BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Wasu tab’e baki sukayi suna tunanin abinda ya tarasu ya fad’a musu kenan ko me? D’orawa yayi da “A yanda nasan danginmu da gulma da jin dad’in yad’a labari nasan izuwa yanzu kowa yasan abinda ya faru jiya na fasa auren yarinyar nan, to akan shi ne dama zamuyi magana.”
Kallon kallo suka wa junansu tare da k’ananan maganganu na abinda ya fad’a wai gulma, ba tare da damuwa ya d’ora da “Naji da kunnuwa na na gani da idona a cikin gidan nan masu cewa wai an fasa aurenta saboda hanyar data d’aukarwa kanta marar b’illewa, da jimawa a cikin gari naji da kunnuwana masu zaginta da aibatata, kuma maganar ta samu matashiya ne daga cikin gidan nan, da ku ahalinta ake zaginta a cikin gari saboda shigarta, mu’amularta da k’awayenta, amma abun tambayar anan su waye silar lalacewarta? Su waye sanadiyar rugujewar aurenta?”
Tsit kowa yayi sai zuba masa ido da akayi, Hamna kuma dake zaune kan kujera tare da Amna da Umaimah ne ta kalleshi tace “Malam, duk yawan mutanen wurin nan sai akai na ne kawai zakayi maudi’inka.”
Ko kallonta baiyi ba kamar baisan da hallitarta ba ya ci gaba da cewa “Kune silar komai wallahi.”
Alhaji *Mani* ne yace “Ya zaka ce mune sila kuma? Yarinyar da take ganin ta waye tana da ilimi da kud’i.”
Cikin jin haushi Hamna ta mik’e ta kalleshi tace “Na zauna ne saboda yan uwana dana gani amma ba dan jin shirmenka ba.”
Juyawa tayi zata fita ya kalli kowa na wuri yana murmushi yace “Kun gani, babu wanda yayi yunk’urin yi mata magana kan abinda tayi yanzun, kai tsaye ta nuna ni mashirmanci ne kuma zaman nan baida anfani, bata duba kasancewata babba a gareta ba, hakan bai isa a gareku da zai zama dalilin da zaku tsawatar mata ba.”
Mik’ewa yayi tsaye yace “To ku saurara, dalilin had’uwar nan ba wai saboda ita bane, wani babban kuskuren mu ne na ke so na tunatar daku shi dan ku gyara, idan kuma baku gyara ba ni dai Allah ya gani kuma ya sani na tunatar daku, tunda a cikin nan akwai wad’anda zan iya musu fad’a, akwai wanda na isa na d’auki bulala na zane su, haka kuma akwai wad’anda ko kallon da bai dace ba zan iya musu ba.”
Cikin misaltawa da hannu yace “Naji zafi sosai har zuciyata sanda nake tsintar k’ananan maganganu a cikin gari cewa Hamna wai tana abinda take so, daga cikin gidan nan ban tab’a gani ko jin ance anga wanda ya tsawatar mata ba, ban tab’a ganin wanda yace mata ta canza shiga ko kayan jikinta ba, a cikin gidan nan ma babu wanda ya damu da ita bare kuma daga waje, kuma abinda na lura ya jawo hakan ba zai wuce wariyar launin fatar da ake nunawa ba, wai yau lalacewar ahalin nan ya kai matsayin da kowa nashi kawai ya sani, babu wanda zai iya kallon d’an dan uwanshi ya mishi magana ko fad’a kan abinda yayi bai dace ba, kowa yafi son ya tsaya daga nesa yana nuna d’an uwanshi da baki, wannan wace irin rayuwa ce?”
Husseina ya kalla da Hassana da Hajia yace “Kune manyan da suka rage mana a ahalin nan, kuna da dama da iko a hannunku yanda zaku iya tank’wasa duk wani k’aramin tsagera, saboda kuwa ku kuka haifi iyayenmu, amma me kukeyi dan gyara iyalin nan?”
Matse bakinshi yayi yace “Kowa nashi yaja ya killaceshi a jikinshi yake bashi kulawa, d’aya ba zata iya iya tattaunawa akan matsalar data shafi d’aya ba, ko da na tashi a gidan nan cikin sauk’i na fahimci wacece kakata wacce ta haifi mahaifina, wanda ba haka ya kamata abun ya zama ba, yanda gidan nan ke da girma da mutane ya ci ace yaro zai sha matuk’ar wahala kafin ya gane mahaifiyarshi ma bare kuma kaka.”
Kallon Husseina yayi yace “Bansan asalin meye tsakaninki da Hajia ba, amma yanda ke ma kike nuna baki damu da al’amuran ‘ya’yanta ba abun babu dad’i, sanin kanki ne Alhaji baya nuna banbanci tsakanin wanda suke nashi da wanda suke na yan uwanshi, amma a gaban idonshi duk wani al’amari daya kamata kiyi magana saiki zuba ido kina kallo, saboda a ganinki ai ahalin Hajia ne ke kuma ba kya son shiga sabgarta, amma ya ci ace kina yi ko dan d’an uwanki.”
Sauran mutanen ya kalla yace “Yau da kuka ga yarinyar nan akan titi cikin shigar da bata dace ba, kowa na da iko da hujjar da zai iya mata d’an banza duka, kuma babu abinda zai faru duk inda za aje, ku dubeku kuma da kuke gida d’aya, kuna sane da duk rashin mutumcin da take amma kuna kallo, ba komai ya kawo hakan ba sai dukanku kowa yana ji cewa ba ciki d’aya suka fito da ita ba.”
Yayi maganar ne yana nuna su Amar da hannu, d’orawa yayi da “Dukanku nan babu wanda baya zarewa k’anninsa ido wanda suka fito ciki d’aya, amma wanda suke yan uwan juna kuma duk abinda yayi sai ka kalleshi da ido ko ka nuna baiyi laifi ba.”
Juyawa yayi ga lieutenant da Ummy yace “Tanti Hadiza data baku amanar yaran nan ta baku ne da tunanin zaku tarbiyancesu kamar yanda ita ma zatayi, bakuyi laifi ba da kuka nuna musu soyayya har baku ganin laifinsu, amma kun kasa gane abinda ke daidai dasu da wanda ba daidai bane, kunfi kowa sanin tanti mace tsayayya da jajircewa kan abu, mace ce ita da bata yarda da raini ko shashanci ba, domin kuwa a rashin son wannan abubuwan ne ma yasa yau bata gidan nan, saboda ta k’i yarda a mulketa da ranta da lafiyarta, me kuke tsammanin zata ji idan taji an fasa auren ‘yarta? Musamman ma taji dalilin fasa auren.”
Hajia ya kalla yana murmushi yace “Hajia, Hajia, Hajia, nasan nan da zan bawa kowa dama ya fad’i dalilinsa na yin shiru, to kowa zai ce ne ke ce baki bayar da damar shiga hurumin iyalinki ba, suna da gaskiya ta wani b’angaren, amma ni dai a gani na ba hujja bace da zata sa kowa ya k’yale kuma yana ganin ba daidai ba, Hajia bansan me ye a kanki ba, amma ni dai kina birgeni, saboda jajircewarki da tsananinki kan iyalinki ya taka muhimmiyar rawa wajen hana faruwar wasu abubuwan, daga sanda kikayi shiru kuma sai komai ya fara lalacewa, matsalar d’aya ita ce ba kya jan iyalinki a jiki ta yanda zasu saba dake, idan akwai sabo tsakaninki dasu zasu iya fad’a miki komai daya shafesu babu tsoro, amma tsoron nufo ki ma Hajia yana gigita wasu, wasu duk maganar da zasuyi sai sun anbaci sunanki da cewa kar a ja musu matsala, misali Ummy na.”
Ya fad’a nunata da hannu ya d’ora da cewa “Ita ce surukarki ta farko a gidan nan kuma matar babban d’an ki, a k’alla yanzu tana da shekara talatin da shida a gidan nan, amma wannan shekarun basu sa ta samu kusanci dake ba, har yau har yanzu bata iya kallon cikin idonki ta fad’a miki abinda ya dace da ita ko ya’yanta, uwa ta kan sadaukar da komai nata akan yaranta, amma banda Ummynmu, a jimawarta gidan nan ta kai matsayin da zata iya zartar da hukunci kuma ya yanku, amma har yanzu zuciyarta rawa take idan tana tare dake, jikinta b’ari yake idan tana magana dake, hakan ne yasa ta b’oye miki al’amari mai girman gaske wanda ya kamata ace kin sanshi, da kin nuna ita ‘yarki ce data fad’a miki ko da ba zaki ji dad’i ba.”
Dukansu ya kalla yace “Rayuwar nan bata da anfani idan ba zaka anfani d’an uwanka ba, ya kamata mu san yanzu mun rasa dattawan da suka rage mana, dukanmu yanzu anan mu ne muka rage ma junanmu, mu rik’e zumuncinmu kar muyi wasa dashi, mu kula junanmu kamar yanda zamu kula wanda muka fito ciki d’aya dasu, idan haka ta kasance wallahi ba *Ammar* marar kunya da rashin tarbiya d’aya za’a samu ba, za’a samu wasu Ammar d’in ma, sannan marasa jin magana ire iren yarinyar can…”