BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Bayan tafiyar su da kamar minti ashiri *Bilkisu* ta shigo gidan tare da *Imranatu* dake d’auke da yaronta, kamar dai yanda suka saba kullum yanzu ma da sallama suka shigo Sameera ta amsa musu, kai tsaye Bilkisu kitchen ta nufa tana fad’in “Matar Abbas nasan dai ba kya rasa abin dad’i a gidanki, dan haka bara na samo abin tab’awa.”
Imranatu ce dake shirin zama ta aje yaronta tace “Ke dai wallahi anyi acici, ke ba kya da aiki sai ki kai bakinki.”
Tana kusa da shiga ta juyo tace “Lafiya ce ta kawo haka, da babu lafiya sai kun dinga lallab’a ta akan na ci.”
Dariya Sameera tayi tace “Gaskiya ta fad’a kuma, amma kuma abin mamakin bata tashi ciye-ciyenta sai ta zo nan gidan, bansan me ya sa ba?”
Imranatu ce tace “Baki ji tace ba kya rasa kayan dad’i ba, ai da wannan ne kika rabamu da mazajenmu ta yanda basa iya cin abinci idan ba nan ba.”
Cike da murmushi tace “Kuma na samu kan mijina ba, kuma ai idan kuka so zaku iya rik’e su gidanku du dinga cin abinci.”
Hannu ta mik’awa yaron daya fara zagaya tsakiyar falon da rarrafe tace “Oya *Muhsin*, come on beby.”
Juyowa yayi cike da murna ya wangale baki ya taho da sauri, d’aukar shi tayi ta aza saman cinyarta ta ci gaba da hira da Imranatu, sai lokacin Bilkisu ta fito da k’aramin plate a hannunta d’aya hannun kuma da inibi tana sha, kamar jiran zamanta suke sai kuwa sallamar yara wasu da gudu wasu kuma a nutse, kasancewar yaran Imranatu dana Bilkisu duka tare suke karatu da yaran Sameera yasa gidan ya gauraye da hayaniya lokaci d’aya, gaishe da iyayen sukayi inda Raihan da kuma babbar ‘yar Bilkisu *Fadila* da kuma ‘yar Imranatu *Ma’awa* kasancewarsu yan wari ne yasa suka zaune akan kujerun suka fara cirewa k’annan su uniform, sai Abdul wanda har yanzu yake zuwa islamiyyar kafin hutunshi ya k’are, kallonshi sameera tayi da yayi zaune a kujera tace “Son an gaji ko? Ya karatun?”
Cike da nuna kasala yace “Ammie karatu yayi zafi kam.”
A hankali cikin nutsuwa Raihan ta kalleshi inda Ma’awa ta amsa mishi da “Wallahi yah Abdul kai dai anyi rago, wai Ammie fa saboda yau ajinsu malaminsu bai zo ba shi aka wakilta a matsayin malamin shi ya sa yake fad’in haka.”
Kallonta yayi yace “Au, ke kin d’auka koyarwar sauk’i gareta? To gobe ki jaraba koyarwar ki gani.”
Bilkisu ce tace “Wannan ai ba zata iya ba, surutu zatayi ko karatu?”
Turo baki tayi cikin shagwab’a tace “Mama.” Kallonta tayi tace “K’arya na fad’a kenan?”
Fadila da ke kallonsu kallon Abdul tayi cike da birgewa, cikin taushin murya tace “Yah Abdul ko zamu maka tausa ne?”
Murmushin gefen labb’a ya mata yace “Nagode k’anwata, ba sai kin wahala ba.”
Cike da nutsuwa da sanyin jiki Raihan ta mik’e da kayan su *Diya’u* a hannu ta kalli Sameera tace “Ammie an gama abinci? Danni yunwa nake ji.”
Murmushi Sameera tayi tace “Kowane tsuntsu kukan gidansu yake, kowa da abinda ya dame shi, to kije ki watsa masu ruwa sai ku sauko ku ci abinci.”
Kama hannun Diya’u tayi tace “To Ammie kinsan fa yaron nan naki da iyayin tsiya wallahi kullum shi ke bani wahala wajen shirya shi.”
Diya’u ne ya fizge hannu yace “To Ammie ni nace bana so ko zan dinga yi wa kaina wankan, ai yanzu na iya amma sai ace wata ce zata min.”
Da kallo Sameera ta bishi kafin ta girgiza kai tace “Ki rabu da shi kawai tunda ya girma zai iya da kanshi.”
Ba zato ba tsammani sukaji Ameer ya fashe da kuka, Sameera na waigawa taga shi da Khlifa ne, shiru tayi sai Raihan ce ta isa garesu ta shiga tsakani ta tambayi meya faru, Ameer ne ya fara fad’in abinda ya faru inda Khalifa yace “Ammie wato dan yana mai sunan Baba ne na daka shiyasa kikayi shiru.”
Abdul ne ya kama hannun Khalifa yana fad’in “In banda abinka bros ai dukanku kun sanya mana uwa a tsakiya ne, kai Abban ta ne (mahaifin Abbas) shima kuma Ameer abban ta ne (mahaifinta), to yanzu a fad’an nan wa kake so ta shigarwa?”
Cike da wayo yaron yace “Ni mana, tunda ni surukine, kaga akwai kunya tsakaninmu.”
Zasu wuce ne ta gaban Sameera ta daki mazaunanshi tace “Ya dai yau naga *aku na* ba karsashi haka?”
Kallonta yayi ya turo baki yace “Ammie kema parrot zaki kirani dashi kamar yanda tsofaffin can suke fad’a.”
Janyo shi tayi ta rumgume a k’irjin ta tace “Ayya! Sorry Dady na, ba haka nake nufi ba, na ga dai ka shigo ba magana ne.”
*Raudat* ce ta fashe da dariya tace “Ammie yunwa yake ji fa shiyasa.”
Hararan Raudat tayi tace “Ba fa nasan sharri kinji, Abba na k’arko ne da shi yunwa ba zata sa shi ya zama rago haka ba.”
A kasalance ya kalli Sameera ya shafa cikinshi yace “Ammie yanzu dai bara na haura sama na sauko, idan na ci abinci zaki sha labari.”
Bushewa akayi da dariya sai Raihan da ita dai murmushi ne nata dan sam yarinyar bata da hayaniya kuma bata son hargagi a rayuwarta, komai cikin nutsuwa da sanyi take yin shi.
Sama suka nufa haka ma Abdul da Jabir, Imranatu ce ta fito da makullin gida ta bawa Ma’awa tace “Kije ku canza kaya ku ci abinci, ki kula da kyau kar a hargitsa min lissafin gida bayan na gama gyara komai.”
Sameera ce ta kalli yaran dake fita ta kalli su Imranatu tace “Jiya munyi magana da Abban Raihan akan maganar Abdul da Raihan d’in, yace yana tunanin yi musu baiko idan mun dawo daga bikin *Arfat* (yar kawu *Bakura* yaya ga iyayensu Sameera da Abbas), yace idan so samu ne yana so a d’aura musu aure saiya tafi da matarshi idan hutunshi ya k’ar.”
Bilkisu ce tace “Kuma hakan ba wata matsala? Ni har yanzu gani nake Raihan yarinya ce wallahi.”
Sameera ce tace “Ba wata matsala yar uwa, tunda dai ta balaga ta kai matakin da zata iya d’aukar namiji ai shikenan, zamu kiratada yarinya ne idan bata zama mace ba, amma kinga Raihan bana da shakku a kanta, na yarda da ita ta yanda zan iya kaita gidan mai mace biyu ma saboda nasan na bata horon da zata iya zama da kowa.”
Bilkisu ce tace “Kuma gaskiya kika fad’a, to amma ya waccen maganar?”
Saida Sameera ta sake kallon yaran dake ta ficewa har yanzu sai Fadila data rage ita ma tana shirin fita tace “Maganar gwajin jinin da za’a mishi wannan ba matsala bane, tun farko ma yallab’ai ya b’ata lokaci ne saboda ganin rashin dacewar hakan.”
Imranatu ce tace “Banga laifinshi ba gaskiya, haka kuma banga laifin su Ammie ba, amma haka zai daure yasan abunyi dan lokaci k’uracewa yake, yanzu ana fara maganar zasu ce ina sakamakon yake, amma kinga idan aka tabbatar da lafiyarshi ai mu kan mu hankalinmu a kwance yake, tunda wannan cutar ta *HIV* ana d’aukar ta, kuma akan iya haihuwar yaro da ita ma idan ba Allah ne ya kareshi ba.”
Bilkisu ce tace “Oh Allah ka nuna mana wannan rana, ranar da alk’awarin nan zai cika na auren Raihan da Abdul.”
Murmushi Imranatu tayi tace “Ameen ya Allah, Allah yasa muna cikin masu rai da lafiya.”
Cak Fadila ta tsaya daga shirin fitar da take daga d’akin, sakin jakar hannunta tayi ta fad’i k’asa saboda jin wani abu ya daki zuciyarta da k’arfin gaske, kasa motsawa tayi daga wajen kamar wacce aka d’aure, take kuma hawaye suka cika mata ido har suna zarya a kumatunta, muryar Bilkisu ce ta katseta da cewa “Wai tsayuwar me kika wa mutane anan kuma? Kinsan dai *Farisa* (k’anwar ta) ba zata iya bud’e gidan ba ko.”
Rintse ido tayi wasu hawaye masu zafi suka sake antayo mata, a hankali ta bud’e tare da had’e wani k’ululun abu da taji ya tokare mata mak’oshi, sunkuyawa tayi ta d’auki jakarta ta wuce ba tare da tasan ina take saka k’afar ta ba, tabbas yarinya ce ita kuma mai k’ananan shekar, sai dai tasan tana matuk’ar jin Abdul a zuciyarta fiye da yanda take jin komai, tana ji a duniya inhar za ta yi aure to Abdul ne zata aura, ta yarda wannan so d’in da suke jin ana labarinshi ya kamata, ta kuma tabbatar a yau d’in nan taji wani tafasashen kishi ya taso mata akanshi, da haka suka isa nasu gidajen wanda dama had’e suke waje d’aya, kamar yanda iyayen suka d’ora su akan turbar kula da k’annan su yanzu ma haka ce ta kasance, duka yan matan uku kowace ta taimakawa yan uwanta k’anana wajen yin wanka da canza kaya, saidai Fadila bata tare da walwala sam, haka ta shirya musu sahu sukayi sallah tana wannan halin, dan ko dinning ma da suka zauna cin abinci ita bata ci ba, ta dai zauna saboda kar ta gusa yaran suyi wata b’annar, saida suka gama taga sun mik’e zasu fita tasan ina kuma zasu je, saida ta je har k’ofar gidan taga shigarsu gidan kawun nasu (Abbas) kafin ta rufe gidan ta haura sama izuwa d’akin ta, tana shiga ta fad’a kan gado ta fashe da kuka dan shine kad’ai taji tana buk’atar tayi, ita kanta bata san ya akayi ba kuma yaushe ta fara son Abdul, ta dai san kawai yana birgeta tun farko har lokacin da take jin wasu abubuwa a game da shi d’in.