BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Yana fad’in haka ya juya zai bar d’akin, cak kuma ya tsaya saboda duk baya jin dad’in ganin Ummynshi na kuka saboda shi, d’an uwan shi kuma na fitar da jini a dalilinshi, juyowa yayi ya kalli Amar dake shirin bubbuga k’ofar d’akin, sake d’auke kai yayi kuma wata zuciyar na fad’a mishi ai sai ya d’auka ka damu da shi ne, a hankali ya lumshe ido ya sauke numfashi a zuciyarshi yace “Ka damu da shi mana Ammar, ku fa ko a cikin ciki tare kuka rayu, ka d’auka kai da shi kamar kuna rayuwa ne da rai d’aya.”
Bud’a ido yayi ya sake kallon Amar wanda shi ma yake so ya ga sun shirya ko dan mahaifiyarsu ta ji dad’i, kamar baya son maganar haka ya motsa bakinshi yace “Muje na wanke maka ciwonka.”
Da sauri ya k’araso kusanshi ya rumgumeshi dan sam bai d’auka Ammar zai fara mishi magana ba, sosai yake ta k’ara cakume shi saboda k’auna, amma me Ammar zaiyi sai kawai ya raba kanshi da shi ya had’e rai yace “Miye haka malam sai ka b’ata min kaya da jini, muje ni dallah.”
Da k’arfi ya juya ya fita Amar ya bi bayan shi yana girgiza kai, lallai a duniyar nan in har shi ya kasa fahimtar d’an uwanshi to babu mahalukin da zai iya fahimtarshi bayan wanda ya halluce shi, Husseina da Soueba da dariya suka bisu har Husseina na fad’in “Kin gani ko Zeinabu, shiyasa shiga fad’an yara ke da kunya wallahi, dan Allah ki daina damuwa da rayuwarsu, mu yarda cewa haka Allah ya hallici Ammar.”
Tab’e baki tayi tace “Hum! Ni bana so na ji kuna cewa wai yara, yaran nan fa ba dan dogon karatu da sukayi ba wallahi da yanzu sun aje mana jikoki bibbiyu ko sama da haka.”
Dariya Zeinabu tayi tace “Gashi kema kin fad’a kince yara.”
Shigowar Junaid cikin sabon shiri yasa suka kalleshi a tare, shima dai fuskar nan a had’e take dan ranshi ya b’ace sosai, Jamil ya kalla wanda ke zaune yana latsa wayarshi yace “Kai in za ka je ka taso mu tafi.”
Mik’ewa ya yi yace “Mu tafi kawai.”
“Ina kuma zaku je?” Cewar Husseina, a tak’aice Jamil yace “Gidan roumji.”
Zeinabu ce tace “Inda ubanninsu suka tafi zasu je, amma babu wanda zai iya fad’a mana dalilin zuwa.”
A motar Junaid suka d’auki hanya ba ko waiwaiye saboda su isa da wuri, Ammar ma wani d’aki suka shiga wanda ya ware yake zuba duk wasu kaya da suka shafi na jinya, sannan har magunguna ke akwai da kayan aiki masu mahimmanci wanda babu su a ma k’asar baki d’aya, hakan yasa baya wasa wajen kula da su, zaune Amar yayi kan gado Ammar yasa k’aramin almakashi da k’ada da yan ruwan kashe ciwo yana goge masa, babu mai kallon idon wani bare magana, saida ya gama ya duba inda ke buk’atar a rufe yasa k’aramin bandeji ya rufe mishi, ba tare daya kalleshi a yace “Kana jin jiri?”
Saida ya d’an dafe kai yace “Eh, dan da k’yar ma na kawo kaina nan, na so na ce ka goye ni amma kuma…”
Kallonshi yayi yace “Amma kuma me?”
“Kana hushi da k’aninka, d’an uwanka, shak’ik’inka, sannan abokin rayuwarka.” Duk yayi maganar ne cikin marairaicewa, k’ala bai ce masa ba sai ma wasu kwalaye dayake fito da su yana son d’auko wani magani, ya sha wahala kafin ya d’auko ya bud’e ya d’auki wanda yake buk’ata ya mayar da sauran, fitowa yayi daga d’akin jim kad’an ya dawo, ruwa ya bashi a roba tare da maganin yasha, d’aya maganin kuma ya sa a cikin kofi da ruwa, saida ya gama tafasa ya mik’a mishi ya shanye ya aje kofin, ba tare daya kalli fuskarshi ba yace “Ka kwanta kan gadon nan.”
Ganin ya juya zai fita yasa Amar cewa “Har zuwa wane lokaci?”
Ba tare daya juyo ba yace “Har a busa k’aho.”
Murmushi kawai Amar yayi shi kuma ya fice, yana fita kuma motar shi ya fad’a ya tayar, mai gadi na bud’e k’ofa ya suri motar yayi waje, hanya ya d’auka shima kamar zai tashi sama, shi ma dai kamar su Junaid hanyar gidan roumji ya nufa, sai dai duk gudunshi bai iya riskar su Junaid ba dan sun rigashi d’aukar hanya kuma suma gudu suke sosai.
*K’arfe* 06:20 na yamma Amar ya fito cikin shiri ya samu Ummy ya mata sallama yace zai tafi shima k’auye saboda kar ran Abba ya b’ace, cike da damuwa tace “Amar kayi hak’uri mana zuwa gobe sai mu tafi tare, tunda kaga ba lafiya ne da kai ba.”
Dariyar gefen labb’a yayi yace “Haba Ummy lafiya ta lau fa, ki bari naje kawai kar Abba ya ga kamar bamu ji maganar sa bane, kuma kinga dukansu fa ina kyautata zaton can suka tafi, kinga gwara nima na hanzarta na tafi ko da ana sallah magriba ne saina isa.”
Cikin sanyi tace “Shikenan Amar, Allah ya tsare ka ya kare gabanka da bayanka.”
Murmushi yayi sosai yace “Ameen Ummy, sai mun dawo.”
“A dawo lafiya.” Ta fad’a tana binshi da kallo harya fita.
Yana fita su Hamna na shigowa da motonsu dan saida suka kai d’inki sannan suka dawo gida, haka ma ba jimawa Umaima ta shigo gidan tare da drebanta, sai Jamila da ta shigo gaf da magrib daga école.
*Gidan roumji*
Rana ta fad’i sosai su Junaid suka iso, tunda suka fito daga mota lieutenant da colonel ke kallonsu da mamaki, k’arasowa sukayi cikin mutane suka gaishesu da girmamawa tare da musu ta’aziya, sun shiga cikin gidan dan yiwa na cikin gida suma sai ga motar boss ta karyo kwana, da k’arfi ya ci burki ya kashe motar ya fito makulli da waya a hanu, ga kyau ga kyan tsari da hallita sai dai a wurina babu kyan hali, da k’akk’arfar tafiyar nan tashi ya k’araso yana sallama amma fa wanda yayi sa’a ne kad’ai ke ya ji sallamar dan kamar bai so yayi ba, saida yayi zaune ya tank’washe k’afafun shi kafin ya fara bawa na kusa da shi hannu, colonel kam daya tsura mishi ido a ranshi cewa yayi “Lallai yaro na, wannan da ace kai général ne na soja da anshiga uku, ko mu dake iyayanka dai saida muka gaishe da mutane kafin muka zauna saboda wurin mutuwa ne, amma kai sai bayan ka zauna kake gaishe da wanda ke kusa da kai, humm.”
Lieutenant kuma haushin Ammar ne d’in ya kusa kashe shi shiyasa ma ya d’auke kallonshi daga kan Ammar d’in dan kar zuciya ta kwashe shi ya mareshi, yana gama tashi ta’aziyar ya fara danna waya, da sauri Labaran ya kalleshi yace “Ammar ka shiga ciki mana ku gaisa da matan.”
Kallonshi yayi lokaci d’aya kuma ya mayar da kallonshi kan wayar, yana kallon wayar tashi ya mik’e yasa takalminshi ya nufi cikin gidan a ranshi yana fad’in “Yanzu mutum na shiga zasu saka maka ido suna kallo, kowace burinta ka mata magana ta ji dad’i, mtssss, shiyasa na tsani shiga irin taron nan.”
*Ikon Allah sai kallo, to Ammar me ka d’auki matan? Sai kace wasu tsofaffin…*
Yana kallonsu su Junaid suma suna kallonshi haka kowa ya gama ya fito, suna zuwa kuma wasu har sun nufi masallaci wasu kuma na alwala, suma alwala sukayi suka nufi masallacin, tare sukayi sallah suka fito, fitowar lieutenant da colonel yayi daidai da shigowar Amar cikin kwanar, lieutenant a ranshi yace “Wato yaran nan sun raina mutane ko? Amma laifin duk na waccen babban kwabon ne.”
Tsaye yayi hakan yasa colonel ma tsayawa, su Junaid da Ammar na fitowa lieutenant yace su zo, Amar na ganinsu saboda ya hasko fitilar motarshi ya tsaya wajensu ya fito, cikin girmamawa yace “Abba ina wuninku, har kunyi sallah ko? Bara nima na yi alwala.”
Zai wuce lieutenant ya dawo da shi baya ya kallesu dukansu yace “Wato da na ce ku taho gaba d’aya shine kowa yayi gaban kanshi, yanzu ribar me kuka ci da kuka nunawa mutane ku kanku ba had’e yake ba?”