BADAK'ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ko saurarenshi baiyi ba har suka zo inda Jibril ke tsaye mamaki ya gama kashe shi, suna zuwa Amma ya jingina ga koma ya saki yaron ya kalli Jibril yace “Ban hankici (handkiciep) na.”

Mik’a masa yayi yana kallon yaron da tsoro ya gama bayyana a tare da shi kamar ya ga mala’ikan d’aukan rai, yana cikin goge zufar dake tararowa kanshi zuwa fuska da wuyanshi ya kalli yaron yace “Durk’usa.”

Kamar marar k’ashi a jiki haka ya lauye ya durk’ushe yana sake fad’in “Dan Allah kayi hak’uri baba na, wallahi ni ba b’arawo bane tsautsayi ne da yunwa, dan Allah magajina ka bashi hak’uri kar ya kaini prison (magark’ama).”

Ya k’arashe maganar da duban Jibril, idon nan sun kad’a sunyi jawur ya kalli yaron da kyau yace “Kai, kasan ko wanene ni?”

Da sauri ya girgiza kai yace “A’a.”

“To meyasa duk garin nan ka rasa wa zaka figi kayanshi sai ni?”

K’uri ya masa da ido yana kallo jikinshi banda rawa babu abinda yake, hannu ya d’aga kamar zai mareshi yace “Da kai nake kana jina ka min shiru.”

Cikin kukan firgici yace “Wallahi yunwa ce tasa, kwana biyu ban ci komai ba, kuma nayi bara ban samu abinda zan ci ba shiyasa, dan Allah kayi hak’uri ka gafarce ni.”

Fuska a had’e yace “Ina iyayenka suke?”

Ba tare daya tsagaita kukan ba yace “Ba yan garin nan bane, suna zinder ne, almajiranci suka kawo ni.”

A lokacin ne su Junaid suka fito sun gama tattaunawa, Amar ne yayi saurin ciro wayarshi ya duba mai kira, saida gabanshi ya fad’i ganin Hajia ce, Junaid daya fahimta yace “Karka d’auka tunda yanzu zamu koma, gwara musha giyar ta dubu sai ayi kankat.”

Wayar ya kashe tare da jefata aljihu a lokacin ji sukayi kawai Ammar yace “Shiga mota zan mayar da kai gidanku.”

Pik’i-pik’i yayi dan shi dai bai bai yarda gidansu zai kaishi ba, amma tsoro yasa ya mik’e yana d’an rakub’ewa da d’ar-d’ar har ya shiga inda su Junaid suke, saida suka d’auki hanya Amar ya tambayi Jibril meya faru? Jibril da yake tunanin wai Ammar wane irin mutum ne? Anya wannan ba Allah ne ya dubesu ba ya k’i bashi aikin sojan da yake so, girgiza kai yayi yace “Kai dai abar kaza cikin gashinta kawai.”

Junaid ne yayi dariya a harshen fransanci yace “Dan Allah ka bamu musha mu ma, meya faru?”

Nan Jibril ya canza harshe shima ya fad’a musu, ba jimawa kuma sun iso gidansu kaka, ko cikin gidan basu shiga ba sukayi alwala suka shiga masallacin dake kusa da su sukayi sallah, nan kaka tace su shigo su ci abinci, basu mata musu ba suka shiga ciki suka zauna kan tabarma, shinkafa ce da miyar taushe (tauhe ) aka kawo musu, sai ruwan sanyi a gafe suna korawa, duk da Ammar sai wani had’e fuska yake amma har ranshi miyar ta birge shi, tare da almajirin nan suka ci har suka ida sukayi hamdala, nan suka musu sallama suka tafi tare da cewa sai sun dawo, daga nan suka sake d’aukar hanyar komawa gida.

*Gidan roumji*

Suna sauka suka fahimci babu motar yaransu samari wanda suke jinsu kamar wasu garkuwarsu ne idan suna tare da su, mamaki suke ko lafiya, amma sai Labaran yace watak’ila ko motarsu ta samu matsala dan k’arfen nasara babu tabbas, a haka aka bar maganar aka shiga abinda ya tara kowa, har akayi addu’a aka gama aka kwashe awa d’aya babu su babu labari, nan aka fara kiran wayoyinsu amma a lokacin suna hanya akwai matsalar hanyar sadarwar yasa kiran ma baya shiga, wannan abu ya basu mamaki hankali kuma ya fara tashi, lieutenant da ranshi ya b’ace ne yace kar wanda ya sake kiransu, ai babu yaro a cikinsu, kuma da idonshi ya ga motarsu biye dasu har cikin garin nan, dan haka ba musakai ne ba zasu iya k’arasowa k’asa ai, idan kuma hakan ya gagara ai zasu iya kiransu su fad’a musu, dan haka yace su k’yalesu kawai su zuba musu ido, amma basu bari Hajia taji me ake ciki ba, duk da kowa ya bar maganar a zahirance amma haihuwa ta shiga tsakaninsu da b’acin ransu, kowa da abinda yake tunani a ranshi a game da nashi yaron da sauran yaran, a hakane fa har lokacin sallah azahar yayi, lokacin ne Hajia tace ayi haramar tafiya gida dan ita ta gaji da zaman k’auyen nan, a lokacin taji abinda ke wakana, kafin tace komai ne ta kira lambar shalele amma bai d’aga ba, tana sake aika wani kiran kuma sai aka ce wayar kashe, lokacin ne ta rufe ido ta dinga surfa masifa a cikin gidan har akayi sallah hankali ba kwance ba, kuma abinda yafi damun lieutenant da Sa’ada shine cewa da take wannan d’an banzan Ammar d’in ne ya d’auke mata shalele, ita bata ma san ina ya kaishi ba, inda Zeinabu ta tabbatar lallai Hajia bata k’aunar nasu yayan saina Sa’ada suma kuma d’a d’aya take so, Soueiba kuma ta k’ara yarda bata son duk wani jini daya fito daga jikin sarakuwarta Husseina, Alhaji kuma yana ji ya zuba mata ido dan in yace yayi magana zata mishi rashin mutumci ne cikin mutane, dan haka kawai yake kallonta har tayi ta gama, a haka dai tasa suka sake dawowa gida dan ganin meke faruwa.

Tashin hankali, labarin da suka samu a gida ma shine ai tare kuka fita dasu, cikin masifa Hajia tace “Kuma basu dawo ba?”

“Basu dawo ba Hajia.” Cewar Nana mai aiki, cire gyalenta tayi da jakarta ta aje ta zauna kujerar falo tana rau da kanta, duk wani motsin Sa’ada saita kalleta, hakan yasa ta kasa motsawa daga inda take saboda gudun karta zargeta, sallah la’asar kad’ai tasa kowa ya gusa daga falon dan gabatar da sallah, haka gidan ya ci gaba da zama shiru Hajia kuma na zaune a falo ta kasa ta tsare sai taga shigowarsu, inda Alhaji ke zaune a bayan gidan iskan ‘ya’yan itatuwa na kad’a mishi.

*Saida* wannan yaron ya nuna mishi har k’ofar gidansu saidai kamar suna k’uryar gari ne, yaron na fitowa Ammar ya ciro lalitarshi ya fito da kud’i, jaka goma goma guda uku ya bashi yace “Wannan kayi sana’a dashi, idan kuma na sake ganinka a irin wannan banzar rayuwar wallahi saina lahira yafi ka jin dad’i, kasan dai da aljanuna zasu iya nuna min duk inda kake ko?”

Da sauri yaron ya dinga girgiza kai alamar eh kamar k’adangare, jinjina kai shima yayi alamar ah to ka ma shiga hankalinka kafin ya sake had’e fuska yace “Idan kuma ka shiga gidanku ka ce da iyayenka shugaban *sojojin niger* (general) ne ya dawo da kai yace ka zauna gida, idan har suka sake mayar da kai…”

Saida ya kalli gabanshi ya d’an cije leb’e ya kalli yaron yace “Ka fad’awa mahaifinka da kaina zan sauke mishi kafad’a ta hannun hagu.”

Da sauri yaron yace “Babana ya rasu, nan daga mamata ne sai k’annan Baba na.”

Zaro mishi ido yayi cikin d’aga murya yace “To su k’annan baban na ka basu da kafad’a ne?”

“Suna da.” Ya fad’a a muryar kuka, wani jinjina kai yayi alamar jin dad’i yace “To ka fad’a musu haka.”

Yana fad’a ya d’aga gilashin motar ya fizgeta da k’arfi ya tayar da k’ura suka koma baya dan su hau titi, yaron da baki sake saida ya ga b’acewar motar ya juya gida, tunaninshi wannan ba wai aljanu ne dashi ba, shi da kanshi ne aljanin, amma inba haka ba taya kawai zai d’auko ni ya dawo dani? Yanzu karatun nawa fa da nake duk da yunwa bata vari na ma fahimta? Ya malaminmu zaiyi? Ya k’annan babana da kakata zasuyi idan suka ga na dawo? Zasu d’auka tserewata nayi ai tunda dama banso nayi nisa da uwata ba, da wannan tunani barkatai ya shiga cikin gidan, duk abinda aka fad’a mishi ya fad’a sai dai bai fad’i gaskiyar dalilin rabuwarsu ba, gidan tunda suka ji yace shugaban sojoji ma suka sha jinin jikinsu, kakar yaron wacce ta haifi babansu ce tace ma autan ta ai a kwaso duk yaran dake sauran garuruwa su zo nan suyi karatun, dama can yawan gidan ne yasa suka rage ta hanyar turasu almajiranci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231 232 233 234 235 236 237 238 239 240 241 242 243 244 245Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected