BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

*Safiya*…

*Alhamdulillah*

*Masoyan k’warai ina godiya, ‘yan k’asata ba zan manta da hallacinku gare ni ba.*
09/09/2020 à 17:58 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)“`

_Bismillahir rahamanir rahim_

_36_

Gaba d’aya baya jin dad’i tunda ya tashi, tunda ya ganta kusa dashi yaji baya tare da wannan zumud’in na son ya kasance da ita, tunanin abinda ya faru jiya ya tsaya masa a rai, duk da shine farko a wurinshi daya tab’a aure, amma yanda ita ce taja hankalinshi sai yanzu ne yake b’ata masa rai, ta nuna masa ita yar bariki ce, tabbas ya samu gamsuwa da ita, amma tunanin irin mazan da tayi mu’amula dasu, har yanzu yana ganin fuskar yaron nan da suka tab’a had’uwa lokacin da yaje wurinta. Har ga Allah, yau d’in nan duk yaji ta fice masa a rai, yana ji kamar ba zai iya rayuwa da wannan tunanin ba, dan zuciyarshi ba zata d’auka ba, zai kuwa iya jurar wannan matsin? Sukuku ya k’arasa shirinsa suka kammala karin kumallo wanda aka aiko musu daga cikin gida, duk da ta lura da yanayinshi ya canza amma da zai fita sai tace “Junaid ina so zan shiga cikin gidanku na gaisa da mutane, ina so nasan kowa kuma kowa ya sanni mu fahimci juna.”

Kallonta yayi a gatse, *Junaid*? Sunanshi ta kira gatsau haka? D’auke idonshi yayi daga kallonta yace “Ba damuwa, kije.”

Ficewa yayi wanda hakan ya matuk’ar b’ata mata rai, kutumar uba, ita zai cewa kije kuma ya tafiyarshi, me yasa bai ce su tafi tare ba tunda yasan ba ko ina ta sani ba? Lallai ma yaron nan a cewar ta, mik’ewa tayi ta shiga d’aki ta sake gyara shirinta ta yafa mayafi ta fito, tabbas ta ga k’ofar da taji ana cewa har da k’ofa da zata sadaka da cikin gidan, dan haka bata tsaya komai ba ta bud’a ta shigo, k’arewa gidan kallo take tana tunkarar babban falo, tsari da kyawun gidan ya birgeta sosai, ta kuma saka a ranta dole sai tayi gatsau gatsau ta hakane kawai zata iya tsallake rashin mutumcin da zata iya fuskanta, dan in tayi laushi zasu samu abun gori a kanta, shiga tayi falon da sallama tana sake kallon falon, Hajia da lokacin ta gama karyawa tana zaune, tana ganinta ta saki wata shegiyar dariya tace “Sanin wa Junaid ya auro min ya kawo cikin gida yasa ba zanyi mamakin ganinki a yanzu ba kuma anan.”

Murmushi Maryama tayi ta k’araso ciki tace “Kamar yanda nima banyi tunanin ganin mamaki a fuskar kowa ba saboda ganina.”

Cike da k’asaita Hajia tace “Wannan na d’aya daga cikin dalilan da suka na gujewa Junaid aurenki, bana son rashin kunya da fitsara a rayuwata.”

Ba tare data daina murmushi ba tace “Gashi kuma hakan har ya zama d’ab’iata ta yanda ba zan iya dainawa cikin sauk’i ba.”

Saida ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya tace “Ina fatan dai ya fad’a miki akwai doka da oda a gidan nan, kuma nice nan mai bayar da wannan doka da odar, dan haka ki iya bakinki kisan me zaki dinga fad’a min, da ban so ba da yanzu haka baka cikin gidan nan, kina can bakin titi kina neman wanda zai kwantaki ya baki na abinci.”

Kalaman sun mata zafi sosai, kuma wannan ne dama take gudu a auren Junaid, amma sai bata nuna ba tace “Bai fad’a min akwai mai bayar da doka da oda ba, watak’ila kuma bai fad’a min bane saboda yasan a inda ya d’auko ni, ina rayuwa ne cikin ‘yanci babu mai hanani bare sakani, yana da tabbacin ba zanji maganar kowa ba anan shiyasa.”

Sake had’e fuska tayi tace “Ki fad’a min meya shigo dake nan kika baro b’angaren ku? Dan ban son kai da kawowa haka kawai.”

Murmushi ta mata sosai tace “Na zo gaishe da surukata ne.”

Da yatsa ta nuna mata d’akin Zeinabu tace “Ki wuce to ki gaggauta fitowa ki koma d’akin mijinki, dan ba zan lamunci rashin hankali ba.”

Zata wuce d’akin data nuna mata ta ji tace “Su sauran amaren ko suna ina?”

Juyowa Maryama tayi zatayi magana sai kuma Hajia tace “Kai na manta fa, ashe su d’in tarbiyata ce, ba zasu tab’a yin wannan fitsarar ba.”

D’aga gira tayi tace “Har mu gani dai.” Zata sake wucewa Hajia tace “Gashi kuwa muna gani a halin yanzu, da budurwa ya aura da watak’ila yanzu sai an taimaka miki, amma kash, da yake baiji magana ta ba gashi da k’afafunki kika shigo nan cike da k’aryar rashin kunya.”

Fitowar Ummy tare da Zeituna daga madafa sun gama gyara komai yasa Maryama yin shiru, ganin kamala a fuskar Ummy kuma dama tasan ita ce uwarsu Ammar saita gaisheta da ladabi, da fara’a Ummy ta amsa da “Lafiya lau amarya, ya kwanan bak’unta kuma?”

Hajia ce ta katse da cewa “Kinga alamar bak’unta a tare da ita ne? Matar data shigo da kanta nan ba tare da ko rakiyar mijin ba, mtssss.”

Sunkuyar da kai sukayi hakan yasa Maryama kallonsu a ranta tace “Eh lallai, da alama wannan ita ce hawan jinin gidan nan, to wallahi idan ba tayi wasa ba ni zan k’asara ta kowa ma ya huta, ni ba zan d’auki wannan iskancin ba.”

Juyawa kawai tayi ta nufi d’akin Zeinabu, zata k’wank’wasa k’ofar wacce ke bud’e sai labulen d’akin da akayi ruf dashi sai kuma ta tsaya, kasa kunne tayi sosai jin muryar Inna na fad’in “Ya kamata dai ku sani duk son ku na kuga kun rufe sirrin nan wallahi ba zai rufu ba, dole wata rana gaskiya tayi halinta, munyi kuskure baya bai kamata mu ci gaba da zama cikin wannan kuskuren ba, babban laifi muka aikata da muka bari aka d’aura miki aure da ciki a jikinki, idan har baku fito kun fad’a ba kowa yasan halin da ake ciki, to fa ku sani matsalar zata farane daga lokacin da ta Allah ta kasance da colonel Hussein.”

Cike da damuwa Zeinabu tace “Inna nima sai yanzu na fara fahimtar hakan, na sani da ace a waccen lokacin muna da ilimi na addini da bamu yarda munyi aure da ciki ba, yanzu gashi shekaru sunja babu wanda yasan da al’amarin nan, ina jin kunya da tausayin Junaid idan yaji cewa an haifeshi kafin aure ne, hakan na nufin baya da gadon mahaifinshi, sannan waccen jarababbar matar bansan me zata iya yi ba idan ta sani.”

Inna ce tace “To sai me? Hajia tunda bata da wutar da zata saka ku duk hargaginta ai na banza ne, kuma karki damu da Junaid akan gadon ubanshi, tunda dai yana da aikinshi mai kyau da yake yi duk da ma bashi ya so ba, dan haka wannan ba damuwa bane.”

Shiru kawai Zeinabu tayi tana tunanin mafita, Inna ce tace “Kawai ki fad’awa colonel d’in dan kusan ta yanda zaku fad’awa wanda suka dace su sani, amma dai kuyi da hanzari dan rayuwa yanzu ba tabbas.”

Kallonta Zeinabu tayi tace “Kenan yanzu Inna kin yafe kud’in fa muke baki duk wata?”

Dariya Inna tayi tace “Na yafe kam, amma ai dole kinsan dai nauyi na yana wuyanki.”

Dogon tsaki Zeinabu tayi a zuciyarta tace “Aikin banza, kamar ba ke kika bamu shawarar yin shiru ba a waccen lokacin.”

Maryama dake tsaye bakin k’ofa tana jin haka ta juya da k’arfi ta bar wajen, bata tsaya komai ba ta koma b’angaren ta, tana shiga d’aki ta cire mayafinta ta shiga safa da marwa a tsakiyar falon, lallai ita ma ta samu makamin yak’ar mutanen gidan nan, kenan mijin data aura kafin aure aka haifeshi? To ai gwara ma ni da banyi aure da ciki ba, da wannan tunanin ta kira Iklima tace ta kawo mata Huda tare da kayanta yarinya zata dawo gidan ubanta kawai, Iklima ta so ta bari har tayi sati d’aya amma tace ta kawota kawai, ba yanda ta iya ta shirya Huda wacce da za’a koma da ita Goure ta kawo mata ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected