BADAK’ALA COMPLETE HAUSA NOVEL
Ammar kuma juyawa yayi zai kalli k’awarta ta sai kuma ya ga ita sai wani had’e fuska take, kallon gabanshi yayi hakan yasa k’awar cewa ” Yayanmu mun gode fa daka d’auko mu, dan har mun fara tunanin k’aryar da zamu fad’a a gida zuwa gobe.”
Cike da shak’iyanci yace “Karki damu, ai mace irinki tafi k’arfin ta rasa mai sa’ar da zai d’auko ta, ni ne da godiya.”
Fasa mata kai yayi da wannan maganar tashi, sai kawai tace “Nagode, amma nima sa’ata ce ace na shiga motarka har muna musayar yawu da kai.”
Tsaki sukaji wanda yasa shi kallon Hamna da tayi tsakin, to na meye? Haka kawai taji ranta na b’acewa sai kumbura take, kamar Ammar yasan me take ji a zuciyarta sai kuwa ya biyewa k’awar suna ta hira, saida aka kawo inda zasu sauka tace “Mai kyau zaka iya aje ni anan ma.”
Da murmushi yace “To mai kyau.” Pakawa yayi su biyu suka sauka ya zuro kanshi yace “Bansan nawa ne farashin lambar wayarki ba, amma zan so ki fad’a min komai tsadarta zan biya dan a bani.”
Cike da duniyanci tace “Farashinta mai tsadar gaske ne, amma kai na musamman ne, dan haka kawo wayarka na saka maka kyauta.”
Cikin fara’a ya mik’o mata wayar yace “Ina godiya da wannan karamcin.”
Tana cikin saka masa tace “Ai karrama mai karamci yafi k’arfin iyawata ni kad’ai, kai babban mutum ne.”
Saida ya saci kallon Hamna yayi murmushi yace “Kinsan ba kowa yake gane girma da darajarka ba, wasu idan sukaga suna rayuwa tare da kai sai su mayar da kai kamar abun banza.”
Bashi wayar tayi ya amsa tana fad’in “Ka rabu da su kawai, zasu fahimta ne a sannu duk ranar daka mallaki wacce zata dinga nuna musu darajar taka.”
Wani murmushi yayi na iskanci yana goge lambar yayin da ita kuma take tunanin yana saka lambar ne a wayarshi yace “Ke wasu fa mahaukata ne basa fahimta duk yanda zakiyi da su, ki barsu da shan kayan ruwa kawai suna cika musu mafitsara.”
Dariya tayi sosai yayin da sauran kuma sukaji kunya, kamar tasan da Hamna yake sai cewa tayi “Barta kawai, zan dinga fahimtar da ita matsayinka ko ta fara ganin girmanka.”
Ammar ne yace “Amma zan iya sanin adadin matakan tsaron dake gidanku? Domin idan na tashi zuwa nasan irin shirin da zanyi.”
Murmushi ta masa tace “Ka zo duk sanda kake so, zaka samu k’ofa a bud’e.”
Da wani yanayin shegantaka yace “Allah ko?” Ita ma a salon wayewa ta marmad’a masa ido, hannu ya zuro ya bata da niyyar su gaisa yana fad’in “Saina kiraki mai kyau.”
Bashi hannu tayi wanda yasha akaihu zargama zargama ita ma suka gaisa tace “Sai na jika mai kyau.”
Kashe mata ido yayi ba tare daya saki hannunta ba yace “Za dai ki jini a waya mai kyau, amma jina ai sai bayan aure.”
Murmushi tayi harda sunkuyar da kai tana d’an matsa hannunshi mai laushin gaske tace “Har kasa na fara tunanin kaina a matsayin matarka.”
Kallon wannan mahaukaciya ce ya mata yace “Ni fa tunda na ganki nake jin ina k’amshin lalle.”
Cikin b’acin rai da jin kamar ta rufe shi da duka tace “Dan Allah ni muje ka kaini gida na gaji da jin wannan zancen na ku.”
Juyowa yayi ya mata wani kallon zan ma ci ubanki ne yarinya, kawar da kai tayi shi kuma ya saki hannun k’awar ta ta yana fad’in “Saida safe.”
Jan motar yayi suka wuce har saida ya aje sauran ma kafin suka d’auki hanyar gida, babu mai magana ko kallon wani har suka kusa isa gida, a daidai su sha kwana motar police ke nan da alama wucewa zasuyi motar ta samu matsala, haka kawai wani police ya tsayar dasu, tsayawa yayi ya sauke madubin motar yana kallonshi daga shi har shi kowa fuska babu annuri, police d’in ne yace a harshen fransanci ” Malam daga ina haka a daren nan?”
A hankali Ammar ya kalli agogon hannunshi k’irar gucci ta fata, ganin duka yanzu ne k’arfe *11:18* na dare yasa ya kalleshi yace “Daga inda ka aike mu mana.”
Da alamar tambaya police d’in yace “Me? Malam wace irin amsa ce haka? Tambayarka muke daga ina kake?”
“Amsar kenan na baka, akan me zaka tare ni yanzu kana tambayata daga ina nake?”
Hassala yayi yace “Wai waye kai da zaka ce ba za’a tambayeka ba? Kafi k’arfin doka ne ko me? To fito daga motar sannan ka bamu takardun motar.”
Murmushi yi wanda har yasa Hamna tsorata dan tasan k’aramin aiki ne yayi bala’i da shi yasa su kwana a gark’ame, murfin motar ya kama zai fito yana fad’in “Bara na fito kaga tsawo na to.”
Cak ya tsaya saboda hannunshi da Hamna ta rik’e, yana kallonta ya ga hawaye har sun cika idonta, cikin rawar murya tace “Dan Allah ka basu takardun mu wuce.”
Fizge hannunshi yayi yace “Sake ni dallah, ni zai nunawa wannan k’azamin kakin nashi, waye shi da har zai tambaye ni waye ni? Bari na nuna masa daidai nake da shi, uban wa ma ya bashi damar tsayawa nan d’in.”
Zai fito ta sake rik’e rigarshi hawaye suka zubo mata tace “Dan Allah fa nace yah Ammar, ina jin tsoro.”
Da k’arfi ya kawar da kanshi daga kallonta saboda jin zafin ganin hawayenta da yayi, police d’in dake tsaye ne yace “Kai nake jira ai ka fito, madame ki barshi mana naga me zaiyi, naji kana fad’in wai k’azamin kaki na, to fito na nuna maka k’arfin ikon kakin nawa.”
Cikin hassala da k’ufula ya daki sitiyarin motar da k’arfi, yana son ya fita ya nuna mishi bai tsoronshi sai dai ya kulleshi, amma kuma baya son ganin Hamna cikin damuwar nan, ganin hawayen ta ma yasa shi jin babu dad’i haka yasa shi dole ya juyo ya kalle shi ya saisaita nutsuwarsa ya k’ak’aro murmushin na ganeka kuma zamu had’u ya masa yace “Yallab’ai, ka barmu mu tafi mana, madame d’in nan rigima ce da ita, kasan mace mai ciki saurin hawa.”
Jin haka sai police d’in ya k’ara jin wata izza ai sai yace “Kawai ka fito daga motar ka bamu takardunka, yo har mu zaka d’auka wasu sakarkaru har kake fad’a mana magana, yau zaka gani.”
Kallon Hamna yayi ita ma ta mishi kallon taimaka ka basu dan Allah, hakan yasa yace mata “Akwai takardun, amma wallahi ba zan bashi ba.”
D’aya daga cikin wanda suke tare ne yana duba motar ya matso yace “Ya dai? Lafiya?”
Kafin police d’in yayi magana Ammar yace “Abokina wannan mutumin ne ke son b’ata min lokaci, to wai halan baya da aure ne? Inba haka ba ai da zai fahimci larurar da kan iya saka miji fitowa a dare kuma tare da iyalinshi, ka ganta nan.”
Ya fad’a yana nuna mishi Hamna da gabanta fad’uwa yake ido taf da hawaye ya ci gaba da cewa “Tun sallah isha’i ta sani zagaye garin nan da neman wani wai karas, na fad’a mata yanzu ba lokacin karas bane amma ta k’i yarda, kai har karas d’in da Allah ya hore min na ce ta gatsa ☹️ amma tace bai mata ba, da k’yar na samu yanzu na lallab’a ta ita da d’an baba na siya mata alewa zamu koma gida, yanzu gashi kasa min ita kuka, domin Allah haka ya dace?”
Jami’in da yaga Ammar daban ne da mamaki yace “Dan Allah me sunanka?”
Murmushi ya masa yace “Ammar, Ammar Hassan Gaga.”
Zaro ido yayi ya bashi hannu yace “Abokina kace yan biyun lieutenant ne? Ah masha Allah, zaku iya tafiya kawai, Allah ya tsare Allah ya raba lafiya.”
Hannu ya bashi suka gaisa kafin ya kalli waccen yana hararenshi suka wuce, suna tafiya ya kalleta ya mata rank’washin tsiya a kai yana fad’in “Shegiya yanzu baga anfanin saka babban mayafi ba, da wannan shegen siririn ne a jikinki da yanzu tayaya zan iya kallonki na ce matat…” Sai kuma yayi shiru, turo baki tayi gaba ba tace komai ba har suka isa gida, saida suka tsaya sun fito a tare suka nufi hanyar b’angaren su, tana daf da shiga falon ta juyo ta kalleshi tace “Allah ya isa rank’washi na da kayi.”