BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cike da girmamawa tace ” Lafiya k’alau Baa, na zo ganinku ne dama.”

“Amma a safiyar nan? Ina mijin naki yake?”

“Baa ai tare muke da shi ma ya wuce kasuwa, yace na zauna zuwa yamma saina koma.”

Fita yayi ita kuma ta shiga ciki, nan a mahaifiyarta ta samu sai dai bata fad’a ata meya kawota ba, dan tasan ba lallai ta yarda da abinda ya kawotan ba, duk da tana goya mata baya amma wannan karan tasan zasu iya samun matsala, dan haka taja baki tayi shiru amma ta saka ido kowane lungu da sak’o na gidan da tasan mahaifiyarta na ajiya, kusan wuni tayi a gidan kafin tayi nasarar ganin k’ullin maganin da suka je suka amso wajen wani mai maganin gargajiya na zubar da ciki, d’auka tayi ba jimawa kuma tace ta tafi gida, tana zuwa bata tsaya komai ba ta jik’a maganin kamar yanda sukayi waccen lokacin tasha, baifi awa d’aya ba cikinta ya fara matsanancin ciwo, lokaci d’aya ta fita hayyacinta kamar ba ita ba, ana haka kuma jini ya biyo baya ya fara mata zuba, Suley ne ya shigo da sallama amma jin ihunta yasa ya hanzarta lek’awa d’akin nata, k’arasawa yayi yana tambayarta lafiya, amma ta kasa magana sai matsar ciki take, tunawa da yayi yanayin daya ganta waccen ranar da kuma tunawa da yayi tana da ciki, ranar farko da ranshi ya b’ace fiye da kima a kan Zeeya wanda har yasa shi zabgeta da mari duk da halin da take ciki, kamar zaiyi kuka yace “Yanzu Zeeya’atu cikin nawa ne zaki zubar? Cikin da muka samu ta hanyar sunna?”

Shiru yayi yana tattara nutsuwarshi kafin ya juyo ya kalleta yace “Insha Allahu indai wannan cikin na halak ne wallahi babu abinda zai same shi, ba zai zube ba Zeeya’atu saiya fito duniyako ba kya so.”

Hak’ik’a a duniya akwai bayin da Allah ke musu baiwa ta hanyoyi daban daban, Zeeya’atu kam tasha wahala a banza dan kuwa cikin nan bai zube ba, zan iya kiran haka da dama Allah ya rubuta cikin nan zai rayu kuma zai fito ya taka k’asa, ko kuma na ce Suley bawan Allah ne wanda Allah ya kub’utar da rantsuwarshi saboda kar kaffara ta hau kanshi, (duk hakan mai yiwa ne a wajen ubangiji), saida akayi tafiya mai nisa aka kaita babban asibiti, jini aka k’ara mata tare da cewa a kiyaye gaba, daga haka kuma ta fara rainon cikin, sai kuma sabbin rashin mutumcin data fito da su kala kala, amma sai Suley ya sake banza da ita yana shanyewa kamar yanda ya shanye na baya.

Yau ma kamar kullum daga d’akin shi ya fito cikin shirin fita, ya rufe k’ofa ya juyo kenan kamar saukar ruwan sama sai ko yaji ruwa a jikinshi, saida numfashinshi ya sauke na wucen gadi dan sosai ruwan suka dira a fuskarshi, kusan minti biyu yayi a haka kafin ya bud’e ido ya sauke akan Zeeya dake gabanshi da robar wanke-wanke ita ma tana kallonshi, a hankali ya fara kallon jikinshi ba wai jik’ewa kad’ai kayanshi sukayi ba harda datti na abinci duka, sake kallonta yayi wata zuciya na fad’a mishi yi mata shegen duka gobe ba zata sake ba, amma yana kai kallonshi kan tulelen cikinta da yanzu yake wata na bakwai sai kawai yaji ya k’ak’aro wani murmushin da ganin kasan na bak’in ciki ne, girgiza kai yayi yace ” Ke ba shed’an bace Zeeya, dan haka baki fi k’arfin addu’a ba, duk da nasan komai a kanki wanda ba kya tunanin na sani, amma ina miki fatan shiriya saboda ina so na zauna dake cikin aminci ko dan hallacin da mahaifinki ya min a rayuwa, dan haka kije Allah ya shiryeki shirin addinin musulunci, Allah ya ganar dake gaskiya.”

Cikin sanyin jiki ya cire rigarshi ya shanyata a zanar data shiga tsakanin filin gidan da k’ofar shigowa, d’aki ya koma ya sake kaya ya fito ita kuma ta ci gaba da kai da kawonta , saida taga harya kusa kaiwa k’ofa tace “Ni idan ka fita ka siyo min masara ina so zan dafa.”

Juyowa yayi ya kalleta yace “To, zan siyo miki.”

To fa da irin wannan wulak’ancin suke zaune, duk da dai an samu canji ta b’angaren zuciyar Zeeya, amma a halinta kam babu abinda ya sauya, *kwana tashi* a haka har Allah ya sauki Zeeya lafiya, ta haihu kuma haihuwa ta ban mamaki a waccen lokacin, domin kuwa *’yan uku* haka ta haifesu kuma duka maza, ba mutane a kad’ai har gwamnati saida ta shiga lamarin yaran nan ta hanyar basu kyauta da kuma iyayensu, yara sun zo da arzik’i dayawa, dan bayan kyautar da gwamnati ta musu har sarkin garin agadez mai zamani a wannan lokacin saida ya musu goma ta arzik’i, masha Allahu yaea sun ci sunan *Hassan*, *Hussein*, da kuma *Harouna* (wanda suke kiranshi da *Gambo*), duk abubuwan da Zeeya tayi a baya Suley ya manta da su ya kuma mata uzuri, gashi tunda ta haihu abubuwa sunyi sauk’i saboda kakarta da kuma k’anwar ta *Fatime* suke zaune a gidan tare da ita, Fatime yarinya ce mai nutsuwa da kunya, dan ko ido bata had’awa da Suley bare wasa ya shiga tsakaninsu, har tayi arba’in suna tare da ita saboda rainon yaya uku da wahala sosai, ganin idon mutane yasa Zeeya ziyartar d’akin Suley idan dare yayi, yanzu kam sai ladabi da take mishi idan gaban mutane ne amma bayan idonsu kuma halin take siyarwa, a haka wata rana ta shiga d’akin na shi ya nemi hakk’in shi wurinta amma ta zazzaga masa bala’i son ranta, har da cewa ba zata yarda wani abu ya sake shiga tsakaninsu ba bare harta sake haihuwa dashi, murmushi ya mata yace “Kuma gashi kam an fad’a mana a tarihin gidanmu muna da baiwar haihuwar ‘yan bibbiyu, sai gashi ke kin fara da uku abun birgewa, mahaifina ma yana da Husseini, sannan k’annai na ma yan biyu ne.”

Rana ta farko data fara sanin yana da yan uwa, amma bata nuna wani damuwa ba, zaune yayi a lokacin sosai yana kallonta yace “Zeeya’atu, a k’alla yanzu muna da shekara d’aya da rabi da aure, a wannan lokacin zan iya cewa ni dake bamuyi farin ciki ba, Zeeya kinyi min abubuwa da dama a gidan nan daya kamata ace na d’auki mataki akan haka, amma ban d’auka ba saboda mahaifinki ya min komai a rayuwa, amma daga ranar da kika haifo min yaran nan, na kallesu da idona na kuma tuna wahalar da kika sha wajen haihuwarsu, sai naji kin samu wani girma da matsayi a zuciyata, Zeeya’atu duk da kin k’untata min a rayuwa amma sai naji a duk duniyar nan babu mai so na da k’aunata sama dake, zee’ayatu matsololin rayuwa da muka shiga ne harya jefoni garinku, banda kowa sai yan uwa na mata biyu, wanda har yanzu d’aya daga ciki bansan ina take ba, amma sai gashi lokaci d’aya kin haifo min magada yara maza har uku…”

Rawarda muryarshi takeyi ne yasa yayi shiru ya duk’ar da kanshi, hawaye ne suka dinga zarya a fuskarshi, hakan ne yasa Zeeya jin wani abu a zuciyarta da bata tab’a ji a game dashi ba sai yau, ji take kamar ta tashi ta rarrasheshi amma kuma tana jin ba girmanta bane, saida ya gaji dan kanshi ya share hawayenshiya d’ago ya ci gaba da cewa “Tabbas kyautar daga Allah take, amma kema kinyi k’ok’ari Zeeya, ina godiya sosai ga Allah daya bani su, sannan kema ina gode miki, Allah ya saka miki da alkairinsa, Allah ya baki lafiyar da zaki shayar dasu cikin k’oshin lafiya.”

Hak’ik’a maganganunshi Sun huda zuciyarta sosai ta yanda ta kasa ko motsin kirki harya fita daga d’akin, haka aka ci gaba da tafiya duk da Zeeya na jin soyayyar mijin nata amma babu abinda ta rage a game da rashin mutumci, a haka yara sukayi wata uku da haihuwa, zuwa lokacin kuma kakarta ta koma sai Fatime ke tayata kula da yaran, ana haka Suley ya shirya sake komawa ganin iyalinshi, ya so tafiya tare da Zeeya dan taga mahaifarshi ko ya tsira daga gorin da take masa, amma sai Zeeya tace ai babu inda zataje tunda babu wanda ta sani, haka yayi ban kwana dasu ya kuma bar musu duk abin buk’ata sannan ya kama hanya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected