BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Bud’ewa yayi ya shiga ya goge su duka tare da bloquén d’in lambar, kiran lambar yayi ko da ta gani ta d’auka jiki na rawa, na yan Maradi ya mata ta hanyar cewa “Ke dan mai… me kike nufi da ni? Na miki kama da d’an iska irinki? To saurare ni da kyau kiji.”
Saida ya gyara zama yace “In kika k’ara kula ni ma ko a hanya wallahi daga ubanki har kakanki na ashirin sai sun zubar da hawaye, in kika k’ara tuna ko sunan matata ma sai yan uwanki sunyi nadamar kasancewarsu yan uwanki, In kuma kika sake aiko min hoton rub’abb’ar fuskar nan taki mai kama da gurb’ataccen tumatir Allah saina watsa miki asid kin k’arasa dahuwa, shegiya b’abb’akar banza ke ba kyau ba ba kyan jiki ba har ki tsaya kina bariki, to ki kiyaye ni kafin ki fara nadamar sani na da kikayi, yanzu ma wallahi na raga miki ne dan ni dan ni fad’a da mace ba aikina bane, amma da namiji ce ke da tuni na nemi inda kike na cire miki k’ashin baya, ‘yar banza mai kama da agwaluma.”
*Kuyi hak’uri da jaruminku, bakin ya saba da…*
Amie da tunda ya fara magana tayi shiru take saurarenshi, saida taji ya kashe wayar ta bi wayar da kallo, ya ci mutumcinta sosai fa ta yanda ba zata iya mantawa ba, amma ya zatayi daya wuce tayi wuri ta aje shi, dan tasha jin labarinshi wurin Hamna tun kafin su b’ata, tasan in tace ma tayi dashi ita ce a kasa da cizon yatsa.
Ko da ya gama fad’a shima ya aje wayar ya mik’e ya shiga wanka, daya fito shiryawa yayi cikin kayan bacci ya fesa turare ya fice wajen matarshi. Da sallama ya shiga ya same su duk zaune a falon, kusan Hajia ya zauna yana kallon Nazifa dake kusa da Hamna suna kallon waya yace “Ke tashi samo min abinci.”
Mik’ewa tayi a ladabce ta shiga madafa, kallon Hajia yayi yace “Hajia jikar nan taki bata san meye miji ba, kiga fa babu ruwanta da na ci abinci ko ban ci ba, ita dai data samu ta cika tunbi shikenan ni na mutu dan yunwa.”
Ko kallonshi ba bare ta tanka masa, haka ma Hajia bakinta taja tayi gum, jin babu wanda ya kula shi yasa yace “Hajia yau wace rana?”
Kallonshi tayi tace “Yau talata.”
“To juma’a insha Allahu zamu koma sabon gidanmu.”
Duk yayi maganar ne yana kallon Hamna, duk da bata kalleshi ba shiru tayi daga danna wayarta, sanda tayi k’ok’arin kallonshi kuma saita lura da wajenta yake kallo, dan haka bata yarda ta kalleshi ba, Ummy ma kallonshi tayi ba tace komai ba sai Hajia da tace “Ammar da gaske kake?”
A lokacin Nazifa ta fito ta sunkuya ta mik’o mishi abincin, saida ya karb’a ya fara ci yace”Allah kuwa Hajiata, tafiya zanyi daga nan mu barku ku sarara kuma.”
Cike da rashin jin dad’i tace “Ammar bana so ku bar nan wallahi, in na bari kuka tafi kamar ban cika burin marigayi ba na son zama a waje d’aya, kuma kaga yanzu kana tashi daga nan sauran ma zasu ce zasu tashi.”
Gyara zama yayi yana kallonta yace “Hajia kiyi hak’uri dan Allah ku ba kowa dama ya d’an matsa, ni na miki alk’awari zumuncinmu ba zai lalace ba sanadiyar tashinmu, na kuma miki alk’awarin ko da na tashi daga nan kullum zan dinga zuwa kowace safiya ina gaishe ki, haka ma kafin na kwanta saina tabbatar da na zo kin ganni na ganki sannan.”
D’an lab’e baki tayi tace “Shikenan, Allah yasa alkairi.”
Su Ameer ya kalla dake kewaye da Husseina tana musu tatsuniya ya kalla yace “Heyy, duk wani wanda yasan mallaki na ne shi ya had’a kwomantsanshi, dan babu wanda zan bari.”
Murmushi ta saki daga nan zaune dan ta fahimci ina zancen ina ya nufa, har ya gama cin abinci suna ta hira dasu Husseina da Hajia, bayin Allah dariya har rik’e ciki sukeyi, sun daddage sai biye mishi suke yi kam, idan ya fad’i wani abu ita kanta Hamna da Ummy sai sun murmusa ko har ma su dara, amma duk da haka bata kalleshi ba bare ta mishi magana. Saida dare yayi sosai kowa yayi haramar nufa inda zai kwantar da hak’ark’arinshi, ta mik’e ta nufi d’akinta na yan mata wanda Nazifa ce a ciki yanzu da Huda shima ya bi bayanta, tsayawa tayi ta juyo ta kalleshi tace “Ya dai kake biyata malam?”
Wani kallo ya mata yace “Ke kike bina ko ni ke binki?”
Girgiza kai kawai tayi ta wuce, ko da suka shiga suka same su kwance kan gado d’aya Huda har ta fara bacci, wucewa yayi ya kwanta kan gadon Hamna, kallonshi tayi da mamaki cikin rad’a tace “Meye haka malam? Baka ga yara ne?”
Rintse ido yayi yace “Ban gansu ba.”
Juyawa tayi ta kallesu sai taga Nazifa ta mik’e zata fita, da sauri tace “Ke dawo kwanta wajenki, ina zakije ke da nan ne wajen baccinki, bak’on daya mana haure shine zai fita.”
Ko da ta fad’a ta shige ban d’aki da kayan baccinta a hannu, da murmushi ya bita ya kalli Nazifada ta dawo ko ta koma ta kwanta, bata jima ba ta fito ta aje kayan data canza kan kujera, kan gadon da suke kwance taje ta shige tsakiyarsu tana fad’in “Ku matsa min nima.”
Bud’a ido Huda tayi ta kalleta ta hangi gadonta, saida gabanta ya fad’i ganin tonton d’in ta kan gadon a dakinsu, juya baya tayi ta yanda take kallon k’ofar shigowa ta matsa mata, wajen k’afafunsu ta maido kanta ta d’ora matashi ta kwanta, ta lik’e ido taji muryarshi tsaye a kanta yace “Ku matsa min nima.”
A tsorace suka tashi zaune tare ban da Hamna data san halin kayanta, kallonshi sukayi ya kuwa tsaya kusan kanta rik’e da pillow shi ma, Nazifa ce tayi saurin wuntsilawa ta sauka daga gadon ta nufi hanyar fita, da sauri Huda ta tashi ita ma ta bi bayanta suka fice Nazifa na fad’in “Yau mun shiga uku, to su kna d’akinsu wai?”
Cikin turo baki Huda tace “Muje d’akin Hajia kawai mu kwanta.”
Ko da taga sun fita ta mik’e ita ma da niyyar bin bayansu, da k’arfi yayi tsalle ya fad’a kanta hakan ya tilasta mata fad’awa kan gadon da k’arfi, da k’arfi tace “Aouch.”
Kafin ta bud’a ido taji yayi kwance kanta gaba d’ayanshi ya kuma sakar mata nauyinshi, yanda ya tausheta yasa ta kasa yin numfashi mai kyau, bud’a ido tayi ta kalleshi tace “D’aga ni.”
Girgiza kai yayi yace “Zaki koma d’akinmu?”
Girgiza kai ita ma tayi tace “A’a, har sai na yarda babu komai tsakaninka da Amie.”
Da k’arfi yace “Babu komai kankana, taya kike tsammanin zanyi iskanci a waje bayan ina da ke? Sannan na rasa da wanda zanyi iskancin ma sai k’awar ki? Na yarda ni mahaukaci ne kuma ba mutumin kirki ba, amma bana neman mata Hamna kuma bana shan ko da sigari bare k’waya.”
K’afeshi tayi da ido tana kallo, kallon tausayi da jin k’ai da rahama, wa yace shi mahaukaci ne? Dan tana fad’a masa haka ai kawai tana fad’a ne, me yasa zai yarda shi mahaukaci ne kuma ba mutumin kirki ba? Bata ji dad’in abinda ya fad’a ba, a hankali cikin fitar da wahalallen numfashi tace “Wa yace kai ba mutumin kirki bane?”
Saida ya k’ank’ance idonshi yace “Ke mana, haka kike kallona ai.”
A hankali ta d’aga hannunta ta shiga shafa fuskarshi a hankali tana kallonshi, cikin taushin murya sosai tace “Kai mutumin kirki ne Abban yarana, duk gidan nan muna alfahari da kai, dalilinka ne abubuwa dayawa suka canza, ka daina wa kanka wannan kallon, kaji? Ka daina bana so.”
Yanda ta k’arashe maganar da matuk’ar shagwab’a da kashe murya yasa shi jin zuciyarshi ta k’ara narkewa, murmushi ya saki yace “Amma duk da haka ai baku sona.”
Idonshi ta kalla tace “Waya fad’a maka, muna sonka yah Ammar, muna k’aunarka dukanmu.”
D’aya hannun tasa ta tallabo fuskarshi suna kallon juna sosai tace “Ammar *ina sonka*, d’azu nayi niyyar fad’a maka haka, amma wannan Amien…”