BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Husseina dake ta doka uban murmushi ce ta amsa mishi da “Barka Ammar.”
Hajia ya kalla wacce bata da niyyar magana har yanzu, a ranshi yake fad’in “Wannan indai ba shanye Alhaji kikayi ba me zaisa gashi zaune amma ke ce mai zartar da hukunci, Allah ya sawak’e miki.”
Ganin har yanzu shiru yasa ya kalli mutanen d’akin “Idan an gama karatun saimu rufe da salatin annabi ko?”
Su Amar dake kusa dashi duk rik’e dariyarsu sukayi, hakan ya hassala Hajia ta mik’e tsaye da fad’in “Kaiiiii.”
Yana jin haka saiya jingina a kujera ya d’ora hannunshi a matangalin kujera yana shafar k’ulun hallitar dake mak’ogwaronshi wanda bak’in gashi mai silb’i ya rufe shi, kallon yan k’asa tayi dan sunfi dama dama tace “Daga ina kuke?”
Shiru ne ya d’an ratsa wurin yayin da Junaid ke ganin ba zai yarda a d’ora musu laifi ba, dan haka ya d’ago ya kalleta yace “Daga Goure.”
Yatsina fuska tayi ta kallesu da kyau tace “Me kuka je yi a Goure? Wa ma ya aike ku?”
Junaid dake jin wani sanyi na ratsa zuciyarsa babu fargaba yace “Munje sulhunta tsakanin Maryama ne da iyayenta, sannan na gabatar da kaina a matsayin mai son aurenta, kuma sun amince.”
“Wacece hakanan kuma?” Hajia ta tambaya cike da rainin wayo, shiru ya d’anyi dan haka ta kalli Zeinabu dake kallon Junaid da mamaki tace “Ke kinsan wacece hakanan?”
Cike da ladabi tace “Umma ita ce yarinyar da yace yana…”
Bata bari ta k’arasa ba tace “Ku ce min karuwa, wai karuwa kake nufi? Neman aurenta kaje kenan ko me?”
Shiru dukansu sukayi, cikin taushin murya tace “Shalele, har da kai da nake ganin kamar kana da hankali? Ya zaka biye musu wajen yin wannan d’anyan aikin? Halan wani ne ya tilastaka?”
Ta fad’i hakane tana kallon Ammar da shima yana jin haka ya kalleta, dan yasan shi take nufi, d’auke idonshi yayi dan haka Amar yace “Babu wanda ya tilasta ni, kawai naga yan uwana zasu tafi ne ni kuma na tafi tare da su.”
D’aga kai tayi sama cikin gadara tace “Hakan na nufin kenan kun girma? Kun isa ku yanke hukuncin daya shafi rayuwarku ba tare da sanin kowa ba, hakan na nufin zaku iya ji da al’amari komai girmanshi idan ya taso muku ba tare da shawarar ko da iyayenku ba, to da kyau, amma ku saurare ni kuji.”
Fuskantarsu tayi da kyau tace “A gidan nan ba ayi ba ba kuma za ayi wanda zai taka min doka ba ya kwana lafiya, matuk’ar ina raye banga wanda ya isa a gidan ya dinga juya rayuwarshi yanda yake so ba, dan haka tunda kun nuna min zaku ja dani, ni kuma zan dakatar da al’amarin yanzun nan.”
Juyawa tayi ta koma inda take ta zauna ta d’ora gwiwoyin hannunta a saman cinyarta kafin tace “Hutun makaranta da za’a bayar na kwana goma nan da sati uku, ku shirya mishi da kyau, dan aurenku za ayi.”
Da sauri suka d’ago suka kalleta inda Ammar ya dakatar da shafar gemun da take yana mata kallon mai bisa ruwa, jinjina kai tayi da yake nuna tabbas babu fashi tare da d’orawa da ” *Shalele* zaka auri ‘yar uwarka *Umaima*, *Junaid* zaka auri ‘yar uwarka *Hamna*, kai uban sarkin marasa kunya zan had’a ka da wacce baka isa kace ta maka laifi ba bare harka zalinceta ( *Ammar*), za’a d’aura aurenka da *Amna*.”
Juyawa tayi ta kalli Jamila sannan ta kalli Jibril, ita dai badan tana so ba zata had’a tsatsonta dana Husseina, amma idan ba tayi ba yanzu tsohon na zai kawo mata cikas a lamarinta, dan haka tace “Kai kuma *Jibril* zaka auri Jamila, wannan shine hukunci na, da wani mai ja.”
Ta fad’a tana kallon iyayen duka, amma cikinsu sai kowa ya girgiza kai harda arhar murmushi da suke mata ana fad’in ai duk gida ne dan haka abun farin ciki ne, da murmushin k’asaita tace “Ku tashi ku bani wuri.”
Mik’ewa sukayi kamar babu lakka a jikinsu, amma Ammar ko niyyar tashi ma baiyi ba, sun fara tafiya tace “Shalele.”
Juyowa yayi tace “Idan kayi wanka ka ci abinci ka same ni d’aki na.”
“To.” Kawai ya fad’a suka bar falon, kallon Ammar tayi tace “Ko saina tasheka ne kai kuma?”
Saida ya d’an harareta na wucen gadi kafin ya mik’e ita kuma tsaf ta gane hararenta yayi, dan haka ma tace “To ko da magana ne?”
Cikin takonshi na isa yace “Ke ma kisan ai idan da maganar zan fad’a, dan bana tashi da kwananniyar magana a baki na.”
Hamna ce ta saki cokalin hannunta saboda wani abu da taji, juyowar da Hajia tayi ne tasa ta saurin d’aukar cokalin, mik’ewa tayi ta aje farantin kankanar ta fita farfajiyar gida, Amna kuma Inna lillahi kawai take maimaitawa, wai da gaske ita ce aka had’a da Ammar? Tab’, lallai sunanta margayiya daga yau, to ita ta ina zata iya da auren Ammar? Mutumin da idan ya fad’a maka wata maganar sai kayi sati kana kuka, shine zatayi zaman aure dashi? Umaima kuma har cikin ranta zab’in ya mata, dan dama Amar na masifar birgeta, haka ma Jamila sam bata ji a ranta wai an tauye ta ba, sai dai ta d’auka zata fara shan bikin yayunta ne dan ita ce k’arama a duk cikinsu, to amma haka Allah ya so sai fatan alkairi kawai.
Suna shiga b’angaren su kowa wanka ya shiga cikin matuk’ar sanyin jiki, amma banda Ammar da shi sam baiji wani abun bak’in ciki ba, hasalima yace Amna dai ce ta shigo d’akin shi a matsayin mata, Allah yasa ta mata shirin da zata uya zama da shi, duk ranar daya samu wacce zuciyarshi ke *so* to ko a yau Amna ta zo gidan saiya fad’a kuma saiya aureta babu mai hanawa.
*WAIWAYE*
_(ADON TAFIYA)_
*Suley Hassan Gaga*
05/06/2020 à 20:32 – Ummulkhairi: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BADAK’ALA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*Labarin gaske*
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_
*SADAUKARWA GA*
_*AHALI NA*_
_Allah ba dan mu ba ka yafe mana zunubanmu, Allah ba dan halayenmu ba ka gafarta mana kurakurenmu, Allah dan rahamarka ka jik’anmu ka mana gafara, *Astagfirullah wa atubu ilaikh*._
*TAURARIN NIGER*
“`(Tsintsiya madaurinki d’aya)“`
_Bismillahir rahamanir rahim_
_10_
*Suley Hassan Gaga*
Haifaffen garin *Marad’i* dake jamhuriyar Niger, a wata unguwa da ake kira *d’an gulbi*, mahaifinshi Alhaji Hassan yana da mata biyu, ta farko ita ce *Rumanatu* wacce suke kira da Ramma, tana da ‘ya’ya uku, babban shine *Innusa* (Yunus), sai k’anwar shi *Barira*, sai kuma k’aramar *Rahmatu*, sai matarshi ta biyu *Saratu* wacce ita ce mahaifiyar Suley da ‘yan uwanshi mata ‘yan biyu masu sunan *Hassana* da *Husseina*, iyalin Hassan Allah ya musu baiwar haihuwar yan biyu, hakan yasa a ahalin nasu suke da yan biyu masu yawa maza da mata, Ramma na da ‘ya’ya uku namiji d’aya da mata biyu, sai dai kasancewarta shu’umar mace yasa ita ke juya gidan da mutanen cikin shi.
Hassan yana da tarin arzik’i kama daga shanu zuwa tumaki da gonaki, a zamaninshi yana d’aya daga cikin masu kud’in da ake lissafawa a garin maradi da kewayenshi, amma dayake ya samu hatsabibiyar mata data riga ta gama mallakeshi da sihiri saiya zamana dashi da talaka duk d’aya, domin kuwa gidanshi ma ba’a cin abinci mai kyau bare suruta, tunda Saratu ta shigo gidan take fuskantar matsi daga gareta inda ta mayar da ita kamar baiwa a gidan mijinta, duk wahalar gidan ita ce har lokacin da rabon ‘ya’yansu ya koka suma suka durmiya cikin wahalar, duk da kasancewar Suleymane babba kuma namiji amma haka ya zama kamar d’an daudu dan duk wani aikin gida na mata babu wanda bai iya ba, haka suke wannan rayuwar kamar bayin da aka siyo da kud’i dan babu wanda zasu fad’a ma ya taimakesu, duk da lokuta da dama Husseina na basu matsala dan ita ce marar hak’uri, amma haka zatayi saboda uwar na tausarta da cewa tayi hak’uri wata rana sai labari.