BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ita kanta wani banbarak’wai taji abun, amma sanin halin yaron nata yasa tayi murmushi tace “To yarona meye na tashin hankali a ciki? Shi aure ai lokaci ne, nasan kuma kasan da haka, sanin kanka ne duk iyayen nan naku matansu d’aya d’aya ne, tunda har yanzu Alhaji ya yanke wannan hukuncin to ku rumgumi k’addara mana, watak’ila fa tsananin rabo ne, kuma inhar ya kasance rabo ne to ka sani wallahi ba kai ba ko Hajia ce tayi yunk’urin hanawa wannan rabon zai iya halakata, ko da kuwa zata gitta masa tsinuwarta ce, dan rabon ‘ya’ya idan ya koka wallahi sai sun zo duniya ko duka mutanen duniya basa so, dan haka ni dai abinda zan shawarce ka dashi shine kuyi hak’uri dan Allah, kar ka d’agawa iyayenka hankali Ammar, kuyi fatan yarinyar ta zama alkairi ga mahaifinka kawai da kuma mahaifiyarka.”

Kallonta yayi a nutse yace “Shikenan Aunty, ni zan fita saina dawo.”

Mik’ewa yayi ya saka takalminshi ta kalleshi tace “Baka fad’a min cewa Hajia ta zab’a muku yan uwanku ba?”

Murmushi yayi kawai ya shafa sumar kanshi ya fice, girgiza kai tayi dan tasan bai gamsu da abinda ta fad’a mishi ba, yana fita kuwa shawagi ya dinga yi ya jima bakin ruwa yana kallon gudanarsu, daga nan kuma ya zarce bakin kasuwa wajen mijin auntyn suka sha hira, a tak’aice tare suka wuni har yamma suka dawo gida, nan ma wani shafi hira suka bud’e kamar d’a da uba kafin daga bisani zuwa *05:56* ya d’auko hanya, saida yayi sallah ya wuce gida kai tsaye da tunanin wacce zai samu kuma yau.

*Bayan* dawowarsu da yamma Labaran na d’akin mahaifiyarshi da abinci gabanshi amma tunani ne fal a ranshi, lura da hakan yasa Husseina kallonshi cike da kulawa tace “Ga damuwa ina gani a fuskarka, sai dai bansan dalilin da yasa kake son b’oye min ba?”

Da d’an murmushi ya kalleta yace “Ba komai Hajiata, kawai dai gajiya ce sai kuma yau da gobe.”

Murmushi itama tayi kawai ta share maganar, d’ibar wata loma yayi zai kai baki sai kuma ya tsaya ya kalleta saboda tsikararsa da zuciyarshi tayi yace “Hajiata, zan iya tambayarki wani abu?”

Kallonshi tayi tace “Zaka iya mana, ina jinka.”

Kallonta yayi yace “Hajia kiyi alk’awarin ranki ba zai b’ace ba da tambayar da zan miki?”

Annurin fuskarta ne ya b’ace ta kalleshi da kyau tace “Ka fad’a ina jinka.”

Cike da fargaba ya d’anyi k’asa da kanshi yace “Hajia dama…dama in..ina son…sanin..cika…kken bayani…ne akan…” Shiru yayi ya kalleta hakan yasa ta kalleshi tace “Akan me kake son sani?”

Sauke kanshi yayi yace “A…kan mahaifi na.” Saida ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi saboda abune da shi dai rabon daya fad’a tun yana shekara ashirin da biyar a duniya, k’ura mishi ido tayi tana kallo wanda hakan ya haifar da zubar hawayenta, hijabinta ta saka tana share hawaye, a tsorace ya matsa kuma da ita yasa hannu yana share mata hawayen yana fad’in “Dan Allah Hajiata kiyi hak’uri ki gafarce ni, Hajiata ki daina zubar da hawayenki dan Allah indai akan abinda na fad’a ne, na hak’uri da son sanin abinda nake son sani.”

Cikin kuka da son bayyanar da abinda ke ranta tace “Alhaji mahaifinka ya cuceni, ya cutar da rayuwata, ya lalata min k’uruciya ta, sanadiyar abinda ya aikata min har yanzu nake zaune a matsayin bazawara, mahaifina har ya mutu yana hushi dani saboda abinda ya faru dani, Alhaji meyasa zaka min maganar shi? Wannan tsinann…”

Da sauri ya rufe mata baki saboda jin hakan ba zai mishi dad’i ba, duk da ta hanyar da bata dace aka same shi ba kuma bai ma san waye mahaifin nashi ba, amma dai ba zai so jin tsinuwarta akan shi ba, hak’uri ya dinga bata yace ba zai sake maganar ba ta hak’ura kawai, saida tayi shiru ta kalleshi tace “To ka ci abincin naka.”

Da sauri ya koma kan kujerar yace “To Hajiata zan ci, kiyi hak’uri dan Allah.” Nan ya fara aika abincin ba dan yana masa dad’i ba sai dan faranta mata rai kawai.

Ana idar da sallah magrib Hamna ta shirya zuwa kan amarya ba tare da kowa yasan fitarta ba a gidan, Husseina ce a falo zaune ta k’walla mata kira saboda sunyi magana da Alhaji akan hidimar bikin lieutenant, yanzu haka ta kirata ne dan taje ta siyo mata pliwa dasu sukari da sauran kayan had’in biscuit da cincin na tarban bak’i, Amna dake kwance kan gado da doguwar riga bak’a da kallabinta, rigar ta mata kyau sosai ta fito mata da gwagwab’an mazaunanta da k’irarta, tashi tayi ta fito tana amsawa a matsayin Hamna (baki daddara ba kenan)?, tana zuwa ta zauna kusa da ita tace “Hajia gani.”

Kallonta Husseina tayi ita dai bata ga wani banbanci ba, domin kuwa akwai kwalliya a fuskarta wacce ta b’oye duhun da take dashi, sai dai bata ga dogon gashi kwance a baya ba, k’aramar jakar hannunta ta d’auka ta fito da kud’i ta mik’o mata tace “Hamna wajen *Ilu* zakije ki siyo mana wannan kayan.” Ta fad’a da mik’a mata takardar da tasa aka rubuta mata kayan dan karta manta ita ma.

Amsa tayi tace “To Hajia.” Mik’ewa tayi ta shiga d’akin su ta d’auko makullin moto ta fito, har ta wuce Husseina tace “Hamna.” Cak ta tsaya da tunanin ko ta ganeta, a hankali ta juyo ta kalleta ita kuma tace “Yau wace rana Hamna na aike ki baki ce a kawo kud’in mai ba.”

Wurga yan matsakaitan idonta tayi ta sauke b’oyayyar ajiyar zuciya tace “Hajia ai akwai mai.”

Girgiza kai Husseina tayi tace “Dama can ai iskanci ne kesa kike cewa babu mai.”

Yanda tasan idan Hamna ce za tayi haka kuwa tayi sumbatar hannunta tayi ta jefa ma Husseina tace “Saina dawo sai ki biya kud’in aiki.”

Da murmushi kawai ta bita har ta fice, motonta ta hau ta tsaya bakin k’ofa tayi oda wanda yasa mai gadi bud’e mata k’ofa, ta murd’a zata fita kenan motar Ammar ta kutso ciki shima, yanda hasken fitilun motar ya d’auke mata ido yasa tasa bayan hannunta ta rufe ido, ganin haka yasa ya k’i kashe hasken sai k’urawa bakinta ido da yayi wanda shi kad’ai ya fito fili, a hankali ya lumshe ido saboda wani tunani da yayi yanzun nan, ina ma ace matarshi ce shi kam da ya samu nutsuwa a tare da ita a halin da yake ciki na rashin dad’in nan, kashe hasken yayi ya lek’o da kanshi ta gilashi yace “Sai na zo na d’auke ki ne dake da moton?”

Da sauri ta sauke hannunta ta kalleshi tana girgiza kai, gabanta ne ya fara fad’uwa inda jikinta na rawa ta kau ce mishi a hanya, da kallo ya bita a hankali ya furta ” *Amna* kenan.” (Wato ya gane wacece)

Jira take ya wuce ko ta samu ta fita amma taga baida niyyar haka, muryarshi taji yace “Ina zaki?”

Da tsoro fal a fuskarta da kuma muryarta tace “Hajiarsu Jibril ce ta aike ni shagon Ilu?”

Wani kallon babu wasa ya mata yace “Ki aje moton ki zo muje na kaiki.”

Bud’e baki tayi cike da bayyanar tashin hankalin zatayi magana sai kuma ta tuna waye gabanta, ruf ta rufe bakinta ta d’an jinjina kai alamar to a zuciya kuma tana fad’in “Kin mutu Amna.”

Komawa tayi ta aje moton ta dawo, yana kallon kowace gab’a ta jikinta harta bud’a gidan gaba zata shiga, zata zauna taga wani kallo da yake mata kamar na bansan iskanci, hakan yasa ta rufe k’ofar ta kama murfin baya zata shiga, a tsawace yace “Dan ubanki waye dreban naki? Ni ko uban wa?”

Da sauri ta rufe jiki harya fara rawa ta bud’e gaba ta zauna, yanda ya kafeta da ido yasa yake iya fahimtar yanda take sauke numfashinta kamar wacce tayi gudu, jin bai tayar da motar ba yasa ta d’an d’ago kai ta kalleshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected