BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ture shi tayi daga jikinta ta tashi zaune tana kallonshi, shi ma kallonta yake yana jin kamar ya fasa ihu yau Hamna ce tace tana son shi? Yana kallonta ta tashi tsaye tana fad’in “Saina fara cin uwar yarinyar nan kafin hankali na zai kwanta, sai naji abinda ya had’ata da mijina.”

Tasowa yayi yana k’arewa fuskarta kallo yana fad’in “Hamna ni kike kira mijinki? Wuuuuu duniya dad’i, Hamna yau nine kike so? Kishi na kike?”

Da sauri ya d’auki wayarta dake kan kujera ya bud’e ya shiga danne danne, tana kallonshi ita dai sai ji tayi ya saka wak’ar *Umar m Shareed* mai taken *soyayya akwai dad’i*, aje wayar yayi sai kuwa ya shiga kwasar rawa ba kunya ba tsoron Allah, da fari da mamaki ta fara kallon yanda yake rawar, amma sai abun ya fara bata dariya, zaune tayi bakin gadon tana kallonshi, tsakaninshi da Allah yake rawar kamar ya ga *Adam A. zango* a gari, bata ankara ba taji ya jawota yana juyata a dole ita ma tayi rawar.

Tun tana tirjewa tana so ya rabu da ita har wata wak’ar ta shigo wacce ta iya taka rawarta fiye da zaton mai karatu, (in baku manta ba tun a farkon littafin ita d’in gwanar rawa ce da iya shoki), biye masa tayi suka shiga rawa har da dariya kamar mahaukata.

Ummy da tasan sai sun tsula tsiya tunda taga ya shiga d’akin, kuma a gaban idonta su Nazifa suka fito, ta jima tana k’wank’wasa k’ofar amma basu ji ba, kuma gashi tana jin dariyarsu da sautin kid’a, dan haka kawai ta tura k’ofar ta shiga idonta rufe dan kaucewa mummunan gani, a hankali ta bud’a ido ta hange su sun cake sai kwasar rawa, rik’e baki tayi tace “Inna lilliahi wa’inna ilaihi raju’un.”

Da sauri suka tsaya suna kallonta, ko da ya ga Ummy ce ya matso yana fad’in “Ummy albishirinki?”

Ta d’auka zai ce Hamna ce ke da ciki, sai kawai ta kalleta tace “Hamna wace lalacewar ce kuma wannan? Rawa a daren nan?”

Laushi tayi kamar ba ita ba tana k’yabta ido, jinjina kai Ummy tayi tace “To maza d’auki kayanku ku koma b’angarenku kafin ku tara mana aljanu, tunda abun ya zama iskanci, nan kike ta kumbura ke hushi kike ashe d’aurin duniya ne.”

Langab’e kai tayi tace “Allah Ummy da gaske ne, yanzu ma da zan ga Amie saina tattaka ta.”

Kallonta Ammar yayi yace “Wai ke ba zaki fita harkar yarinyar nan bane?”

Zaburo mishi tayi tace “Eh d’in ba zan fita ba, sai naji dalilin da yasa ta kula ka.”

Kallon fahimta ya mata yace “Ki tabbatar zaki b’arar min da ita?”

Cike da tabbaci tace “Allah kuwa zan iya.”

Kallonta yayi da kyau yace “Gobe da safe ki shirya idan zan fita na kaiki gidansu, zan so ganin yanda zaki d’auketa ki nunawa sama ta bakwai kafin ki dirota k’asa, dan ni abun farin cikina ne ace matata na fad’a akai na, kinji ko?”

Cikin murna tace “Da gaske?”

Ba alamar wasa yace “Ina fad’an abinda ba zan iya bane?”

Da farin ciki tace “A’a.”

“Dan haka ki shirya zan kaiki.” Ko da ya fad’a ya juya zai fita, ita har ga Allah ta ma manta wai yaji tayi, kallon Ummy tayi tace “Saida safe Ummy.”

Rik’o hannunta tayi ta dawo da ita baya tana fad’in “Zo nan.”

Kallon juna suka shiga yi Ummy tace “Hamna ina yace zai kaini? Gidansu Amie fa naji yace.”

A hankali tace “Eh Ummy.”

Da mamaki Ummy tace “Anya kuwa Hamna kina so mu zauna lafiya dake? Ke fad’a min me kike so ku zama yanzu?”

Shagwab’e fuska tayi tace “To naji Ummy ba zamu je ba.”

Tab’e baki tayi tace “To yanzu binshi ne zakiyi?”

Da sauri ta juya ta nufi kan gadon tana fad’in “A’a Ummy, bacci zanyi.”

Nufa kanta Ummy tayi tana neman abun bugu tana fad’in “Hamna zan ci ubanki a gidan nan, tashi wuce ki bi mijinki, na gaji da masufarku wallahi karku kashe ni da raina.”

Da gudu ta arta ta fito daga d’akin, ko sauka bai gama ba daga matakala tayi tsalle da niyyar haye bayanshi, shi kuma da baisan da zuwanta ji kawai yayi yayi sungululu ya tafi ta kai suuuu.

*Tsakaninku ne*

Bashi daya rigata ba har ita san da kai tayi duk suka wuntsile a wurin, saida suka gama durkuwa k’asa suka fara kallon kansu dan ganin salon fad’uwar, Ammar da yaji kamar wuyanshi ya karye kallonta yayi, tana zaune kan matakalar ta rik’e k’afa da hannu tana kukan shagwab’a, wani huci ya shiga saukewa da tunanin me ma zai mata ne shi kam, shin ya d’auke ya jujjuyata sannan ya dasata a k’asa, ko kuma ya sake hawan benen da ita sai ya sakota ta fad’o, ko kuma…

*Uwar Lalla ranar da aka kawoni gidana haka na kusa tahowa ta kai na karya wuya amma tuni angona ya cab’oni aradu ta baya, kai bene baiyi ba.*

Ummy dake tsinkayensu ta sama tana jiran taga me zai faru, tashi yayi a hassale yana fad’in “Ke dan ubanki ni kika wuntsilo? Hamna ni kikawa wannan wurgowar? Ashe k’arfin tsiya ne dake kamar bagwariya, ai kuwa yau zaki c…”

Da sauri Hamna data kasa tashi saboda k’afarta ta bud’e hannayenta ta jawoshi da k’arfi har yana neman fad’awa kanta, bai gusar da fuskarshi daga kanta ba yana mata kallon mamaki yaga ta k’amk’ame shi tana fad’in “K’afata! Wayyo Allah k’afata, yah Ammar ka taimaka min dan Allah.”

Kallon fuskarta yayi kawai yaji a ranshi ta gama dashi, kallon k’afar yayi wacce ke rufe da dogon wando, sake kallonta yayi yace “Ciwo take miki?”

“Eh.” Ta fad’a tana rushewa da kukan shak’iyanci, d’aga kai yayi ya kalli Ummy sannan ya kalleta yace “Bari Ummy ta taho saita kaiki d’akinki, ni dai ba zan d’auke ki ba.”

Da sauri ta k’ara jawo rigarshi tace “A’a d’auke ni, d’aukeni muje b’angarenmu kafin Ummy ta taho, ita ta koro ni fa daga can.”

Murmushi yayi yace “Allah?”

“Eh.” Ta fad’a da sauri tana d’aga mishi hannu saiya d’auketa, gyara tsayuwarshi yayi ya d’auketa gaba d’ayanta ya k’arasa sauka da ita, ba tare daya juyo ba yace “Ummy saida safe, yar yajinki ta koma.”

Rufe fuska tayi cikin k’irjinshi har suka fice, har saida suka b’acewa ganinta sannan ta girgiza kai ta shiga saukowa a hankali tana fad’in “Allah kaine Allah, Allah ka shirya min yaran nan shirin addinin musulinci, Allah ka kawar da idon mak’iya da bakin mutane akan su.”

*Ameen Ummy.*

*Alhamdulillah*
04/11/2020 à 14:39 – Ummulkhairi: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BADAK’ALA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍

*Labarin Gaske*

*NA*

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _BA SO BANE_
*3* _D’AUKAR FANSA_
*4* _AUREN HAD’I_
*5* _SANIN MASOYI (sai Allah)_
*6* _JIHADI_
*7* _ITACE K’ADDARARMU_
*8* _K’ANGIN RAYUWA_
*9* _MAATA_
*10* _KAWUNA NE_
*11* _KALLON KITSE_
*12* _AURE_
*13* _SANIN MASOYI (baya da k’ura)…_
*14* _BADAK’ALA…_

*SADAUKARWA GA*

‍‍‍ _*AHALI NA*_‍‍‍

✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ ️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

_75_

Ko da suka shiga ya sauketa kan gado, zaune yayi ya fuskanceta da kyau yace “Hamna, yanzu nan duk cutar nan da kika min shikenan kin cuci banza kenan?”

Saida tayi da gaske ta samu ta rik’e dariyarta tace “Rama to.”

Zaro ido yayi yace “Ni! Ni d’in banza da zan rama, a’a na yafe.”

Cikin bushewa da dariya tace “To bacci zanyi.”

“Kwanta.” Ya fad’a yana kallon idonta, zanin rufa taja ta rufa tana dariya k’asa k’asa, sai yanzu take hango sanda ta bankad’o shi yayo k’asan nan daram, sai kawai ta juyo tana k’ara barkewa da dariya, ganin tana dariyar ba tsayawa har da rik’e ciki yasa yace “In ban miki Allah ya isa ba ki ce ba sunana Ammar ba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected