ba.”
Kallonshi yayi yace “Idan laifi kayi kuma shine sai a bokitinka zan huce saboda tsoronka nake ji.”
Sunkuyar da kai yayi shi kuma ya juya zai tafi sai kuma ya tsaya ya juyo yace “Baka da wani mabugi haka kamar sanda ko icce?”
Shi kam mai gadi baya da dan ko shayi ko girki idan buk’atar yi ta kamashi k’aramin gas gare shi, dan haka yace “Babu yallab’ai, amma bari a samo maka.”
Takalminshi yasa da niyyar fita nema sai Ammar yaga tsumagiya aje, d’auka yayi yace “Bari wannan ma yayi.”
Juyowa yayi ya kalleshi yace “Yallab’ai da ka bari na samo maka wanda yafi wannan, ita ma ina ajiya ne saboda yara wani lokacin.”
Kallonshi yayi saida ya kawo bokitin nan gaf da kunnenshi ya tak’ark’are ya had’a tsumagiyar nan da bokiti ya shiga bubbugawa da k’arfi kamar zamanin da ake shela da baki, rintse ido yayi sosai saboda yanda k’arar ke shiga hudar kunnenshi, saida yaji yayi shiru sannan ya bud’e ido ya kalleshi, shima kallonshi yayi yace “Har gari ya waye babu mai kwana a gidan nan, baiwar Allah na can tasha fama ta haifo min yara har biyu, biyu fa.” Ya fad’a yana nuna mishi biyu da yatsunshi ya ci gaba da cewa “A lokaci d’aya, kuma kuma ku kuna baccin iya shege.”
Juyawa yayi cikin takon k’arfi kamar zai shiga filin daga ya shiga falon Hajia, saida ya tsaya tsakiyar falon ya fara bubbuga bokitin yana ihu yana fad’in “Kowa ya fito, kowa ya tashi.”
Har sama ya haura k’ofar kowane d’aki ya bubbuga yana shelar kowa ya fito, har yara masu nauyin bacci saida suka fito haka Zeinabu da Hamna take hangenshi daga sama, Kamal ne ya iya jarumtar cewa “Yah Ammar lafiya ka tashemu a bacci?”
Kallon duka yaran yayi yace “Kowa ya sauko k’asa.”
Cikin turo baki da girmama jarabarshi kowa ya sauko rai a b’ace, kamar zai basu horan yak’i haka suke jera suna kallonshi, kallonsu shima yake yace “So nake ku fita farfajiyar gida kuyi murna kuyi tsalle kuyi ihu da hauka saboda murnar samun ‘yan biyu da nayi, yan biyun ma ni duka jinsin aka had’a aka ban, dan haka ina so duk unguwar nan ta shaida anyi sabon *Ammar* da kuma k’anwarsa *Amna*.”
Yanda ya fad’a haka suka fita duk sukayi inda suka ga su Hajia, d’aga kai yayi suka had’a ido, girgiza kai tayi a ranta tace “Allah ya shiryaka Ammar.”
A zahiri kuma ce masa tayi “Saboda wannan ne ka d’aga mana hankali? Allah ya baka lafiya to.”
Sake d’aga kai yayi yace “Ki sauko kema ko kuma na sauko dake yar bak’in ciki, hassada kike min na samu ‘ya’ya biyu a lokaci d’aya.”
Wani murmushi ta masa tace “Biyu ko uku?”
Dara daran idonshi ya sake kafewa kanta da mamaki yace “…
*Alhamdulillah*
*Wallahi rashin comment yasa duk rubutun ya fice min a rain, ba zan dakatar da rubutun ba amma zan iya daina turawa ko ina, idan kun canza na samu gamsuwa zaku ga wata page gobe insha Allah ba ma sai kun tambaya ba.*
_A kafta, yawan sharhi yawan rubutu._
14/10/2020 à 00:58 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin Gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_