BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Girgiza kai yayi yace “A’a ban sani ba, fad’a min miye matsalar?”

Cikin nutsuwa Amar yace “Ammar kasan fa Hajia ba son doguwar mu’amula take tsakaninmu da Hajiarsu Jibril ba, sannan ina auren Umaimah wanda dukansu yan uwa ne, kaga abune da ba zai yiwu ba ai.”

Wani kallo ya masa kamar na wanda baisan ciwon kansa ba kafin yace “Yanzu Amar wannan har dalili ne da zai iya sawa ka hak’ura da wacce kake so? Hajia ba tana nusar damu dasu bane saboda Allah, tana so muyi nesa dasu ne saboda izzarta da wani buri na zuciyarta, hakan haka saika haramtawa kanka abinda Allah ya hallata maka.”

K’ara matsawa yayi kusanshi ya sake dafa shi yace “D’an uwa, daga ni har kai mun sani ba wai kowa ya auri wacce zuciyarsa ke so bane, umarninta ne muka bi mukayi biyayya, kada ka tauye kanka ta b’angaren abinda kake so in har ba sab’on Allah bane, idan kace zakayi haka kuma wallahi zaka wahalar da kanka ne sannan ka wujijjiga zuciyarka, idan bar Hajia tace bata yarda ba ka tambayeta dalili? Sannan ta fad’a maka hujjar k’in amincewarta.”

Nunfasawa yayi ya ci gaba da cewa “Kar kayi wasa da damarka yaro, inhar kana sonta to kawai ka fad’a a gida asan abunyi.”

Murmushi Amar yayi yace “Daga yanda kake magana d’an uwa kamar kai ma ka fad’a soyayyar nan ko?”

Murmushi yayi shima yace “Sosai ma, amma ni dalili na da yasa na hak’ura da soyayyata yafi naka k’arfi gaskiya.”

Da mamaki yace “Kamar ya? Me yasa ka hak’ura da soyayyarka? Bansan da sarewa ba haka ma tsoro, na d’auka idan ka samu wacce kake so zaka tsaya ne wajen ganin ka same ta ko da hakan zai iya janyo yak’i.”

Cikin fad’ad’a murmushi yace “Amar wasu abubuwa basa buk’atar jarumta ko rashin tsoro, kai halal d’in bata haramta maka halal d’inka ba, karin maganar hausa ne da ake cewa wai *ana barin halak ko dan kunya*, ni tawa halal d’in ta haramta mani wata halal d’in ne.”

Wani kallo ya bishi dashi na son gano abinda yake nufi, shi kanshi saida ya ji bugun zuciyarshi ya k’aru da sauri sauri, cike da mamaki da tsoron abinda zai fad’a yace “Ammar, kar dai kace min kankana kake so?”

Rintse ido yayi tare da buga tagumin rashin jin dad’i, ya jima haka kafin ya bud’e ido ya kalleshi, wata iska ya furzar mai zafi tare da d’aga kafad’u yace “Amna duniyata ce, uwar ‘ya’yana ce, kwanciyar hankali na ce da farin ciki na, k’aramin abu idan ya gilma ta gaban rayuwata marar dad’i gurinta nake zuwa na samu nutsuwa, ba zan iya mata butulci ba har na bari tasan abinda ke zuciyata ba, Hamna kuma ita ce burin zuciya ta, abincin ruhina sannan mafarkina, su biyun sun sani tsakiya bansan ya zanyi ba, *sune k’addarata*, na d’auka da hannu biyu har naga yanda ubangiji zaiyi dani.”

Yana gama fad’a ya bar wurin, da kallo ya bishi sai yaji kamar ya zubar masa da hawaye, shima cikin k’warin gwiwa ya shiga wajen Hajia dan fad’a mata abinda ke ranshi babu b’ata lokaci, bayan sun gaisa yake sanar da ita shi fa yana son k’ara aure, cike da mamaki tace “Shalele aure kuma? Yaushe akayi auren naku da har zaka k’ara wani? Umaimar bata kwantar maka da hankali ne?”

Cikin turo baki yace “Hajia kawai ina so na k’ara auren ne, dan Allah kada ki hanani.”

Girgiza kai tayi tace “Ba zan hana ka ba, amma fad’a min wace yarinya ka samu?”

“Farisa.” Ya fad’a ko kallonta baiyi ba, k’ank’ance ido tayi tace “Wai me yasa ba kwa ganewa ne yaran nan? Shalele ya zaka min haka? Wace Farisa kuma yarinyar da ko jinin al’ada yanzu ne ta fara shi.”

Kallonta yayi yace “Eh ita Hajia, a hakan ta min wallahi ina so.”

“Kayi hak’uri shalele ka nemi wata, ba zan yarda a sanadiyarku ba na rasa ji da kaina da d’aukakata ba.”

Kallonta yayi da matuk’ar mamaki, amma daya tuna abinda Ammar ya fad’a masa sai yace “Hajia d’aukakarki? Yanzu akan hakane zaki hana mu abinda zuciyarmu ke so?”

Shiru ta masa sai kawai yace “To Hajia me yasa ba kya son aure na da ita?”

“Saboda kakarta tsohuwar karuwa ce, ita kuma wannan rayuwa tana bin ahalina kamar yanda yan biyu ke bin mahaifa, a dalilin auren Farisa kana iya haihuwar yaran da zasu addabeka.”

Cikin jinjina kai yace “Hakane, na gani kam, to amma Hajia taya su tanti Zeinabu suka samu Junaid ta wannan hanyar bayan kuma hakan ba d’ab’iar zuri’arki bace? Ko dai zama da Hajiar…”

Cak ya tsaya da maganarsa saboda hannun data d’aga da niyyar marinsa sai kuma ta tsaya, kallonshi tayi ido jawur kamar zatayi kuka ta nuna masa k’ofa tace “Fita, fitar min a d’aki.”

Mik’ewa yayi ya kalleta yace “Kiyi hak’uri Hajia, Umaimah ba irin matar da nake so bace, ba zan iya hak’urin zama da ita ba gaskiya har bak’in cikinta ya kashe ni, ki taimaka ki yarda da aure na da Farisa.”

Fita yayi ya rufe mata d’akin, zaune tayi kan gado ta fara wa kanta karatun tanutsu, wata rana fa komai zai iya fitowa in tayi wasa, to miye mafita daya wuce ta amince da buk’atarsu, take ta sawa zuciyarta ruwan sanyi ta d’auki niyyar gyarawa ko dan kar a mata dariya ma.

*Da dare* ma kowa na harkar gabanshi ya wuce d’akin Ummy data kira shi a waya tace ya zo, da sallama ya shiga ya zauna yace “Ummy gani kince na zo.”

A hankalce ta kalleshi tace “Ammar, da izinin ka aje Baba Inussa a asibiti?”

Kallonta yayi yace “Ummy kafin nayi taimako saina nemi izinin wani? Kawai naga yana buk’atar kulawar asibiti ne shiyasa na d’aukeshi.”

“Amma kasan hakan me zai iya janyowa kuwa? Me yasa baka tsoron abin fad’a ne?”

Nisawa yayi yace “Ummy ba haka bane, kamar yanda zamu iya bayar da komai namu ga Alhaji matsayinsa na kakanmu haka shima Alhajin, wani k’aramin abune daya faru tsakaninsu shekaru da dama, mu bamu san komai ba bai kamata mu tayasu hura wutar ba.”

Cikin d’aga murya tace “Ammar, ina so ka sallameshi daga asibitin nan ka kaishi wata ko kuma ka mayar dashi gida ka ci gaba da bashi kulawar, amma zamanshi a asibiti zai janyo maka matsala da ma ni kaina, ni kuma wallahi ba zan yarda ka k’ara ja min banzayen matsaloli ba ina zamana lafiya.”

Kallonta yayi fuskarsa a had’e yace “Kiyi hak’uri Ummy, a gaskiya ba zan iya d’aukeshi daga nan ba, bugun k’irji nayi na nuna na isa dashi shiyasa na kawo shi nan, saboda tsoron Hajia kawai ba zan lalata aikin alkairin da nayi niyya ba, Ummy ke ma ya kamata ace kin rage tsoron nan da kike mata, tsoron Hajia yana saki kina aikata kuskure a kowane numfashi na rayuwarki.”

Tsuru ta masa da ido, gaskiya ne abinda ya fad’a fa, amma da yake abun ya gyauraya da jininta saita rufe ido tace “Naji ina tsoronta, kawai ina so ka d’aukeshi daga asibitin nan.”

Kallon mamaki ya mata yace “Hajia Alhaji ne fa d’an uwan Alhaji na Abbanmu, ya zaki ce a masa haka?”

Cike da k’aguwa tace “To naji, idan ba zaka fitar dashi ba ka fad’awa Hajia tasan da zamanshi, kaga idan ta amince shikenan saiya zauna.”

Tashi yayi tsaye ya juya mata baya yana fad’in “Hajia dai, Hajia dai, wai abun alkairi ma saika nemi umarnin Hajia, to wai ita ta busa mana rayuwar nan ne ko me?”

Mik’ewa Ummy tayi ita ma tace “Na sani dama ba zaka yi ba, ban isa na saka kayi ba saboda baka d’auke ni bakin komai ba, kaje kayi duk abinda kaga dama, amma ka sani shirme ko haukanka ba zai k’ara sani a damuwa ba, yanzu b’ace min a gani.”

Kallonta yayi yace “Ummy me yasa kullum sai ki kore ni daga wajenki? Kina yawan fad’a min b’ace min da gani, me yasa?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected